Tattaunawar Iran da Amurka na inganta zaman lafiya a yankin : Araghchi
Published: 20th, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka za ta iya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
A yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen dandalin tattaunawa na Tehran, Araghchi ya ce kasashen yankin suna goyon bayan tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka.
” Zaman lafiya da kwanciyar hankali su ne batutuwa mafi muhimmanci ga dukkan kasashen yankin,” in ji shi.
Ya nanata matsayar Iran kan turbar diflomasiyya da kuma muhimmancin da take baiwa manufofin kyakkyawar makobtaka ta hanyar tattaunawa.
A wani bangare na jawabin nasa, ministan harkokin wajen na Iran ya ce dandalin tattaunawa na Tehran karo na shida ya samu halartar masana da jami’an kasashen waje da ba a taba ganin irinsa ba.
Wannan yunkuri a cewarsa, ya bayyana yuwuwar Teheran a matsayin cibiyar musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na ƙasa da ƙasa.
Bugu da kari, ministan harkokin wajen na Iran ya ce ya tattauna da takwarorinsa na Oman da Qatar kan tattaunawa da Amurka.
Mista Araghchi ya yi maraba da matakin da kasashen yankin musamman na yankin tekun Fasha suka dauka na sauya ra’ayinsu game da Iran, kamar yadda suke a matsayin “kyau” dangane da shawarwarin da aka yi tsakanin Tehran da Washington.
Idan dai ba a manta ba a farkon watan Afrilu ne aka fara tattaunawa tsakanin Iran da Amurka karkashin jagorancin masarautar Oman.
Ya zuwa yanzu dai an gudanar da shawarwari guda hudu kan shirin nukiliyar Teheran da kuma dage takunkumin. Bangarorin biyu duk sun bayyana tattaunawar a matsayin mai kyau da kuma amfani.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Iran da Amurka
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Ce Gabatar Da Bukatar Dakatar Da Tashe Makamashin Uranium Karshen Tattaunawar Da Amurka
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Rvanchi ya bayyana cewa a duk lokacinda gwamnatin Amurka ta gabatar da dakatar da tache makamacin Uranium a cikin Iran tattaunawar ba zata je ko in aba.
Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto Steve Wit-koff jakadan shugaba Trump na musamman a yanking abas ta tsakiya, kuma wakilinsa a tattaunawar Tehran da Washingtong kan shirin makamashin Nukliyar Iran ya fadawa kafafen yana labarai kan cewa duk wata yarjeniya da za’a kulla da Iran a kan shirinta na makamashin Nukliya sai ya hada da rashin tashe makamashin Uranium a cikin kasar Iran, wanda zai nesantata daga makaman Nukliya.
A nasa bangaren Takhta Ravanci ya bayyana cewa tun farko Iran ta bayyana cewa batun tace makamashin Uranium a cikin gida alfakharin kasarmu don haka ba ma abinda tattaunawa ne da wata kasa ba.
Sai dai ya kara da cewa, duk tare da cewa Amurka takan bijiro da wasu al-amura ga kafafen yada labarai sabanin abinda take bayyana wa a fagen tattaunawa, Iran zata ci gaba da halattan tarurrukan tattaunawar sai randa Amurka ta gabatar da wannan bukatar ta kuma sake jin ansar da muka sha nanatawa kan cewa batun tashe makamashin Uranium a cikin kasa bayan cikin ajendar Iran da Amurka.