Iran: Cikakken Goyon Bayan Amurka Ga ‘Yan Sahayoniya Ne Yake Sa Su Tafka Laifuka
Published: 16th, May 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriryar musulunci ta Iran ta sanar da cewa, saboda yadda Amurka take bai wa ‘yan sahayoniya cikakken goyon baya ne, ya sa su cigaba da aikata laifuka na kisan kiyashi akan mutanen Gaza.
Bayanin da ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta fitar, ya zo ne saboda tunawa da zagayowar lokacin da aka kori Falasdina aka kirkiri HKI, wanda ake kira da “Nakba” ta bayyana cewa; Falasdinawa ne suke da hakkin ayyana makomarsu,kuma nauyi ne na doka da halin kwarai akan kasashen duniya su takawa HKI birki akan kisan kiyashin da take yi a Gaza.
Bayanin ya sake jaddada kira da gabatar da masu hannu a kisan kiyashin al’ummar Gaza a gaban kotu domin su fuskanci sakamakon laifukan da su ka tafka.
Bayanin ya yi ishara da munin laifukan da ‘yan sahayoniyar suke tafkwa a Gaza, wanda ya shafi mata da kananan yara da ba su ji, ba su gani ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Afuwar Tinubu za ta buɗe hanyar ci gaba da aikata miyagun laifuka — Atiku
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan yadda shugaba Bola Tinubu ya yi wa wasu mutane afuwa, ciki har da waɗanda suka aikata manyan laifuka.
A cikin saƙon da Atiku ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ana yin afuwa ne ga waɗanda aka yi wa rashin adalci ko waɗanda suka nema gafara bayan sun shafe wani lokaci a gidan yari.
Yajin Aikin ASUU: Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a KadunaYa ce a wannan karon an yi wa masu safarar ƙwayoyi, masu garkuwa da mutane, masu kisan kai, da kuma masu cin hanci da rashawa afuwa.
Atiku, ya ce abin mamaki ne yadda gwamnati ke yafewa irin waɗannan mutane, a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalar tsaro da lalacewar tarbiyya, musamman tsakanin matasa masu shan miyagun ƙwayoyi.
Ya ce bincike ya nuna cewa kashi 29 na waɗanda aka yi wa afuwa suna da alaƙa da hakrar miyagun ƙwayoyi, yayin da Najeriya ke ƙoƙarin wanke sunanta a idon duniya kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi.
Atiku, ya ce maimakon wannan afuwa ta zama darasi ga masu laifi, ta zama hanyar durƙusa da ɓangaren shari’a da jami’an tsaro da ke sadaukar da rayukansu wajen kamawa da hukunta masu aikata laifuka.
Ya ƙara da cewa idan gwamnati ta fara yafe wa masu laifi, hakan zai rage ƙimar shugabanci kuma ya ƙarfafa wa masu aikata laifuka su ci gaba da aikata su.
Atiku ya jaddada cewa Najeriya tana buƙatar shugabanci na gari wanda zai tabbatar da adalci a shari’a, ba tare da nuna bambanci ba.