Xi Jinping Ya Ba Da Umurni Game Da Babban Shirin Shekaru Biyar-Biyar Na Bunkasa Tattalin Arziki Da Zamantakewar Kasar Sin Na 15
Published: 19th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ba da umurni kan babban shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin karo na 15, inda ya nanata wajibcin tsai da shiri bisa halin da ake ciki, matakin da ya kasance muhimmiyar dabarar jam’iyyar kwaminis ta Sin wato JKS a fannin gudanar da harkokin kasa, kuma fifiko a siyasance na tsarin mulkin gurguzu mai salon musamman na Sin.
Xi ya ce tsai da babban shiri na 15 na da babbar ma’ana ga tabbatar da manyan tsare-tsare da aka tanada a yayin babban taro karo na 20 na JKS, da gaggauta zamanantar da al’ummar Sinawa. Don haka dole ne a samar da shiri bisa halin da ake ciki, bisa tushen demokuradiyya da doka da shari’a, ta yadda al’ummun kasa za su iya cin gajiyar manyan tsare-tsare.
Ban da wannan kuma, an saurari ra’ayin jama’a daga dukkan fannoni, da koyi da dabarun da aka samu a ayyukan yau da kullum, don dunkule ayyukan da za a yi da manufofin da za a dauka, ta yadda za a cimma nasarar aiwatar da shiri mai inganci.
Sin za ta gudanar da shiri na shekaru biyar-biyar na 15 a badi, yanzu kwamitin kolin JKS na rubuta shawarar tsai da shirin. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Ginin Babban Asibitin Anka Da Aka Inganta
Sauran sassan da aka gyara da kuma saka kayan aiki sun haɗa da sashen Kulawa da Mata (ANC), ɗakin tiyata, ɗakin X-ray, sabon ginin hukunta asibiti, masallaci, gidan Babban Daraktan Lafiya (gidaje mai ɗakuna 3), da kuma sashen kula da yara, da dai sauransu.
A yayin jawabinsa a wajen ƙaddamar da aikin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, an kammala gyaran gine-ginen tare da sanya dukkan kayan aikin kiwon lafiya cikin kwangilar cikin watanni 12.
Gwamnan ya ce, “A shekarar da ta gabata ne aka fara gyaran wannan asibitin, kuma wani kamfanin cikin gida ne aiwatar da kwangilar.
“Saba hannun jarin ya mayar da asibitin zuwa wurin kiwon lafiya na zamani tare da na’urori na zamani, wannan ba shakka zai inganta jinya ga ‘yan jihar a garin Anka da kewaye.
“Ga al’ummar Anka da kewaye, wannan aiki na ɗaya daga cikin alƙawuran da muka ɗauka na samar da ribar dimokuraɗiyya da inganta rayuwar ‘yan ƙasa.
“Za mu ci gaba da ba da fifiko kan al’amuran ci gaba, tare da tabbatar da cewa al’ummarmu sun samu ingantaccen lafiya kuma da araha, ilimi, noma, hanyoyi, da sauran muhimman ababen more rayuwa a faɗin jihar nan.
“Zuwa ga ma’aikata da mahukuntan babban asibitin Anka, ina kira gare ku da ku tabbatar da gudanar da wannan cibiya mai inganci da kulawa, ina kuma roƙon ku da ku jajirce wajen samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga jama’armu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp