“Wannan ya ba wasu jihohi fiye da goma sha daya ‘yancin kai, tare da karin wadanda ake sa ran za su biyo baya. Wadannan jihohin yanzu suna iya shiga cikin masana’antar wutar lantarki, daga samarwa har zuwa isarwa, rarraba, har ma da samar da mitoci.”

“Na biyu, dole ne mu magance rashin ingancin ababen more rayuwa, wanda ya taru a cikin shekaru 60 da suka wuce saboda rashin kula da rashin isasshen zuba jari don farfado da tsarin zamanantar da wutar lantarki.

Ministan ya kuma jaddada bukatar cike gibin mita na sama da kashi 50 bisa dari, yana mai cewa shirin shugaban kasa yana nufin cimma wannan ta hanyar girka mita miliyan 18 a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Ya ce an kaddamar da wutar lantarki ta tashar Solar PV mai karfin 600kW da 3MW a makarantar horar da sojojin Nijeriya domin bai wa gwamnatin tarayya kwarin gwiwa wajen magance karancin wutar lantarki.

Daraktan gudanarwa na Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA), Abba Abubakar Aliyu, ya bayyana kaddamar da aikin hasken rana na 2.5MW a matsayin wata mafita ga Nijeriya wajen samun wutar lantarki ga makarantun ilimi.

Ya kara da cewa hukumar ba kawai tana kaddamar fara wani aiki ba ne, tana kuma lura da tasirin zamantakewa, bincike, da ci gaban mai dorewa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Lantarki wutar lantarki

এছাড়াও পড়ুন:

Rasuwar Ɗantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –  Shugaban ƘasaTinubu

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu
  • Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere
  • Yara 150,000 Ake Haifa Da Cutar Sikila A Nijeriya Duk Shekara – Rahoto
  • Mutuwar Dantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya – Gov Ododo
  • Hukumar NPA Na Son Tara Kuɗaɗen Shiga Naira Tiriliyan 1.2 A 2025
  • Rasuwar Ɗantata Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –  Shugaban ƘasaTinubu
  • Ƙasashen Afrika 10 Da Suka Fi Girman Kasafin Kudi A 2025
  • Indomie Ta Kaddamar da gangamin “Ingantaccen Abinci Domin Nasara” Don Daukaka Abinci Mai Gina Jiki da Murnar samun Nasara
  • Ƙungiyar Lauyoyi Musulmi Reshen Kaduna Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Matafiya A Filato
  • Indomie Ta Kaddamar Da Shirin Gangamin Abinci Mai Gina Jiki Na ‘Ingantaccen Abinci Domin Nasara’