Chadi: An Kama Tsohon Fira Minista Kuma Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasa
Published: 16th, May 2025 GMT
Da safiyar yau Juma’a ne dai jami’an tsaron kasar Chadi su ka kai wani farmaki na kama tsohon fira minista kuma jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Succès Masra.
Jam’iyyar hamayya da Masra yake jagoranta, ta bayyana abinda jami’an tsaron su ka yi wa jagoran nata da cewa, garkuwa ce.
Ita kuwa hukumar kasar ba ta fitar da wani bayani akan kamun Masra ba,wanda shi ne ya zo na uku a zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar da ta gabata.
Bayanin da jam’iyyar adawar ta masu; Sauyi” ta wallafa a shafinta na ‘facebook’ ya kunshi cewa; shugaba Succes Masra an yi garkuwa da shi da karfin bindiga da safiyar yau 16 ga watan Mayu da misalign karfe; 05; 56 daga gidansa da yake kusa da babbar cibiyar jam’iyyar.
A karkashin sanarwar, Shafin jam’iyyar na ‘facebook’ an kuma wallafa hoton bidiyo na shugaban jam’iyyar yana fitowa daga gidansa zagaye da masu dauke da makamai da suke sanye da kakin soja.
Babban mai shigar da kara na kasar ta Chadi Umar Muhammad Kidilayi ya fada wa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa lallai an kama Masra.
Masra dan shekaru 41 ya rike mukamin Fira ministan kasar na tsawon watanni 5 gabanin zaben shugaban kasar da aka yi a watan Mayu na 2024.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.
Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an da za a ɗauka zuwa 50,000, bayan umarnin da ya bayar a ranar Lahadi na ɗaukar jami’an tsaro 30,000.
Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakaduHaka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.
Kazalika, shugaban ya bai wa hukumar ’yan sandan farin kaya ta DSS umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai a rundunar kare dazuka wato Dakarun Gandun Daji ta Forest Guard.
Shugaba Tinubu ya kuma umarci DSS ta aika dakarun Forest Guard “domin zaƙulo ’yan ta’adda da ’yan fashi daga dazuka.”
“Babu wani sauran gidan ɓuya ga miyagu,” in ji shi kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ta bayyana.
Sanarwar ta ƙara da cewar, za a sake horar da jami’an ’yan sanda da aka janye daga gadin fitattun mutane kafin mayar da su aikin ɗan sandan gada-gadan.
Shugaban ya yi amfani da damar wajen jinjinawa hukumomin tsaro wajen kuɓutar da mutane 34 da aka sace a Mujami’ar Kwara da ɗalibai 24 da aka sace a makarantar jihar Kebbi, yayin da ya ce suna ɗaukar matakan da suka dace wajen kuɓutar da ɗaliban makarantar mabiya ɗarikar Katolika da ke Jihar Neja.
Tinubu ya jinjinawa rundunar sojin ƙasar a kan gudumawar da jami’anta ke bayarwa da kuma gabatar da ta’aziyar rasuwar Janar Musa Uba da ƴanta’adda suka yiwa kisan gilla, yayin da ya buƙace su da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da ake fama da tashin hankali.
Shugaban ya buƙaci majalisar ƙasa da ta sake fasalin dokokin tsaro domin bai wa jihohi damar samar da ’yan sanda na kashin kan su, yayin da ya ce gwamnatin tarayya za ta taimaka musu.
Tinubu ya kuma buƙaci Masallatai da Majami’u da su dinga neman taimakon jami’an tsaro a duk lokacin da za su gudanar da taron ibadun su, musamman a yankunan da ake fama da matsalar tsaro.
Shugaban ya kuma jajanta wa gwamnatoci da kuma mutanen jihohin Kebbi da Borno da Zamfara da Neja da Yobe da kuma Kwara saboda kisan gillar da ƴan ta’adda suka yiwa mutanen su.