2025-05-19@01:27:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3254

«Manyan Mata»:

    Ga yadda ake yi: Ki jika auduga da miski mai kamshi. Ki shafa a wurin da jinin haila ya tsaya don tsafta da jin kamshi. Sauya Tufafi da Shirya Sabuwar Tsabta Ki tabbatar kin canza tufafin da kika sa lokacin haila. Ki yi amfani da sabbin kayan ciki don jin tsabta. Komawa Ibadah Bayan wankan...
    Aƙalla ’yan kasuwa 15 ne aka kashe a wani sabon hari da wasu ‘yan bindiga suka kai wasu garuruwa da ke Ƙaramar Hukumar Agatu a Jihar Binuwai. ’Yan kasuwar na kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar Oweto da yammacin ranar Asabar lokacin da aka kai musu hari a kusa da garuruwan Ogwumogbo da Okpo’okpolo....
    Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, ta biya wa maniyyatan jihar 2,047 kuɗin hadaya domin sauƙaƙa musu wajen hidimomin aikin Hajji na shekarar 2025. Amirul Hajji kuma Mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Lawal Jobe, ne ya bayyana haka a ranar Lahadi yayin da yake yi wa mahajjatan jirgin farko bankwana kafin...
    Wani babban jami’in hukumar jin daɗin alhazai ta babban birnin tarayya Abuja wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya tabbatar da cafke Yahaya Zango inda ya ce ya daɗe yana wasan ɓuya tsakaninsa da jami’an tsaro kafin dubunsa ta cika a yau. “Ya so ya shige cikin sauran alhazai amma tuni jami’an tsaro sun gama...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Za ki samu kaza sai ki wanke ta, sannan ki tabbatar kin tsane mata ruwa ba’a barinta da ruwa ko kadan, sai ki zuba magi da gishiri da kori da kayan yaji da tafarnuwa idan kin so za ki dakata ko ki zuba ta haka, sai ki cakuda sosai ya shisshiga cikin kazar, sannan ki...
    Rahotanni daga kasar DRC sun ce  a ranar Litinin din da ta gabata kungiyar ‘yan tawaye ta M23 ta kori fararen hula 181  daga garin Goma zuwa kasar Rwanda. Kungiyar ta zargi fararen hular da ta kora da cewa, ba ‘yan kasa ba ne, asalinsu daga kasar Rwanda ne. Bugu da kari an gabatar da...
    A wani rahoton da MDD ta fitar a cikin kwanakin nan, ya bayyana cewa, tun daga 2024 ne yunwar da ake fuskanta a duniya ta kara tsanani domin ta shafi mutanen da sun kai miliyan 295. Rahoton  ya kara da cewa; wannan adadin na mutanen dake fama da yunwa mai tsanani suna warwatse a cikin...
    Wani jami’in Hukumar Sibil Difens, Abubakar Abdulkadir Mayos, ya mayar da kuɗin wata maniyyaciya Naira 822,038 da suka ɓata a sansanin alhazai na Yola da ke Jihar Adamawa. Kuɗin da aka samu sun haɗa da dala $505 da Riyal 30 na ƙasar Saudiyya, wanda ya kai kimanin Naira 822,038. An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin...
      Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood? Kin san komai a rayuwa akwai abin da Allah ya tsara maka kuma duk abin da Allah ya tsara maka za ka ga sai ya tabbatu, ni dai farko mahaifiya ta zan iya ce miki tsohuwar furodusa ce ta taba ‘producing film’ a...
    Wani mutum da ake nema ruwa a jallo bisa zargin garkuwa da mutane an kama shi a sansanin alhazai da ke Abuja. Wata majiya daga jami’an tsaro ta tabbatar wa wakilinmu cewa an kama wanda ake zargin, mai suna Yahaya Zango, yayin da ake tantance takardun maniyyatan da ke shirin tafiya Ƙasar Saudiyya domin aikin...
    Kamar yadda mujallar ta bayar da rahoto a kai, rumfar fina-finai ta kasar Sin ta zama wata alama da ke nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kyautata cudanyar al’adu da hadin gwiwar kasa da kasa a harkar fina-finai. Kana, bisa samun karuwar jawo hankulan kasashen duniya da kuma kafa kwakkwarar turbar fasahar kirkira...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta ceto wata tsohuwa mai shekaru 80 da aka sace a Jihar Kano, bayan wani samame da suka kai Ƙaramar Hukumar Garki. A yayin samamen, sun kashe mutane biyar da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, sannan sun kama wasu biyar. Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan...
