2025-07-08@06:32:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6495
«Shugaban majalisar»:
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ‘Yan Najeriya suna ci gaba da tafka muhawara a kan wanda jamiyyar hadaka ta ADC zata tsayar takarar Shugaban Kasa a zaben 2027. Yayin da wasu suke ganin Atiku Abubakar yana da dimbin magoya baya, wasu kuwa gani suke yi shi ma Peter Obi ba kanwar lasa bane. Ko me zai faru idan daya daga cikin su ya samu tikitin tsayawa takara a 2027? NAJERIYA A YAU: Mene ne tasirin naɗin Mataimaka na Musamman a rayuwar jama’a? DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan wannan lamari. Domin sauke shirin, latsa nan
Ɗan wasan gaban Napoli, Victor Osimhen, ya amince da komawa Galatasaray na dindindin, wani ɗan jarida a Nijeriya kuma makusancin Osimhen, Buchi Laba ne ya bayyana hakan. Ya ce “Osimhen ya bayyana cewa yana son komawa Galatasaray daga Napoli, duk da cewar ƙungiyar ta ƙasar Italiya na fatan ci gaba da kasancewa da tsohon ɗan wasan na Lille, Bula ya rubuta a shafinsa na X. Manyan Kugiyoyin Gasar Firimiya Sun Fara Zawarcin Victor Osimhen Rashin Osimhen A Cikin Tawagar Nijeriya Babbar Asarace – Samson Siasia Yayin da yake zaman aro a Galatasaray, Osimhen ya taimakawa ƙungiyar ta lashe gasar Super Lig ta Turkiyya, ɗan wasan na Super Eagles ya zura ƙwallaye 25 a wasanni 36 da ya buga, hakan yasa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamna Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutane 48,000 domin jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙara ƙarfafa matakan kiwon lafiya a matakin farko a fadin Jihar Yobe. Buni ya bayyana shirin fara samar da daidaito a bangaren kiwon lafiya wanda zai samar da inshorar lafiya ga mata masu rauni da yara ‘yan kasa da shekaru biyar sama da 38,000 a fadin jihar. Dalilin da matan karkara a Kano suka fi son haihuwa a gida Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya Gwamnan ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba yayin da ya kaddamar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin fadada harkokin kiwon lafiya, musamman ga marasa galihu. Ya bayyana hakan ne a ranar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar raya kasa da aiwatar da gyare gyare ta kasar Sin (NDRC) ta ce kasar za ta kara daukaka tsarin wuraren cajin lantarki da gina tsarin ta yadda zai zama mai inganci da ingantaccen lantarki da kyakkyawan fasali, da amfani da fasahohin zamani. NDRC da wasu hukumomin gwamnati 3 sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa game da bangaren a yau, inda suka ce wuraren cajin ababen hawa masu amfani da lantarki na da muhimmanci matuka wajen goyon bayan raya masana’antar kera ababen hawa masu amfani da lantarki da ginin sabon tsarin samar da lantarki tare da rage fitar da hayakin Carbon a bangarorin sufuri da na makamashi Zuwa karshen shekarar 2027, kasar Sin na sa ran samun sama da...
Gwamna Mai Mala Buni, ya ƙaddamar da tsarin inshorar lafiya na mutane 48,000 domin jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙara ƙarfafa matakan kiwon lafiya a matakin farko a fadin Jihar Yobe. Buni ya bayyana shirin fara samar da daidaito a bangaren kiwon lafiya wanda zai samar da inshorar lafiya ga mata masu rauni da yara ‘yan kasa da shekaru biyar sama da 38,000 a fadin jihar. Dalilin da matan karkara a Kano suka fi son haihuwa a gida Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya Gwamnan ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba yayin da ya kaddamar da wasu sabbin tsare-tsare da nufin fadada harkokin kiwon lafiya, musamman ga marasa galihu. Ya bayyana hakan ne a ranar...
An gudanar da taron kafa kungiyar masana masu binciken sararin samaniya mai zurfi ta kasa da kasa wato IDSEA a birnin Hefei dake lardin Anhui, yau Litinin. Wannan ita ce kungiyar masana kimiyya da fasaha ta kasa da kasa ta farko da kasar Sin ta kafa a fannin binciken sararin samaniya mai zurfi. A cikin watan Afrilun bana ne majalisar gudanarwar kasar Sin ta amince da kafa kungiyar IDSEA, wadda kungiyoyi guda 5 suka ba da shawarar kafa ta tare, ciki har da cibiyar binciken duniyar wata da ayyukan binciken sararin samaniya ta hukumar kula da sararin samaniya ta kasar Sin, da cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar Faransa mai suna “Planetary Exploration, Horizon 2061.” Kuma ta zama wata kungiya...
Wata ƙungiya mai zaman kanta, Nigeria Health Watch ta ce ta gano har yanzu fiye da rabin matan da ke zaune a yankunan karkarar Jihar Kano sun fi son haihuwa a gida a maimakon zuwa asibiti. Kungiyar ta alaƙanta hakan da al’adun mutanen, waɗanda ta ce an fi samun masu su a ƙauyuka da kuma yankunan karkara fiye da a birane. Daraktar shirye-shirye ta ƙungiyar, Kemisola Agbaoye ce ta bayyana hakan ranar Litinin, yayin gabatar da rahoto a wani taron masu ruwa da tsaki don bayyana abubuwan da suka gano a binciken da suka gudanar a ƙananan hukumomi shida na jihar. Cutar Diphtheria ta yi ajalin ƙananan yara 3 a Zariya Amurka za ta ɗauki nauyin ’yan tawaye domin yaƙi...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a birnin Yangquan na lardin Shanxi a yau Litinin. Shugaban ya ziyarci dandalin da aka kebe domin tunawa da katafaren gangamin soji na yaki da harin Japan, inda ya gabatar da furanni ga wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin. Ya kuma ziyarci babban dakin tunawa da gangamin. Shugaban ya kuma yi bitar irin jarumtar da sojojin suka yi yayin yakin da kuma tarihin yadda JKS ta jagoranci sojoji da al’umma wajen hada kai domin yakar ‘yan adawa da bijirewa kutsen Japan, da fahimtar tarihin juyin juya hali a wurin da gado da yayata ruhin yakin kin harin Japan. Daga baya, ya je wani kamfanin kere-kere na valve dake birnin, inda ya fahimci...
(ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya. Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba Hakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar Alfijir Labarai a safiyar Litinin. Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga...
(ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 8, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar wannan ayyukan, akan farashin kaso 50% cikin 100 shima za a biya. Labari Mai Daɗi: Asibitin Kwararru Mai Zaman Kansa A Kano Ya Rage Kaso 50 Na kuɗaɗen Ayyukansu Asibitin Aminu Kano Ya Musanta Cire Mahaifar Mara Lafiya Ba Tare Da Izini Ba Hakan na kunshe ne cikin wata sanar da shugaban asibitin Alh Auwal Muhd Lawal ya bayyanawa jaridar Alfijir Labarai a safiyar Litinin. Lawal yace sun yanke wannan hukuncin ne sakamakon buƙatar da al’umma suke da ita a wannan bangarorin ga...
Wannan lamari ya buɗe sabon shafi a siyasar ƙasar nan, inda ƴan adawa suke ci gaba da cewa zuwan sabuwar jam’iyyar wani sauyi ne da za a samu a cikin ƙasar. Wani mai sharhi a kan siyasa, Sani Kabo, ya bayyana abin da ya samu shafin yanar gizon jam’iyyar a matsayin wata ƴar manuniya ga irin buƙatar da ake da ita wajen sauya sheƙa da kuma haɗin kan ƴan adawa, inda ya misalta abin da yake faruwa da shekara ta 2013, lokacin da aka samar da jam’iyyar APC wadda ta kawo karshen mulkin jam’iyyar PDP a wancan lokaci. Shima wani masanin siyasa a Nijeriya wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce wannan ya nuna yadda al’ummar ƙasar suke buƙatar...
Kananan yara uku sun rasu yayin da wasu da shidan ke kwance a asibiti sakamakon sake bullar cutar nan ta mashako a garin Zariya da ke Jihar Kaduna. Wani mazaunin unguwar Kwarbai a yankin na Zariya, Mallam Bashir Magaji wanda ya rasa ’yarsa sakamakon barkewar cutar wadda a turance ake kira Diphtheria, ya bayyana yadda take bazuwa cikin sauri a kwanakin nan. Kira ga Haƙuri: A Dakatar da Ƙirƙirar Sabbin Masarautu a Jihar Bauchi Amurka za ta ɗauki nauyin ’yan tawaye domin yaƙi da ta’addanci A cewarsa, ’yarsa da ta nuna alamun kamuwa da cutar na kumburin wuya da sarkewar numfashi, an gaggauta mika ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, amma daga bisani ta ce ga...
Kasar Sin ta gudanar da bikin cika shekaru 88, da dukkan al’ummar kasar ta fara yakin kin jinin harin sojojin Japan a yau Litinin. Inda a wani bangare na bikin aka kaddamar da wani baje koli mai taken “Domin ‘yantar da kasa da zaman lafiyar duniya”. An gudanar da bikin tare da baje kolin ne a babban dakin adana kayayyakin tarihi masu nasaba da yakin, wanda ke kusa da gadar Lugou, wadda kuma ake kira da “Marco Polo Bridge”, wurin da sojojin Japan suka fara kaiwa sojojin kasar Sin hari a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 1937, lamarin da ya zamo tushen mamayar da sojojin na Japan suka yiwa kasar Sin. Zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS,...
Kamfanin jirgin sama mallakar jihar Enugu, wato Enugu Air, ya fara aiki a hukumance ranar Litinin bayan ƙaddamar da shi a filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu. Mutane da dama sun halarci bikin ƙaddamarwar tare da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, da sauran manyan baki da suka halarci bikin ƙaddamarwar. APC Ta Tafka Asara, Wani Jigo Ya Fice A Enugu Masu Gida Sun Yi Ruwan Kwallaye A Enugu Enugu Air wani ɓangare ne na hangen nesa da ƙudurin Gwamna Peter Mbah, don inganta harkar sufuri da mayar da Enugu cibiyar jiragen sama a Nijeriya. Kamfanin ya fara aiki da jirage uku na Embraer E170 da E190, wadanda suka dace da zirga-zirgar cikin gida. Jirgin zai fara tashi tsakanin...
A yau Litinin ne kungiyar ta Hizbullah ta fitar da sanarwa wacce ta kunshi yin Allawadai da harin ta’addancin da HKI ta kai wa kasar Yemen, wanda ya shafi tasoshin jiragen ruwa da muhimmacin cibiyoyin kasar. Bayanin na Hizbullah ya kuma ce; Makiya suna tsammanin cewa ta hanyar wannan irin harin na wuce gona da iri za su yi hana Yemen ci gaba da matakin da take dauka na daukaka wajen taimakawa Gaza, ta daina kai hare-hare masu tsanani da take kai musu. Haka nan kuma Hizbullah ta ci gaba da cewa: Har yanzu ‘yan sahayoniya sun kasa fahimtar dabi’ar mutanen Yamen masu hakuri da juriya akan tafarkin jihadi, domin akida ce, cewa gaskiya ita ce wacce ta cancanci a...
Rahotanni da suke fitowa daga kasar ta Kenya sun ce tun safiyar yau Litinin ne ‘yan sanda su ka rufe muhimman hanyoyin da su ka nufi tsakiyar babban birnin kasar Nairobi da kuma muhimman cibiyoyin kasuwanci. Kafafen watsa labarun kasar ta Kenya sun ce da akwai jami’an ‘yansanda masu yawa da aka girke su a cikin muhimman wurare da shatale-tale a cikin birnin da kuma hanyoyin da suka nufi fadar gwamnati. Dubban mutane ne su ka fito titunan birnin Nairobi domin nuna kin amincewarsu da salon Mulki William Ruto wanda suke zargi da cin hanci da rashawa da kuma kama karya. Zanga-zangar ta yau dai ana ba ta sunan; 7/7, wacce ta samo asali a 1990 da al’ummar kasar su...
Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; kungiyar leken asirin HKI ta cikin gida, “Shabak” ta kama shugaban ofishinta a Falasdinu dake karkashin mamaya Nasir al-Lahham, a gidansa da yake a garin Beithlaham. Majiyar ta kara da cewa; Jami’an kungiyar leken asirin ta “Shabakh” sun dade suna binciken dakin watsa labarin da Lahham yake watsa shirye-shiryensa. Tashar ta “Almayadin’ dai ta bayyana cewa kamun da aka yi wa ma’aikacin nata yana a karkashin Takura mata ne da HKI take yi, domin a cikin watan Oktoba na 2023 ma dai jami’an tsaron sun kai hari cikin gidansa, su ka ci zarafin maidakinsa da kuma kama ‘ya’yansa Basil da Baasil.

Firaministan Kasar Sin: Kasarsa Ta Kimtsa Tsaf Wajen Inganta Aikin BRI Da Bunkasa Kasuwanci Da Zuba Jari Tare Da Habasha
A nasa bangaren, Abiy ya ce Habasha da Sin amintattun kawaye ne na manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, kuma kasarsa tana mika tsantsar godiya ga kasar Sin saboda goyon bayan da ta dade tana bai wa Habasha a fannin raya tattalin arziki da zamantakewa. Yayin da yake nuni da irin muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a harkokin kasa da kasa, musamman a fannin raya ci gaban duniya, Abiy ya ce Habasha a shirye take ta rubanya mu’amala a matakin koli da kasar Sin da kuma zurfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Saboda matsin lamba na doka da kuma la’akari da mahimman batutuwan siyasa, ya zama dole Gwamnatin Jihar Bauchi ta dakatar da duk wani ci gaba na aikin kwamitin da aka kafa a ranar 4 ga Yuli 2025 domin duba yiwuwar ƙirƙirar sabbin masarautu ko sauye-sauye ga tsarin majalisun gargajiya—musamman a yankunan da har yanzu ke fuskantar shari’a a kotu. Ci gaba da wannan lamari mai sarkakiya alhali wasu muhimman ƙarar shari’a na ci gaba a kotuna, ba wai kawai zai saɓa wa kundin tsarin mulki da ikon shari’a ba, har ila yau, zai iya haddasa tayar da jijiyoyin wuya a cikin al’umma, musamman a yankunan da ke da tarihi na rikice-rikicen ƙabilanci kamar Tafawa Balewa da kewaye. Wannan kira na...
Ma’aikatar Tsaron Amurka Pentagon ta ware dala miliyan 130 a kasafin kudinta na 2026 karkashin Yaƙi da ISIS da Kudin Kayan Aiki (CTEF) don taimaka wa kungiyoyi masu dauke da makamai a Syria, cikin su har da SDF da YPG ta mamaye. Wannan dai na zuwa ne a yayin da Siriya ke ci gaba da fuskantar rashin kwanciyar hankali da kalubale masu yawa tun bayan kawo karshen mulkin Bashar al-Assad. Bidiyon tsiraici: Babiana ta sake jawo ce-ce-ku-ce Madatsar Ruwan Lagdo na yi wa jihohi 3 na Nijeriya barazanar ambaliya Manyan matsaloli sun haɗa da kasancewar kungiyoyi masu dauke da makamai daban-daban, rikice-rikicen filaye da ba a warware ba, tsoma bakin sojojin ƙasashen waje, da tattalin arziki mai rauni wanda ke...
A ƙarshe, lauyoyin Majalisar sun ja hankalin lauyoyin Sanata Akpoti-Uduaghan da su yi taka-tsantsan don kauce wa yi wa kundin tsarin mulki kutse ko sanya rikici a majalisa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ƙarshen makon da ya gabata ne fitacciyar ’yar TikTok wacce aka fi sani da Babiana ta fitar da wani sabon bidiyo tana rusa ihu tana kira ga Shugaba Bola Tinubu da wasu mawaƙan kudancin Najeriya da su shiga tsakaninta da ’yan Arewa a kan abin da tace suna yi mata na cin zarafi tun bayan bayyanar bidiyo tsiraicinta a shekarar 2024. Babiana ta yi bidiyon ne cikin harshen Ingilishi inda ta ce ba a yi mata adalci a Arewa kuma ana barazana da rayuwarta. Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos Ta bayyana cewa tsawon shekara ɗaya ta yi tana raɓe-raɓe saboda ba ta son maganganun...
Rahotanni sun bayyana cewa mazauna wasu jihohin Nijeriya uku na cikin shirin ko-ta-kwana, sakamakon ƙaruwar fargabar samun ambaliya saboda yiyuwar sakin ruwan Madatsar Lagdo ta Kamaru. A cewar wani rahoto da jaridar Punch ta wallafa, jihohin da mazauna ke cikin zaman ɗar-ɗar sun haɗar da Benuwe da Edo da kuma Bayelsa, waɗanda tuni suka fara shiri don kauce wa barazanar ambaliyar. Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos Sai dai Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Nijeriya ta yi watsi da rahotonnin da ke cewa an buɗe madatsar ruwan, a yayin da tuni jihohin suka fara shirya wa barazanar. Gwamnatin Benuwe ta ce ta fara aikin wayar da kan...
A taron ƙungiyar BRICS na karo na 17 da aka gudanar a Brazil, ƙasashen mambobi da suka haɗa da China, India, Rasha, Saudi Arabia, Iran da wasu sun soki hauhawar haraji da manufofin kariya ta ciniki da wasu ƙasashe ke aiwatarwa. A sanarwar da suka fitar, sun nuna damuwa kan rikicin Gabas ta Tsakiya, amma sun kaucewa sukar Rasha kai tsaye dangane da rikicin Ukraine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Kula da Muhalli ta Jihar Jigawa (JISEPA) ta yi kira ga al’umma da su ba da hadin kai wajen tabbatar da tsafta da kuma bayar da rahoton duk wani da ake sayarwa da ba bisa ka’ida ba, ko kuma cikin rashin tsafta. Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Adamu Sabo ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa. A cewarsa, wannan kira ya zama wajibi sakamakon nasarar da hukumar ta samu na kwace gurbatattun kayayyakin na sama da naira miliyan 14 a lokacin sintiri da binciken kayayyaki a fadin jihar daga watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2025. Alhaji Adamu Sabo ya kara da cewa, mafi yawancin kayayyakin da aka kwace na...
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari da safiyar Litinin a unguwar Ogaminana da ke ƙaramar hukumar Adavi a Jihar Kogi, inda suka kashe wani Soja ɗaya da aka tura domin bayar da kariya ga ma’aikatan kamfanin gine-gine. Wata majiya daga yankin ta shaida wa LEADERSHIP cewa maharan sun mamaye wurin aikin ne da safe, inda suka yi awon gaba da wani ɗan ƙasar China da ke aiki a wurin. An bayyana cewa bayan harin, maharan sun ajiye motarsu a kusa da tashar watsa shirye-shiryen Radio Kogi da ke Otite, da nisan ‘yan mitoci kaɗan daga inda suka sace ɗan Chinan. CHINADA Ta Nuna Matukar Adawa Da Gasar Wasannin Da Aka Amince Da Kwayoyin Kara...
Wata babbas bas din haya kirar Macarpollo dauke da fasinjoji ta yi hatsari a garin Jos, hedikwatar Filato. Motar mai daukar fasinjoji 56 ta yi hatsari ne bayan isowarta Mahadar Vom da Anguldi da ke Jos, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Hatsarin ya auku ne kimanin milomita 10 kafin motar ta isa inda za ta tsaya bayan doguwar tafiyar mai nisan kilomita. Wakilinmu ya gano cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4 na asubahin ranar Litinin din nan, inda motar ta lalata kusan daukacin shagunan da ke wurin da ta yi hatsari. ’Yan Boko Haram sun kashe mutum 9, skun Jikkata 4 a Borno Turji: Gwamnatin Sakkwato ta ba da sharadin sulhu da ’yan ta’adda Wani mazaunin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya reshen jihar Kano, ta bayyana cewa Fursunoni 58 suna rubuta Jarrabawar Kammala Sakandare ta Kasa NECO ta shekarar 2025. Wannan ci gaba ya samu ne bayan biyan kudin rajista da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi. Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Kofar-Nasarawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Kano. Ya ce wannan karamci na gwamnatin jihar Kano shaida ce ta jajircewarta wajen kula da walwalar fursunoni, gyaran dabi’unsu da kuma dawo da su cikin al’umma yadda ya kamata. “Biyan kudin rajistar jarrabawa da gwamnatin Kano ta yi alama ce ta jajircewarta wajen samar da dama ga fursunoni domin su...

Araqchi Ya Gana Da Babban Malamin Yahudawa Mai Adawa Da ‘Yan Sahayoniyya A Gefen Taron Kungiyar BRICS
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da babban malamin yahudawa rabbi mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron BRICS a Brazil Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana kuma ya zanta da wani babban malamin yahudawa mai adawa da ‘yan sahayoniyya a gefen taron kasashen BRICS a kasar Brazil. Rabbi Yisrael Dovid Weiss, wanda ya je Brazil domin ganawa a gefen taron BRICS, ya gana da ministan harkokin wajen Iran, inda suka yi musayar ra’ayi da shi. Wani abin lura shi ne cewa a baya malamin ya ziyarci ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke kasar Brazil bayan bude littafin ta’aziyya ga shahidan da yahudawan sahayoniyya da suke kai wa hari a kasar hari. A...
Wata babbas bas din haya kirar Macarpollo dauke da fasinjoji ta yi hatsari a garin Jos, hedikwatar Filato. Motar mai daukar fasinjoji 56 ta yi hatsari ne bayan isowarta Mahadar Vom da Anguldi da ke Jos, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Hatsarin ya auku ne kimanin milomita 10 kafin motar ta isa inda za ta tsaya bayan doguwar tafiyar mai nisan kilomita. Wakilinmu ya gano cewa hatsarin ya auku ne da misalin karfe 4 na asubahin ranar Litinin din nan, inda motar ta lalata kusan daukacin shagunan da ke wurin da ta yi hatsari. Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da faruwar lamarin.
Shugaban kasar Rasha ya aike da sako mai zafi wa kasashen Yammacin Turai da suke tallafawa Ukraine A daidai lokacin da yakin Rasha da Ukraine yake ci gaba da ruruwa, kuma har yanzu an gagara cimma tsagaita wuta. Sabbin abubuwan da suka faru a fagen sojan Rasha sun hada da ma’aikatar tsaron kasar da ta sanar da cewa sojojin kasar sun ‘yantar da garuruwan Poddubnoye na Donetsk People’s Republic da Sobolevka a yankin Kharkiv. Sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar ta bayyana cewa: Sojojin kasar Rasha sun ci gaba da zurfafa kai hare-hare kan makiya, inda suka yi ta janyo hasarar bil’adama da na dukiya kan sojojin kasar Ukraine a yankuna da dama na jamhuriyar Donetsk People’s Republic da...
Sojojin gwamnatin yahudawan sahayoniyya sun kai hare-hare kan tashar jiragen ruwa na Hodeidah a kasar Yemen Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan tashar ruwan Hodeidah da ke yammacin kasar Yemen, biyo bayan barazanar da sojojin kasar suka yi a yammacin jiya Lahadi. Majiyar Yemen ta fada a yammacin jiya Lahadi cewa: An ji karar fashewar abubuwa masu yawa a tashar jiragen ruwa na Hodeida, sakamakon farmakin da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a yankin. A cewar majiyoyin cikin gidan Yemen, sama da fashe fashe 20 ne aka samu a Hodeidah sakamakon hare-haren da jiragen saman yakin Isra’ila suka kai.
Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun yi Allah wadai da hare-haren zaluncin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yemen Kungiyar Jihadin-Islami ta Falasdinawa da sauran kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci na Falasdinu sun yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan tashar jirgin Ruwan Hodeida na kasar Yemen, tare da jaddada goyon bayansu ga shugabancin kasar da sojojin kasar da kuma al’ummar kasar ta Yemen. Kungiyar fafutukar ‘yantar da Falasdinu ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da cewa: “Kazamin harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yamen, wanda ya shafi kayayyakin more rayuwa na fararen hula da tashoshin wutar lantarki da tashar jiragen ruwa na Hodeidah da Ras Issa...
Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya rasu, yana da shekara 90 a duniya. Kakakin iyalan basaraken ne ya tabbatar da mutuwarsa da safiyar yau Litinin cikin wani saƙo da ya aike wa manema labarai. Kwanaki biyu da suka gabata ne basaraken ya gudanar da bikin cikarsa shekara 90 a duniya a wani ƙasaitaccen biki da aka gudanar a fadarsa. A shekarar da ta gabata ne aka naɗa Sarki Olakulehin a matsayin Olubadan na Ibadan bayan rasuwar wanda ya gabace shi Sarki Alli Okunmade II.
Mummunan lamari ya faru ne a lokacin da wata mota kirar bas ta kasuwanci da wata babbar mota ta yi taho-mu-gama da tare da daukar rayukan mutane 21 a hanyar Zariya zuwa Kano. Hadarin ya afku ne a Kasuwar Dogo, Dakatsale, wanda ya hada da wata motar kasuwanci kirar Toyota Hiace da wata tirela ta DAF. Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa direban motar bas din ya saba ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa, lamarin da ya kai ga yin karo da babbar motar da ke zuwa. Hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar fasinjoji 21 nan take, wadanda suka hada da manya maza 19 da manya mata 2, yayin...
Hukumomi a jihar Texas da ke Amurka sun tabbatar da mutuwar fiye da mutum 80 sakamakon ambaliyar da ta auka wa jihar tun a ranar Juma’a. Mutum 68 daga cikin waɗanda suka mutu ciki har da ƙananan yara 28, a gundumar Kerr suke. Har yanzu akwai ƴanmata 10 da mai kula da wurin shaƙatawar Mystic da ba a ji ɗuriyarsa ba. Alƙaluman waɗanda suka mutu na sauyawa cikin hanzari, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da lalubo gawarwaki. Shugaba Trump ya ce ya tsara zuwa yankin da lamarin ya faru cikin wannan mako
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce an samar da isassun matakan tsaro domin kawar da wasu gungun miyagu da ke aikata munanan laifuka a jihar. AbdulRazaq ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana wa masu ruwa da tsaki daga yankin Lafiagi na jihar Kwara ta Arewa kan dimbin kokarin gwamnatin jihar a wani taro da aka gudanar a Ilorin. Gwamnan ya amince da damuwar al’ummar tare da tabbatar musu da matakin da gwamnati ke jagoranta kan lamarin. Ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da kai hare-hare a dazuzzukan da aka gano a matsayin sansanin ‘yan ta’adda a Kwara ta Arewa da Kudu. Gwamna AbdulRazaq ya ce ayyukan za su hada da sabbin...
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta gudanar da aikin samar da wutar lantarki ga jami’ar tarayya ta Kashere da ke jihar Gombe domin tabbatar da samar da isasshen wutar lantarki domin inganta harkokin ilimi. Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen taron hadaka karo na uku na jami’ar tarayya ta Kashere da ke karamar hukumar Akko a jihar Gombe. Shugaba Bola Tinubu ya kuma bayyana cewa ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya za ta fara aikin gina madatsar ruwa a kogin Kashere domin tallafa wa shirin koyar da aikin gona na jami’ar da inganta samar da ruwa ga al’ummomin da ke kewaye. Ya jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta samar da ingantaccen ilimi ta hanyar...
A ƙarshe, Farfesa Pate ya yabawa gwamnatin tarayya bisa gina sabbin gine-gine a jami’ar kamar ginin Majalisar Jami’a, katangar jami’a, da ɗakunan kwana. Ya bayyana cewa dalibai 6,870 ne suka kammala karatu, ciki har da 91 da suka samu First Class da kuma 16 da suka kammala karatun digiri na PhD. Haka kuma, jami’ar ta karrama mutane biyar da digirin girmamawa saboda gudummawarsu ga ci gaban kasa da ilimi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani yunkuri na bunkasa samar da wutar lantarki da kuma bunkasar tattalin arziki, gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon kashi na farko na taransfoma 500 ga al’ummomin karkara a fadin kananan hukumomin jihar 44. Gwamna Abba Yusuf ne ya kaddamar da shi a hukumance a Kano a wani shirin da nufin magance kalubalen rashin samar da wutar lantarki. Gwamna Yusuf ya ce samar da taransfoma wani shiri ne na bunkasa masana’antu da zaburar da harkokin kasuwanci musamman a yankunan karkara. “Wannan rabon shi ne kashi na farko na aikin samar da wutar lantarki a yankunan karkara, ba wai kawai wani aikin samar da wutar lantarki ba ne, wani muhimmin mataki ne na inganta samar da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran wanda yake halattan taron kungiyar raya tattalin arziki ta Bricks ya yabawa kungiyar kan yin tir da Amurka da kuma HKI kan keta hurumin kasar da yaki na kwanaki 12 da kuma da kuma kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar ta zaman lafiya wadanda suke Fordo Natanz ta kuma Esfahan. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalti ministan yana fadar haka a taron kungiyar karo 17 wanda ke gudana a hilin yanzu a birnin Rio De jenero na kasar Brazil. A ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata ne jiragen yaki na HKI suka kutsa cikin Iran inda suka kashe manya-manyan kwamandocin sojojin kasar da kuma masana fasahar Nukliyar kasar ga shahada. Bayan haka...
Shugaban Kungiyar Harka Islamia a tarayyar Najeriya Sheikh Irahim Zakzaky ya taya mutanen kasar murna saboda nasarar da suka samu kan HKI da kuma Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan da ya gabata. Ya ce wannan nasarar bata takaita da mutanen kasar Iran kadai ba , hada har da al-ummar Musulmi da kuma da kuma masu sun yenci a ko ina suke. Ya kuma yaba da yadda gikuwan nmalamai na kasar Iran suka sami nasarar kare kasar daga mafi yawan hare-haren HKI a kan kasar. Ya bayyana cewa Iran ta sami nasara a kan kasashen yamma da makamai wadanda suka fi nasu karfi da inganci, har’ila yau sun sami nasara a kan ma;aikatan yahudawan da suke taimaka masu...
Miliyoyin yan Najeriya ne suka gudanar da tattakin Ashoora a birne daban daban a kasar a jiya Lahadi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, da farko ya nakalto daruwan da suka fito tattakin na Ashoora a Abuja babban birnin kasar a safiyar jiya Lahadi. A wannan karon dai masu tattakin Ashoora a Abuja sun fito ba tare da sanya bakaken kaya ba saboda kaucewa rikici da kuma kamu daga Jami’an tsaro a birnin, kamar yadda suka sabayi a shekarun da suka gabata. Labarin ya kara da cewa an gudanar da irin wannan tattakin na Ashoora a garurwa kimai 25 a duk fadin kasar, kuma an kammala ba tare da wata matsala ba. An gudanar da tattaki a jihar Bauchi...
Kamfanin dillancin Labaran Assosciated Press ta bayyana cewa ana ci gaba da sukar Amurka da HKI kan cibiyoyin kisa da suka kafa a Gaza da sunan tallafawa Falasdinawa da abinci. Labarin ya bayyana cewa ya zuwa yanzu Amurka da HKI sun kashe Falasdinawa kimani 635 wajen karban abinda suka kira taimakon abinci bayan sun sa su yunwa mai tsanani wanda zai sa su dole su fito su ne mi aminda zasu a sa a cikinsu. Amma idan sun so sojojin HKI su kashesu. Kamfanin dillancin labaran Associeated Press ya nakalto kamfanoni Amurka guda biyu wadanda sun ce sun shigar da kara Amurka da kuma HKI kan yadda suke gudanar da cibiyoyin rabon abinda suka kira abinci a gaza, wanda bai...
