Sojojin Sudan Sun Sanar Da Kammala “Tsarkake” Birnin Kahartum Daga Dakarun RSF
Published: 20th, May 2025 GMT
A yau Talata ne dai sojojin Sudan su ka sanar da cewa, baki dayan jihar Khartum ta zama ‘yantacciya daga dakarun kai daukin gaggawa na ( RSF), bayan da su ka kwace iko da fadar shugaban kasa dake cikin birnin a watan Maris.
Kakakin rundunar sojan Sudan ya sanar da cewa; Sojojin kasar da dukkanin bangarorinsu, suna ci gaba da sauke nauyin da yake kansu na fada da rundunar kai daukin gaggawa da masu taimaka mata a cikin yanki da kuma a fagen kasa da kasa.
Kakakin rundunar sojan kasar ta Sudan ya kuma ce; Sojojin na kasar Sudan suna samun nasarori a kowace rana.
Wata majiyar soja ta sanar da tashar talabijin din aljazira cewa; dakarun RSF sun kai hare-hare akan cibiyar kiwon lafiya ta soja dake garin Um-Durman’ bayan da sojoji su ka kwace iko da yankuna masu yawa a garin da kuma makamai da albarusai a unuwar “Saliha”.
Yaki a tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar kai daukin gaggawa ya barke ne dai a tsakiyar watan Aprilu na 2023,wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan fiye da mutane 20,000 da kuma tilastawa wasu mutane miliyan 15 yin hijira, kamar yadda MDD ta bayyana.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ana Kara Samun Karuwar Sojojin HKI Da Suke Kashe Kansu
Kamfanin dillancin labarun ” Mehr” na Iran ya ambato tashar talabijin din ‘aljazira’ tana fadin cewa: ” yawan sojojin da suke kashe kansu, da kuma masu kamuwa da cutukan kwakwalwa yana karuwa.”
Majiyar tsaron ‘yan sahayoniya ta tabbatar da cewa; sojojin nasu sun shiga wannan halin ne na kashe kai da tabin kwakwalwa, tun bayan da su ka shiga Gaza.
Tun da yakin Gaza ya barke, an sami sojojin 9000 da su ka sami tabin kwakwalwa, kuma a halin yanzu suna karbar magunguna daga asibitocin mahaukata.
Su kuwa sojojin da suke kashe kansu, ba a yi musu jana’izar soja don haka ba a bayyana adadinsu.