‘Yan Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Halaka Sojojin Sahayoniyya Tare Da Jikkata Wasu A Beit Lahiya
Published: 20th, May 2025 GMT
Wani harin kwanton bauna da rundunar sojin al-Qassam suka kai kan sojojin mamayar Isra’ila a Beit Lahiya ya yi sanadiyar halaka tare da jikkatan sojojin mamaya masu yawa
Rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta sanar da cewa: Mayakanta sun kai wani kazamin harin kwantan bauna a yankin al-Atatra da ke yammacin Beit Lahiya a arewacin zirin Gaza, inda suka yi nasarar ritsawa da sojojin mamaya masu yawa da suka yi sanadaiyyar halakar wasu daga cikinsu bayan jikkata wasu da dama.
Rundunar ta Al-Qassam ta ce: Mayakanta sun kai hari kan motocin sojin mamayar Isra’ila uku da bama-baman Shawaz guda biyu da kuma makami mai linzami, sannan kuma suka yi arangama da wata rundunar mamayar Isra’ila.
Dangane da sakamakon farmakin, rundunar ta al-Qassam ta bayyana cewa: Mayakanta sun kashe tare da raunata sojojin mamayar Isra’ila tare da nuna yadda jiragen sama masu saukar ungulu suke jigilar wadanda suka halaka da jikkata.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Iran, ta yi wa Isra’ila ruwan makamai masu linzami
Iran ta kaddamar da wasu jerin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila a matsayin maida martani kan haren haren da Isra’ila ta kai wa kasar a cikin daren ranar Juma’a.
Bayanai sun ce hare-haren na Iran sun lalata gine-gine da dama da jikkata mutane yayin da wasu rahotannin ke cewa an samu hasarar rayuka na akalla mutum biyu.
A cewar rahotannin kafofin yada labaran Isra’ila daban-daban, makamai masu linzami na iran sun fada a yankunan Tel Aviv, Haifa, Beersheba da wasu wurare.
An bayar da rahoton barna mafi muni a birnin Tel Aviv, inda akalla makami mai linzami guda ya afkawa wani bene mai hawa 50, lamarin da ya janyo fashewar wani abu mai karfi wanda ya sa hayaki ya tashi a sararin samaniyar birnin.
A cewar darektan cibiyar nazarin dabarun da huldar kasa da kasa, Amir Al-Mousawi, daya daga cikin makami mai linzamin na Iran ya afkawa wata cibiyar binciken nukiliya da ke birnin Tel Aviv.
Wasu rahotanni sun ce an kuma yi nasarar kaiwa ma’aikatar harkokin sojan Isra’ila hari.
Gwamnatin kasar ta sanya takunkumi, inda ta umarci mazauna yankin da kada su buga hotuna ko bidiyo na wuraren da makami mai linzami na Iran ya kai hari, kamar yadda kafar yada labaran Isra’ila ta bayyana.
Birgediya Janar Ahmad Vahidi, da yake magana da gidan talabijin na iran, ya ce martanin na iran mai lakabin Operation True Promise III “zai ci gaba muddin akwai bukatar hakan,” yayin da ya sha alwashin daukar fansar jinin shahidai.
Tun da farko, Vahidi ya ce an kai hari a kalla wurare 150 a harin ramuwar gayya kan gwamnatin Isra’ila, ciki har da wasu sansanonin soji masu matukar muhimmanci.