    Yanayin da ’ya’yan shugabanni suke yin fito-na-fito da masu ƙalubalanta ko yin tambaya a kan abubuwa ko matakan da iyayensu suka ɗauka, sai ƙara muni yake yi a fagen siyasar Najeriya. Abin da da ke ƙara zama ruwan dare a Najeriya shi ne yadda a duk lokacin da mutane suka tambayi shugabanni ko suka ƙalubalanci...
    Yanayin da ’ya’yan shugabanni suke yin fito-na-fito da masu ƙalubalanta ko yin tambaya a kan abubuwa ko matakan da iyayensu suka ɗauka, sai ƙara muni yake yi a fagen siyasar Najeriya. Abin da da ke ƙara zama ruwan dare a Najeriya shi ne yadda a duk lokacin da mutane suka tambayi shugabanni ko suka ƙalubalanci...
    Hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sin ta bayyana cewa, gidajen tarihi na sassan kasar sun gudanar da bukukuwan nune-nunen kayayyaki 43,000, da tarurrukan ilimi 511,000. An bayyana wadannan alkaluman ne a yau Lahadi a wani bikin tunawa da ranar gidajen tarihi ta duniya a gidan adana kayayyakin tarihi na babban mashigin ruwa wato...
    A wancan lokacin, Sarkin Abuja shi ne Marigayi Sulemanu Barau, wanda ya rasu a shekarar 1979. Saboda hikimarsa da hangen nesa, ya ga cewa zai fi dacewa mutanensa su samu ‘yanci da asali ta hanyar kasancewa cikin wata jiha a kasar tarayya, fiye da su kasance a cikin wani yanki da ake kira kasar kowa...
    Gwamnati dai ta nisanta kanta daga labarin na karya, inda ta kwatanta batun da cewa, “mai tada hankali da rashin izini”.   Gwamnatin jihar ta kuma gargadi dukkan masu rike da mukaman siyasa da su daina bayyana ra’ayoyinsu da sunan Gwamnati kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi siyasa ba tare da tantancewa ba.  ...
    Samar da kyakkyawar sadarwa a tsakaninku Yawan magana da sadarwa mai kyau na hana matsala girma. Idan wani abu ya dame ku, kada ku boye, ku gaya wa juna ta hanya mai dadi da girmamawa. Gujewa kwatanta rayuwarku da ta wasu Kowanne aure yana da nasa halin. Kada ku kwatanta rayuwarku da ta wasu, domin...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin dakatar da wani hadiminsa, Ibrahim Rabi’u nan take daga muƙaminsa.  Abba ya dakatar da hadimin ne wanda yake ɗauko masa rahoto a ma’aikatar sufuri, saboda wasu kalamai da ya furta kan tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Kwale-kwale ya nutse da mutum 37 a Kwara...
    Iran ta yi kira da a kawo karshen neman shafe wata al’umma daga kan doron kasa tare da kawo karshen rashin hukunta shugabannin ‘yan sahayoniyya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan hare-hare da laifukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take ci gaba da yi a cikin ‘yan kwanakin nan...
    Wani hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 37 a ƙauyen Gbajibo-Mudi da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara. Hatsarin wanda ake fargabar ya auku ne a sanadiyar ɗaukar fasinjoji fiye da kima ya faru ne da yammacin ranar Alhamis da ta gabata. Shin PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta nan da zaɓen 2027? Ainihin...
    Hukumomin kasar za su fitar da gamsasshen bayani mai dauke da sababbin tsauraran matakan, wadanda za su kunshi na mallakar izinin karatu da aiki a Birtaniya. Sakataren harkokin baki na Birtaniya Ybette Cooper ta bayyana wa BBC cewa lokaci ya yi da za su rage daukar ma’aikatan jinya daga kasashen waje. Ta ce wannan matakin...
    Dare da aka zubar da jini mafi muni a Gaza: Sama da Falasdinawa 80 ne suka yi shahada a sassa daban-daban na Zirin Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula a yankuna daban-daban na zirin Gaza, inda suka yi sanadiyyar shahadan sama da Falasdinawa 80, kuma mafi yawansu...
    Sojojin Libiya sun ‘yantar da fursunoni da dama daga gidajen yari na sirri da ke karkashin dakarun Tallafawa da Wanzar da Kwanciyar hankali na Kasar Sojojin kasar Libya a birnin Tripoli fadar mulkin kasar sun ‘yantar da fursunoni da dama da ake tsare da su a gidajen yari na sirri karkashin hukumar “Tallafawa da wanzar...
    Sauran sassan da aka gyara da kuma saka kayan aiki sun haɗa da sashen Kulawa da Mata (ANC), ɗakin tiyata, ɗakin X-ray, sabon ginin hukunta asibiti, masallaci, gidan Babban Daraktan Lafiya (gidaje mai ɗakuna 3), da kuma sashen kula da yara, da dai sauransu.   A yayin jawabinsa a wajen ƙaddamar da aikin, Gwamna Lawal...
    An yi wa ɗan wasan gaba na ƙungiyar Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi allurar barci mai nauyi domin taimaka masa murmurwa daga tiyatar da aka yi masa. Bayanai sun tabbatar cewa an garzaya da ɗan wasan ɗan asalin Nijeriya asibiti ne domin yi masa tiyata a ranar Litinin, bayan ya samu mummunan rauni a cikinsa a...
    A cewarsa, baban dalilin da ya sa suke wannan aiki shi ne, domin a rage wa al’umma musamman masu karamin karfi wahalwalun da suke sha wajen neman lafiya. Malam Hussaini ya yi kira ga sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da su ba da tasu gudummawa wajen irin wannan aiki ta yadda za su...
    Babbar Jam’iyyar hamayya ta PDP ta ce, ta soma ɗaukar matakan ɗinke ɓarakar da ta dabaibaye ta a ’yan shekarun nan. Matakin baya-bayan nan shi ne na taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar ta gudanar. Guguwar raba Masarautar Katsina ta kunno kai Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma Shin ko hakan...
    Bayan da wani matashi ɗan shekara 33 ɗan kasar Japan mai suna Honkon ya yi tarin kuɗi na tsawon shekaru 10 don siyan motar da yake mafarki — na wata sabuwar mota ƙirar Ferrari 458 Spider — sai ya zauna yana kallon yadda motar take ƙonewa cikin sa’a ɗaya da tuƙa ta a karon farko....
    Ya ce da Kwankwaso bai yi tunanin samar da jami’ar Wudil ba, da wannan alherin ba za a same shi ba, suna gode wa sauran wadanda suke ba da gudummawa wajen habakar wannan jami’ar. Alhaji Abdukadir ya yi kira ga magoya baya da masu tasowa cewa idan suka sami dama su yi koyi da jagoran...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya caccaki kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan a ziyarar da ya kai a kasashen yankin Gulf na Farisa, yana mai cewa kalaman abin kunya ne a gare shi da dukkan Amurkawa, kuma bai cancanci amsa ba. Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya...
    An gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu a sassa daban-daban na duniya, a yayin zagayowar cika shekaru 77 da ranar ‘’Nakba’’ cewa da masifa. A Faransa da Ingila duk an gudanar da wannan zanga zanga a wasu sassan kasar. A cikin jerin gwanon, an daga allunan da ke dauke da sakonni irin...
    Iran ta yi kakkausan suka game da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa kan kasar Yemen tana mai danganta su da babban laifin yaki. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa hare-haren da gwamnatin Isra’ila ke kai wa kan ababen more rayuwa na tattalin arzikin kasar Yemen da kuma cibiyoyin jama’a...
    Aƙalla manoma 50 ne suka rasu, sakamakon wani mummunan hari da ‘yan ta’addan ISWAP suka kai garin Malam Karanti da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa, a jihar Borno. Majiyoyi sun ce mayaƙan sun afka wa manoma yayin da suke noma da kamun kifi, duk da cewar suna biyan haraji kafin yin noma. Tinubu ya isa Rome...
    Hukumar kula da ayyukan sama jannati ta kasar Sin ta ce masu bincike sun tabbatar da wata sabuwar halitta da aka samu a cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, wanda aka yi wa lakabi da Niallia Tiangongensis   A watan Mayun 2023 ne, tawagar ‘yan sama jannati ta kumbon Shenzhou-15 ta gano wani...