Kasar China ta maida martani ga takunkuman tattalin arziki na wasu kayakin kiwon lafiya wadanda tarayyar Turai da dorta maya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar kasar ta Chaina na fadar haka ta kuma kara da cewa gwargwadon takunkuman da suka dorawa kasar gwargwadon maida martanin kasar ta China. Labarin ya kara da cewa wannan haramcin ba zai shafi kamfanonin turai da suke samar da kayakin aikin kiwo lafiya a cikin kasar China ba. A cikin watan Yunin da ya gabata ne kungiyarn EU ta hana gwamnatocin kasashe kungiyar sayan kayakin aikin likita fiye da dalar Amurka miliyon 5 tare da bukatar kasar china ta daina nuna bambanci a cikin ahrkokin kasuwanci da ke tsakaninsu.
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ƙalubalanci jagoran ’yan bindiga Bello Turji, wanda ke neman sulhu, da cewa idan da gaske yake yi, to ya sako duk mutanen da ya yi garkuwa da su, ya daina kai hare-hare, kafin ta zauna da shi. Mashawarci na musamman ga gwamnan Sakkwato a kan sha’anin tsaro, Kanar Ahmed Usman ne ya bayyana hakan baya yaɗuwar wani bidiyo da Turji ya saki, wanda a ciki yake neman a yi tsakaninsa da gwamnati. Ɗan ta’addan wanda ya addabi yankunan jihar da makwabta ya saki bidiyon ne kwanaki kaɗan bayan jami’an tsaro sun kashe wasu gaggan kwamandojinsa da Faransa sama da 100. Kamar Ahmed, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa babu yadda za a tabbatar cewa neman...
Tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Nijeriya ta fara gasar ƙwallon ƙafa ta mata ta ƙasashen Afirika da kafar dama, bayan lallasa ƙasar Tunisia da ci 3-0 a wasan farko da suka buga yau Lahadi a filin wasa na Prince Moulay Abdellah. Asisat Oshoala da Rinsola Babajide da Chinwendy Ihezuo ne suka jefa kwallayen da suka yi sanadiyar samun nasarar ‘yan matan, yanzu Nijeriya ta dare teburin rukunin ‘B’ wanda ke ɗauke da ƙasashen Algeria da Botswana da Tunisia da Nijeriya. Ƙwallon Mata: Rivers United Ta Doke Nasarawa Amazons A Wasan Ƙarshe Na Kofin Shugaban Ƙasa Wace Nahiya Ce Ta Fi Iya Ƙwallon Ƙafa Tsakanin Turai Da Kudancin Amurka? ‘Yan matan da Madugu ke jagoranta za su haɗu da ƙasar Botswana...

Mataimakin Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Sabbin Fasahohin Kimiyya A Fannin Aikin Gona Da Kiwon Lafiya
Mataimakin firaministan kasar Sin Liu Guozhong, ya yi kira da a gaggauta samar da sabbin fasahohin kimiyya a fannonin aikin gona da kiwon lafiya, da karfafa cin gashin kan fasahar kirkire-kirkiren magunguna da na’urorin likitanci. Liu, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne yayin ziyarar bincike da ya kai lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin daga ranar Alhamis zuwa Asabar da ta gabata. Ya jaddada cewa, ya zama wajibi a mai da hankali kan bukatu na gaggawa da ake da su a bangaren masana’antar da kuma ba da karfi ga muhimman fannoni kamar masana’antar fasahar samar da iri, da injunan noma, da kayan abinci, da fasahar shuka da kiwo. Liu...
“Na yi Allah- wadai da amfani da madafun iko da tsara sakamakon zabe kafin zabe ta hanyar amfani da karfin mulki da hukumomin gwamnati.” “Wajibi ne Hukumar Zabe ta samu hanyoyin magance wadannan matsalolin a wajen jefa kuri’a maimakon neman hakki a bangaren shari’a wanda daga karshe kotu za ta sanya wasu dubaru ta kori kara mai kyau ta fashin zabe.” Ya bayyana. Ya ce irin wannan matsalar na samar da mutanen da ba su ko iya cin zabe a cikin dangin su ko al’ummar su amma sune ke tinkahon lashe zabe. A cewarsa a matsayinsa na dan majalisar dattawa suna kokarin gabatar da dokokin da za su shawo kan wadannan matsalolin, ya ce sun san hukumar zabe ba za...
A cikin ‘yan kwanakin nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mayar da jawabi ga malamai da daliban tawagar musayar al’adu ta matasan Amurka masu buga wasan kwallon pickle daga gundumar Montgomery ta jihar Maryland, wadanda suka ziyarci kasar Sin a karkashin shirin gayyatar matasan Amurkawa 50,000 zuwa kasar Sin domin yin musaya da kuma nazarin karatu a cikin shekaru biyar. Xi ya ce, makomar alakar Sin da Amurka ta dogara ce da matasa, yana mai bayyana fatan wakilan tawagar za su zama sabbin jakadu na sada zumunci a tsakanin kasashen biyu, da ba da gudummawa sosai wajen yaukaka zumuncin da ke tsakanin jama’ar kasashen biyu. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
Kungiyoyi farar da jam’iyyun adawar siyasa a kasar Togo, sun sake yin kira da a gudanar da Zanga-zanga a ranar 16 da 17 ga watan nan na Yuli da ake ciki. Masu Zanga-zangar dai suna son nuna kin amincewa ne da siyasar hukumar kasar da suke bayyanawa da ta kama-karya, haka nan kuma kashe wasu mutane da aka yi a Zanga-zangar da ta gabata. Bugu da kari, kiran a yi zanga-zangar dai ya zo ne bayan kama wasu ‘yan hamayyar siyasa da aka yi da kuam kara kudin wutar lantarki, da amince da sabon tsarin mulki da ya kara bai wa shugaban kasar Faure Gnassingbe karfin iko. Wasu fitattun masu fafutuka a kasar, sun watsa sanarwa a shafukan sada zumunta...
Raundunar sojan jamhuriyar Nijar sun sanar da cewa, an kashe sojoji 10 da kuma jikkata wasu 15 a wasu hare-hare biyu da masu dauke da makamai su ka kai a yankin Telaberi da kudu masu yammacin kasar. Yankin Telaberi dai yana cikin yankunan da masu dauke da makamai su ka fara kai hare-hare saboda kusancinta da iyakokin kasashen Mali da Burkina Faso. Bayanin na sojojin kasar ta Jamhuriyar Nijar wanda kafafen watsa labarun kasar su ka watsa ya kunshi cewa; Daruruwan masu dauke da bindiga sun kai hare-hare a kan sansanonin soja biyu da suke a yankin Telaberi da hakan ya yi sanadiyyar kashe sojoji 10 da kuma jikkatar wasu 15.” Sai dai kuma sanarwar ta ce, sojojin sun yi...
Dubun dubatar mutanen kasar Lebanon sun yi gangamin raya ranar Ashura ta shahadar Imam Hussain ( a.s) a unguwar Dhahiya wacce aka sauya wa suna suna unguwar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Mahalarta taron sun daga hotunan Sayyid Hasrallah wanda a shekarar da ta wuce yana raye, ya kuma gabatar da jawabi a wurin jimamin Ashura. Haka nan kuma sun rika bayar da taken da yake cewa: ” Muna Akan Riko Da Alkawali Ya Nasrallah.” A yau 10 ga watan Muharram ne dai al’ummar musulmi Mabiya mazhabar Ahlul bayti suke tunawa da shahadar Imam Hussain ( a.s) da iyalansa da kuma sahabbansa madaukaka.
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’ima Kassim ya bayyana cewa; Dakarun Hizbullah mazajen fagen daga ne da ba su karbar kankanci. Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a wurin babban taron Ashura a ungiyar Dhahiya dake birnin Beirut, ya bayyana cew; Yaki na tsaron kasa zai ci gaba saboda mun yi Imani da ‘yanto da kasa, kuma wajibi ne akansu, ko da kuwa an dauki lokaci mai tsawo sannan kuma sadaukar da kai ya yawaita.” Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Isra’ila abokiyar gaba tana ci gaba da mamaye yankuna 5 na Lebanon, don haka babu yadda za a yi mu mika kai.” Haka nan kuma ya yi tambayar cewa; Ta yaya za a tsammaci za mu ki...
A kasar Iraki,miliyoyin mutane sun cika birnin Karbala domin yin juyayin shahadar Ahlul Bayti ( a.s) da iyalansa tsarkaka, a tsakanin hubbaren Imam Hussain da dan’uwansa Abul Fadal Abbas ( a.s). Masoya Ahlul Bayti ( a s.) da su ka fito daga cikin kasar ta Iraki da kuma wasu kasashe, sun yi cincirindo a cikin birnin na Karbala a tsakanin hubbaren Imam Hussain da Abul Fadal Abbas ( a.s). Cibiyar da take kula da wuraren masu tsarki a Karbala ta yi tsari na kula a tafiyar da juyayin a cikin tsaro da kuma gabatar da hidima ga masu Ziyara. An girke jami’an tsaro masu tsaro yawa a cikin birnin na Karbala da zagayen haramin Imam Hussain ( a.s) , haka...
Sanatan ya bayyana cewa gwamnonin yankin na farko sun ba da gagarumar gudunmuwa wajen jagorantar hadin kai wajen cimma muradun yankin daga kan ikon sarrafa albarkatun kasa zuwa matsalolin muhalli da sauransu. A kan wannan ya yi kira ga gwamnoni.masu ci a yanzu da su ci gaba da wannan al’adar, kuma su kara kokari kan ciyar da yankin a gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Masanin Kenya kan huldar kasa da kasa mai suna Cavince Adhere, ya bayyana a yayin zantawarsa da dan jarida na kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan cewa, a matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa ya jaddada daidaito da samun albarkatu, inda hakan ya samu aminci daga kasashe masu tasowa. Kuma har ila yau, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashe masu tasowa ya riga ya samu gagarumin ci gaba, don haka makomar kasashe masu tasowa na bukatar ci gaba da kasancewar Sin a cikinsu. Bugu da kari, Cavince Adhere ya jaddada cewa, Sin ta bayyana bukatun kasashe masu tasowa na duniya yadda ya kamata, kana tana inganta ra’ayoyin da...
Zalum ya kuma shawarci gidajen jaridu da su dinga tantance labarai kafin su yaɗa shi domin kaucewa labaran ƙanzon kuregen da wasu suke yaɗawa. A ƙarshe gwamnan ya ce ya duƙufa wajen hidimtawa al’ummar jihar Borno a ƙarƙashin jam’iyar mai albarka ta APC . Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Labarin da dan jarida ya samu daga ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin a yau Lahadi ya nuna cewa, a kwanan baya kasashen Sin da Myanmar da Thailand sun gudanar da taron ministoci karo na biyu don yaki da laifukan zambar da ake aikatawa ta hanyar sadarwar waya. A gun taron, sassan da abin ya shafa na kasashen uku sun cimma matsaya kan zurfafa hadin gwiwar tabbatar da doka da oda, kuma za su ci gaba da yin hadin gwiwa wajen dakile laifukan zamba ta hanyar sadarwar waya a Myawaddy da sauran wurare, da kawar da harkokin zamba ta hanyar sadarwar waya gaba daya, da kame dukkan ma’aikatan da ke da alaka da laifin zamba, kana za su yi tsayin...
Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci dakarun sojin Najeriya da su murƙushe ’yan ta’adda, masu tada ƙayar baya, da ’yan awaren Biyafara da ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. Yayin bikin Ranar Sojoji ta 2025 da ya gudana a Jihar Kaduna, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci Shugaba Tinubu. Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC Tinubu ya ce: “Lokacin tashi ya yi. Ina tare da ku ɗari bisa ɗari don murƙushe masu yunƙurin rusa Najeriya. Ku ne ƙarfina, goyon bayana da addu’o’ina.” Ya gargaɗi cewa barazanar da ake fuskanta ba ƙananan abubuwa ba ne. “Waɗannan miyagun ba sa bambanta tsakanin coci da masallaci. Suna...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), reshen jihar ce ta tabbatar aukuwar hatsarin. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle. Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC Gwamna ya gargaɗi sarakuna kan mamaye filayen kiwo a Gombe Hatsarin ya rutsa da wata babbar mota ƙirar DAF mai lambar GWL 422 ZE da kuma motar ɗaukar fasinjoji ƙirar Toyota Hummer mai lambar KMC 171 YM. FRSC, ta ce bincike ya nuna cewa direban motar fasinjojin ne ya karya doka ta hanyar bin hanyar da ba ta dace ba, wanda...
Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano, kamar yadda Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar. Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle. Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC Gwamna ya gargaɗi sarakuna kan mamaye filayen kiwo a Gombe Hatsarin ya rutsa da wata babbar mota ƙirar DAF mai lambar GWL 422 ZE da kuma motar ɗaukar fasinjoji ƙirar Toyota Hummer mai lambar KMC 171 YM. FRSC, ta ce bincike ya nuna cewa direban motar fasinjojin ne ya karya doka ta hanyar bin hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan ya sa...
Za ka so karin bayani kan sabbin ‘yan wasan da Arsenal ke shirin dauka? ⚽ Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa zai bar jam’iyyar APC zuwa ADC tare da wasu gwamnoni biyar. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya, ya fitar, Zulum ya ce wannan labari ƙarya ne, kuma wasu ne kawai ke ƙirƙirarsa domin cimma wata manufa ta ƙashin kansu. Gwamna ya gargaɗi sarakuna kan mamaye filayen kiwo a Gombe Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Ya ce yana nan daram a jam’iyyar APC kuma yana biyayya ga jam’iyyar a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya. Sanarwar ta ce, “Mun ji wani labari da ake yaɗawa cewa zan koma jam’iyyar ADC tare da wasu gwamnoni biyar. “Wannan...
Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gargaɗi sarakunan gargajiya a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar kan zargin hannu a mamaye hanyoyin kiwo da filayen kiwo, abin da ke haddasa rikici tsakanin makiyaya da manoma. Gwamnan ya nuna damuwa kan rahotannin da ke cewa wasu sarakuna na karɓar cin hanci suna kuma ba da damar shiga filayen kiwo ba bisa ƙa’ida ba, lamarin da ke ƙara tayar da zaune tsaye a tsakanin al’umma. Majalisar Dattawa ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka “Duk wanda aka kama yana da hannu a wannan aika-aikar, za mu hukunta shi bisa doka,” in ji Gwamna. Ya kuma roƙi makiyaya da su guji shiga gonaki domin...
Majalisar Dattawan Nijeriya ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Akpoti Uduaghan gabanin cikar wa’adin dakatar da ita da ta yi tsawon watanni shida. Majalisar ta ce ala tilas ne dakatacciyar Sanatar ta bayar da hakuri tare da neman afuwa a hukumance gabanin cika umarnin da ta wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar na dawo da ita. Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka An kama ɗan Najeriya yana taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine Shugaban Kwamitin Labarai da Harkokin Jamaa na Majalisar Dattawa, Sanata Adeyemi Adaramodu ne ya bayyana hakan yayin da yake martani kan hukuncin da kotun ta yanke a kan Sanata Natasha. Ya yi bayanin cewa, a yayin yanke hukuncin da ta bayar da...

Taron Ashura Ya Zama Lamari Mafi Girma Da Cinkoson Jama’a, Inda Masu Ziyara Daga Sassan Duniya Suka Isa Karbala
Gangamin Ashura ya zama lamarin mafi girma da cunkoson jama’a inda tattakiin Tuwairij yake gudana tare da faɗaɗa da ba a taɓa ganin irinsa ba Tattakin Tuwairij na bana zuwa birnin Karbala na fuskantar hallara da cunkoson jama’a da ba a taba ganin irinsa ba, inda dimbin masu ziyara daga sassan duniya ke tururuwa zuwa hubbaren Imam Husaini da kuma titunan da ke kewaye. Mai ba da shawara ga babban sakataren cibiyar Hubbaren Imam Husain {a.s} Fadel Oz a cikin wata sanarwa da ya aikewa kafafen watsa labarai ya bayyana cewa: “A shirye-shiryen wannan juyayi, babban Sakatariyar Haramin Imam Husain (a.s) da haramin Abbas sun samar da dukkan sharuddan da suka dace don kula da masu ziyara da kuma tabbatar...
An sake gudanar da wani sabuwar zanga-zanga a manyan biranen duniya domin neman kawo karshen kisan kiyashin da ake yi a Gaza A jiya asabar ne aka sake gudanar da wata sabuwar zanga-zanga a kasashe da dama na duniya domin nuna adawa da hare-haren da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ke ci gaba da kai wa kan zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da 192,000 tare da jikkata yawancinsu mata da kananan yara. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, mutane da dama ne suka gudanar da zanga-zanga a gaban ma’aikatar harkokin wajen kasar a Quito babban birnin kasar, domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a zirin Gaza. Masu zanga-zangar sun yi kira da a kawo karshen yaki da kisan...
Mataimakin shugaban kasar Iran na Farko ya ce; Al’ummar Imam Husaini a Iran ba za su bari makiya su cimma mummunan burinsu ba Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran na farko Muhammad Reza Aref ya rubuta a cikin wata wasika cewa: Domin kare martabar Iran da kasar al’ummar Imam Husaini a Iran da zuciya daya da murya daya da hadin kan al’umma ba za su taba barin mafarkin masu kyama ya tabbata ba. Aref ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na Instagram a jajibirin ranar Ashura inda ya rubuta cewa: “Saboda Iran da kasar da tushen al’ummar Mabiya Imam Husaini a Iran da zuciya daya da murya daya da hadin kan al’umma ba za su taba bari mafarkin makiya...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tafi kasar Brazil don halartar taron BRICS karo na 17 Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya sanar da isar ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin Rio de Janeiro domin halartar taron kasashe mambobi a kungiyar BRICS karo na 17. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Tawagar kasar Iran karkashin jagorancin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi za ta halarci taron kasashen BRICS. Baqa’i ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa: “Sun isa birnin Rio de Janeiro na Brazil, domin halartar taron kasashen BRICS karo na 17.”
Babban Mufti na masarautar Oman ya yi kakkausar suka kan kasashen da ke neman kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya bayyana mamakinsa kan yadda wasu kasashe ke son kulla alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, wata kasa ‘yar mamaya maras tushe. A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X, Ahmed bin Hamad Al-Khalili ya ce: “Abin mamaki ne yadda wasu kasashe ke son kyautata alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, alhali su kansu suna kallon wannan mahalukiya a matsayin wata kasa mai gushewa ko ba dade ko ba jima, al’ummarta dai suna son ci gaba da yakin ne kawai don ci gaba da wanzuwarta, in ba haka ba,...
Aƙalla mutane takwas ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Atura Bus Stop, hanyar Lagos-Badagry, lokacin da wata motar haya ƙirar Mazda mai ɗaukar fasinjoji 16 ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota ƙirar DAF. Hukumar LASTMA ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da rashin iya sarrafa mota daga direban motar hayar. A cikin wata sanarwa, Daraktan Hulɗa da Jama’a na LASTMA, Adebayo Taofiq, ya ce hatsarin ya kasance mai muni matuƙa, inda ya kashe direban motar, yaran moto da sauran fasinjoji shida. Ya ce hatsarin ya jefa al’ummar yankin cikin alhini da ɗimuwa. Jami’an LASTMA, da FRSC, da rundunar ƴansanda da Sojoji daga Ibereko sun gudanar da aikin ceto...
A ranar Asabar, ƙungiyar PSG ta doke Bayer Munich da ci 2-0 a wasan zagayen kusa da na ƙarshe na gasar Kofin Duniya na Kungiyoyi, wanda aka buga a filin wasa na Mercedes Benz, Atlanta, Amurka. Duk da samun katin kora guda biyu, PSG ta nuna kwarewa da jajircewa wajen zura ƙwallaye masu kyau a raga. A wani wasa da aka buga a daren ranar Asabar a filin wasa na MetLife Stadium, New Jersey, Real Madrid ta doke Borussia Dortmund da ci 3-2. Madrid ta fara da ƙwallaye biyu daga Gonzalo Garcia da Fran Garcia, kafin Dortmund ta yi ƙoƙarin dawo da wasan. Kylian Mbappé ya ƙara wa Madrid ƙwallo ta uku da kyakkyawan bugun watsiya, sai dai Dortmund ta...
Hukumomi a Jihar Texas ta Amurka sun ce gomman mutane sun riga mu gidan gaskiya ciki har da kananan yara sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa a ranar Asabar. Sai dai ya zuwa yau Lahadi, adadin wadanda suka mutu sun kai 50 ciki har da kananan yara 15 yayin da ake ci gaba da aikin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su kamar yadda wani babban jami’in dan sanda na yankin, Larry Leitha ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP. An kama ɗan Najeriya yana taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 41 a Nijar Tuni dai Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa wajen kai dauki yankin na...
Lamarin da ya haddasa daya daga cikin bala’i da mutane suka taba fadawa, inda sama da mutum miliyan 12 suka tsere daga gidajensu. Darfur ta kasance yankin da nan da nan rikici kan tashi, inda RSF ke iko da yawancin yankin, in banda birnin el-Fasher wanda ya ci gaba da kasancewa a hannun rundunar sojin kasar da kawayenta. Birnin el-Fasher ya sha ruwan bama-bamai a yayin da RSF ke kokarin kama shi. A watan Afirilu RSF din ta sanar da shirin kafa gwamnati domin zama kishiya ga gwamnatin soji, abin da ya haddasa fargaba cewa hakan zai kai ga rarraba kasar. Alawia ta ce yayin da fadan ya tsananta ake ta ruwan bama-bamai a watan da ya gabata, dole ita...
Sojojin Ukraine sun kama wani ɗan Nijeriya da ke taimaka wa Rasha a yaƙin da suke gwabzawa sama da shekaru biyu biyo bayan mamayar ƙasarsu. Wani bangaren sojin da ke ƙunshe da mayaƙan Rasha da ke goyon bayan Ukraine a wannan yakin, wanda ake kira ‘Freedom Of Russia Legion ne ya kama Kehinde Oluwagbemileke mai shekaru 29 a yankin Zaporizhzhia bayan shafe watanni biyar yana yaƙi a cikin mayaƙan Rasha. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 41 a Nijar Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP Oluwagbemileke ya shafe shekaru huɗu yana zaune a ƙasar Rasha kafin a kama shi akan laifin da ke da nasaba da miyagun ƙwayoyi. An ruwaito cewa matashin ya amince ya shiga...
Rashford dai ya fi son komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona domin yana ganin zai iya buga abin a zo a gani a kakar wasa mai zuwa sai dai ita kuma Barcelona ta fi son dan wasa Nico Williams na kungiyar Athletico Bilbao ta kasar Spaniya, wanda shima yake son komawa Bardelona da buga wasa idan har Barcelonan za ta iya biyan kudin da aka yi masa farashi. Kungiya ta kwana-kwanan nan da ta nemi Rashford ita ce kungiyar Bayern Munchen ta Jamus, bayan da Liberpool ta ce ba za ta sayar mata da Luiz Diaz ba, ana ganin yanzu kungiyar za ta karkata akalarta zuwa neman Rashford. Kungiyoyi irinsu Newcastle United da Tottenham da kungiyoyi daga Saudiyya duka sun...
