Dubban Falasdinawa Sun Fito Kan Titunan NewYork Don Tunawa Da Ranar Musiba ko Nakba
Published: 16th, May 2025 GMT
Dubban falasdinawa ma zauna Amurka ne suka fito gagarumar zanga-zanga don tunawa da zagayowar Ranar musiba a jiya Al-Hamis a birnin NewYork. Inda suka bukaci a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza da gaggawa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne musiba na shekaru 77 da suka gabata.
Falasdinawa da kawayensu daga kasashen duniya da dama su kan fito zanga-zangar tunawa da wannan ranar shekaru 77 da suka gabata a ranar 15 ga watan Mayun shekara 1948., sannan ranar Nakba ta bana tazo a dai-dai lokacinda HKI take kara kissan Falasdinawa a Gaza.
Yansanda a birnin NewYork sun tabbatar da tsaron masu zanga-zanga a duk tsawon zanga-zangar. Banda haka masu zanga zangar suna rike da tutocin falasdinawa da dama da kuma wata guda babba, wacce suka daurata a kan sanennen gada na birnin News York wanda akekira Brooklyn Bridge.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dalibai 29 Suka Rasu A Turmutsitsin Tserewa Ga Fashewar Taransifoma A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
Dalibai 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya yayin tserewa fashewar taransifoma
Akalla dalibai 29 ne suka mutu a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wani turmutsutsu sakamakon fashewar tiranfomar lantarki a lokacin jarrabawar sakandare, a cewar ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Wata takarda daga ma’aikatar lafiya ta ce: “Mutane 29 ne suka rasa rayukansu bayan an kai su asibitocin birnin Bangui.”
Ba a samu ingantattun bayanan yawan wadanda suka mutu ba har zuwa yammacin ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da fashewar ta faru, sama da dalibai 5,300 ne ke zana jarrabawar kwana na biyu na jarabawar sakandare.