Gwamnatin Tarayya Na Ƙoƙarin Farfaɗo Da Sashin Raba Wutar Lantarki A Nijeriya
Published: 16th, May 2025 GMT
A cewarsa, ba ga wannan akwai shirin kawo sauyi kan manyan kalubale da suka hada da lalata na’urorin wutar lantarki, gudanarwa, matsalolin yankuna da suke janyo cikas ga gudanar da ayyuka.
Ya umarci hukumar kula da wutar lantarki a Nijeriya (NERC) da ta tabbatar kamfanonin rabar da wutar lantarki sun bayar da hadin kan da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babu Dalilin Da Zai Sa ‘Yan Nijeriya Su Yi Talauci – Tinubu
Tinubu ya kara da cewa tun bayan karbar mulkinsa, gwamnatinsa ta bayar da fifiko wajen samun damar kudi kuma ta yi alkawarin tallafa wa harkokin kasuwanci da zai habbaka samar da ayyuka da samun kwarewa da kuma masana’antu.
Ya yaba wa gwamnatin Kuros Ribas kan kirkiro shirin tattaunawa da fasahar zamani a harkokin kasuwancin jihar, yana mai cewa wannan ya sa jihar ta yi fice a bangaren fasahar zamani.
“Fasahar zamani zai bai wa harkokin kassuwanci kanana da matsakaita samun damar intanet mai sauri da mai arha da kayayyakin aiki na zamani da samun hadin gwiwa don koyo da ingantawa, tare da tunawa cewa duniya ta kasance wani fage na bunkasa harkokin kasuwanci a zamanance.
“’Yan kasuwa da ke habaka kasuwancinsu a zamanance suna da wuri a Ikom da masu yin kayan daki a Kalabar da masu zanen kaya a Ogoja, Ugep, ko Odukpani.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa tsare-tsaren gwamnatina na sabuwar fata ke nufin samar da yanayi mai kyau ga kanana da matsakaitan karkokin domin su samu damar habaka.
“Kudurinmu ba shi ne, ba kawai bayar da rance ko tallafi ba, gina wani tsarin da zai samar da ababen more rayuwa da kuma karfafa basirar ‘yan kasuwa,” in ji shi.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kuros Ribas, Bassey Otu ya bayyana taron harkokin kasuwanci kanana da matsakaita karo na 8 a matsayin matsayin wata manufa mai matukar muhimmanci a tsakanin jihar da gwamnatin tarayya.
Otu ya ce manufar ita ce inganta ruhin harkokin kasuwanci na ‘yan kasa da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp