Gwamna Bala Ya Yi Alhinin Rasuwar Yariman Bauchi, Garba Muhammad Sambo
Published: 20th, May 2025 GMT
Ya misalta rashin basaraken da cewa, ba rashin ne kawai ga iyalai ko al’ummar masarautarsa ba, a’a rashi ne ga illahirin masarautar Bauchi da ma jihar Bauchi baki ɗaya.
Gwamna Muhammad ya misalta Alhaji Garba a matsayin babban basaraken gargajiya wanda aka sani da hikima, tawali’u, da sadaukar da kai ga hidimta wa al’ummarsa.
“Ya kasance mutum mai dattako wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kyautata zaman lafiya da cigaba,” in ji gwamna Bala.
Gwamnan sai ya yi addu’ar Allah ya jiƙan mamacin ya gafarta masa kura-kuransa tare da sanya shi cikin aljanna maɗaukakiya. Ya kuma jajanta wa masarautar Bauchi, iyalai da al’ummar jihar da fatan Allah ba su haƙurin juriya na wannan babban rashin..
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya yi watsi da hukuncin da Jam’iyyar PDP ta yanke na korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, daga jam’iyyar.
Aminiya ta ruwaito yadda PDP ta kori Wike, Sanata Samuel Anyanwu da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, a yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo.
Cif Olabode George ne, ya gabatar da ƙudirin korarsu, kuma Shugaban PDP na Jihar Bauchi, Samaila Burga, ya mara masa baya.
Sai dai bayan sanarwar, Gwamna Fintiri ya fitar da wata sanarwa, wadda ya nesanta kansa daga matakin da jam’iyyar ta ɗauka.
Ya ce ba ya goyon bayan korar da aka yi wa Wike, domin hakan zai ƙara haifar da rikici a cikin jam’iyyar.
“Ina son na bayyana a fili cewa ba na goyon bayan korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Wike daga PDP. Wannan mataki ba zai amfani jam’iyya ba. Ba zan shiga cikin abin da zai ƙara ruguza jam’iyya ba,” in ji shi.
Fintiri, ya ce yana ganin zaman lafiya da haɗin kai sun ɗore a jam’iyyar PDP.
Ya roƙi ’ya’yan jam’iyyar da su mayar da hankali kan yin sulhu maimakon ƙara haddasa rikice-rikice.
“Na yi imani cewa sulhu da fahimtar juna su ne hanyar da ta fi dacewa. Ina kira ga kowa ya yi aiki don ganin an samu haɗin kai a cikin jam’iyya.”
Fintiri, na cikin gwamnoni huɗu da suka halarci taron, kuma shi ne Shugaban Kwamitin Shirya Taron.
Gwamnonin Jihar Osun, Ademola Adeleke; Taraba, Agbu Kefas; da Ribas, Siminalayi Fubara ba su halarci taron ba.