    Farfesa Radda ya ce an cire ‘yan takara masu yawa da suka cencenta saboda rashin adalci, duba da cewa sun cika dukkan sharadan da ya dace wajen neman mukamin shugabancin makarantar.  Haka kuma, Farfesa Bichi ya ce zargin da ake masa ba gaskiya ba ne, yana mai cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da...
    Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar? Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare? Akwai wani kirkirarren...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya isa birnin Rome na Ƙasar Italiya domin halartar bikin rantsar da sabon Fafaroma, Leo na XIV. Za a gudanar da bikin ne a wajen wani taron addu’a da ake kira “solemn mass” a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu. Crystal Palace ta lashe kofin FA na farko a tarihinta...
    Farfesa Radda ya ce an cire ‘yan takara masu yawa da suka cencenta saboda rashin adalci, duba da cewa sun cika dukkan sharadan da ya dace wajen neman mukamin shugabancin makarantar.  Haka kuma, Farfesa Bichi ya ce zargin da ake masa ba gaskiya ba ne, yana mai cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yi watsi da wasu kalaman shugaban kasar Amurka Donal Trump a ziyar da ya kammala a wasu kasashen larabawa na yankin Tekun farisa, ya kuma bayyana wasu kalamansa a matsayin kungiya ga kansa da kuma mutanen Amurka. Har’ila yau Jagoran ya kara...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa  aiwatar da yarjeniyar zaman zaman lafiya wadanda aka cimma tsakanin kasashen Armenia da kuma Azerbaijan da gaggawa zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto Aragchi yana fadar haka a lokacin...
    Cikin jawabin da ya gabatar ta bidiyo, mataimakin ministan kula da al’adu da yawon bude ido na kasar Sin Rao Quan, ya ce dawowar rubuce-rubucen na Wuxing Ling da Gongshou Zhan, na tabbatar da cewa za a iya nazarta da kare wadannan kayayyakin gargajiya masu daraja yadda ya kamata a mahaifarsu. (Fa’iza) Daga kanmu,...
    Kwanan nan ne Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoton dake sabunta hasashen yanayin tattalin arzikin duniya gami da makomarsa na shekara ta 2025 a tsakiyar shekarar da muke ciki, inda rahoton ke ganin kara harajin kwastam da rashin sanin tabbas game da manufofin cinikayya sun janyo tabarbarewar makomar tattalin arzikin duk duniya, tare da...
    Jagoran jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ƙaryata wani rahoto da ke yawo cewa yana shirin shiga sabuwar haɗakar siyasa. A wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, Kwankwaso ya bayyana rahoton a matsayin “karya, ba shi da tushe kuma makircin wasu ‘yan siyasa ne.” Riƙaƙƙun ’yan daba da...
    Kwamitin Haɗin Gwiwa na Jihar Kano kan Tsaro da Gyaran Matasa, ya kama ’yan daba 31 a wani samame da ya gudana a unguwanni bakwai a jihar. An kai samamen ne daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Mayu, 2025 ƙarƙashin jagorancin Dokta Yusuf Ibrahim Kofar Mata. Tsafta a gidan aure: Abubuwan da kowace mace...
    Tsafta tana kasancewa wani muhimmin ɓangare na rayuwar mace. Duk da cewa galibi ana alaƙanta tsafta da kyawun gani ko ƙamshi, sai dai a zahirin gaskiya tsafta ta wuce gaban haka ce. Ita ce turbar zaman lafiya a gidan aure, makamin janyo soyayya, da ginshiƙin lafiyar jiki da tunani. Hajj: Ranar Lahadi za a fara...
    Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun yi wa manona da masunta aƙalla 15 yankan rago a yankin Baga da ke Ƙaramar Hukumar Kulawa ta Jihar Borno. Rahotanni sun bayyana cewa mayaƙan na ISWAP sun kutsa yankin ne bayan zagargaza da tarwatsa sojoji suka yi wa maɓoyarsu da ke Dajin Sambisa. Shaidu sun bayyana cewa a ranar Laraba...
    A Premier League, kungiyoyi sun gama sanin Man United ciki da waje. “Dalili shi ne su kan hadu sau biyu duk shekara. Sun san abin da za su tarar game da ‘yanwasan United din da kuma filin wasanta, a gasar zakarun Turai kuma, akasari wannan ne karon farko da suke zuwa filin wasa na Old...