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya halarci zaman makokin da aka gudanar a hussainiyar Imam Khomaini (q) da cikin gidansa a nan birnin Tehran a daren Ashoorah a jiya Asabar da yamma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hujjatul Islam Masaoud Ali wanda ya karanta makokin yana fadar cewa, kasar Iran zata dauki darasi daga Imam Hussain (a) na rashin mika kai da azzalumai. Ya kuma bayyana yunkurin da Iraniyawa suke yi a halin yansu yana daga cikin gwagwarmayan duniya don fuskantar azzaluman duniya karkashin jagorancin HKI da Amurka. Ya kuma kara da cewa musulunci ne yake gaba da gaba da kafircin duniya a cikin yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiya ya bayyana cewa dukkan kasashe mambobia a kungiyar ECO ta raya tattalin arziki na kasashen yankin sun yi tir da HKI a taron kungiyar wanda aka gudanar a birnin Khankendi. Na kasar Azerbaijan. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka bayan tawowarsa daga taron a daren jumma’a a kuma shafinsa na X. Shugaban ya kuma kara da cewa Tehran a shirye take ta hada kai da wadannan kasashe makobta don taimakawwa juna a dukkan bangarorin rayuwa wadanda suka hada da kyautata tattalin arzikin yankin da al-adu da sauransu. Shugaban ya bayyana cewa yana godiya ga dukkan kasashen kungiyar ECO da kuma sauran kasashen yankin da sauran kasashen duniya wadanda...

Iran ta Bukaci Gudanar da Bincike Kan Sacewar jami’ar Diblomasiyyar kasar A Lebanon Shekaru 43 Da Suka gabata
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da ci gaba da riki jami’an diblomasiyyar kasar 4 wanda HKI take yi tun shekaru 43 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar tana fadar haka a wata sanarwa da ta fitar shekaru 43 cur da sacewar wadanda Jami’an diblomasiyyar kasar a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a ranar 4 ga watan Yuli n shekara 1982. Jami’an diblomasiyyar suna ne Seyed Mohsen Mousavi, Ahmad Motevaselian, Kazem Akhavan, and Taghi Rastegar Moghadam, wadanda wata kungiyar yar ta’adda wacce HKI take goyon bayanta ta kamasu ta kuma mikawa HKI a lokacinda take mamayae da kasar Lebanon. Rahoton ya yabawa gwamnatin kasar Lebanon kan hadin...
Majiyar kafafen yada labarai na Amurka sun bayyana cewa akalla mutane 52 suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwan sama a jihar Texas. Jaridar US Today ta bayyana cewa an kubutar da daruruwan mutane daga halaka, amma kuma har yanzun ba san makamon daruruwan mutane ba. Sannan kungiyoyin bada agaji suna ci gaba da neman masu sauran shanruwa. Ruwan sama kamar da bakin kwarya ne ya sauka a jiya Asabar ya kuma ciika kogin Guadalupe wanda yayi ambaliya ya kuma rufe garuruwa da dama da suke bakin kogin. Gwamnatin Jihar Tezas Dan Patrick ya bayyana cewa an kubutar da mutane kimani 850 amma yawan matattu kuma yana karuwa a lokacinda jami’an agaji suke ci gaba da neman gawaki da kuma masu...
Kamfanin jiragen sama na UAE airlines ko emirate ya sake farfado da zirga zirga zuwa kasar Iran bayan da aka rufe sararin samaniyar kasar Iran a ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata. Jaridar National ta kasar Amurka ta bayyana cewa kasashe da dama a duniya sun dakatar da zirga zirga zuwa JMI saboda yakin da HKI da Amurka suka kai mata daga 13 ga watan zuyi har zuwa kwanaki 12. Labarin ya kara da cewa kasashen Iraki da Jordan sun dakatar da zuwa kasar Iran saboda yaki kuma saboda gwamnatin Iran ta hana jiragen sama tashi ko kuma zuwa kasar. A ranar Alhamis ne JMI ta gabata ne hukumomin Iran suka bude sararin samaniyar kasar wanda ya nuna...
Dakarun sojin Nijar sun samu nasarar kashe ’yan ta’adda 41 a yayin wasu tagwayen hare-hare da aka kai musu ranar Juma’a a yammacin ƙasar. A cikin wata sanarwa, Ministan Tsaron Nijar, Janar Salifou Modi ya ce hare-haren ta’addancin da ɗaruruwan ’yan ta’adda suka kai a lokaci guda, sun auku ne a yankunan Bouloundjounga da Samira a Ƙaramar Hukumar Gotheye. Sanarwar da aka karanto a tashar talabijin ta ƙasar ta ƙara da cewa an yi asarar dakarun ƙasar 10, kana wasu 15 suka ji rauni a sakamakon wannan hari. Yankin Gotheye yana kusa da iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso kuma yanki ne da ya daɗe yana fuskantar hare-hare daga ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi. Ƙauyen Samira na da kamfanin hakar...
Rukunin farko: Morocco da Zambiya da Senegal da kuma Jamhuriyar Congo Rukuni na biyu: Nijeriya da Tunisia da Algeria da kuma Botswana. Rukuni na uku: Afirka ta Kudu da Ghana da Mali da kuma Tanzania. Bayan karawar bude labulen gasar, akalla za a rika buga wasanni bibiyu kowacce rana a fafatawar cikin rukuni har zuwa ranar Litinin 14 ga watan Yuli. Sannan a lokacin wasannin cikin rukuni za ake buga su daga 13:00 da 16:00 da kuma19:00 daidai da agogon GMT. Za a fara karawar zagaye na biyu daga ranar Juma’a 18 ga watan Yuli. Shekara ukun da ta gabata, Morocco ta gudanar da gasar cin kofin Afirka ta mata, kuma filaye ukun da ta yi amfani da su,...
Taken cimma “Zaman lafiya ta amfani da karfi”, na dogaro ne ga siyasar nuna karfin tuwo, don haka Wang ya aza tambayar cewa, idan har karfi ne ke iya tabbatar da daidai da kuma kuskure, ta yaya za a iya tabbatar da dokoki da adalci? Kana ta yaya kasashe marasa karfi, musamman kanana da matsakaita za su iya rayuwa? (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal
A baya bayan nan, firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko, ya zanta da kafar CMG ta kasar Sin, inda ya jinjinawa shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, wadda ya bayyana a matsayin mai cike da hangen nesa da burikan samar da ci gaba, wanda hakan ya yi daidai da hikima, da managarcin tunanin jagoranci na shugaba Xi Jinping na kasar Sin. Mista Sonko, ya ce Senegal ce kasar farko a yammacin Afirka da ta karbi wannan shawara. Kuma abu ne mai muhimmanci ganin yadda shawarar ke kara ingiza cimma nasarori ga dukkanin sassan. Sonko ya kara da cewa, cikin ‘yan shekaru kalilan, tarin kasashen Afirka sun cimma manyan nasarori na hakika, daga aiwatar da shawarar. Ya ce shawarar ba wai ta...
Ibrahim ya bayyana cewa, sun rarraba mukamai na rikon jam’iyyar a tsakaninsu, kafin babban taro na kasa a nan gaba. Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya tabbatar cewa; hadakar ta ADC, ta zabi Aregbesola a matsayin sakatarenta na kasa na riko, har ma ya wallafa a jawabin karbar mukamin da ya yi a shafukan sada zumunta. Matakin ‘yan adawar na shiga ADC, na zuwa ne bayan kasa cimma bukatarsu ta yi wa sabuwar kungiyar mai suna ‘All Democratic Alliance’ (ADA), rajista a matsayin jam’iyyar siyasa, sakamakon jan kafa da suka rika samu daga babbar hukmar zabe ta kasa (INEC). Haka zalika, Atiku Abubakar da wasu manyan jam’iyar PDP, sun nemi ‘yan jam’iyyar da su hada hannu da su wajen shiga...

Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70
Zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa a birnin Geneva Che Xu, ya yi jawabi a gun taron tattaunawa na shekara-shekara, kan gudummawar fasahohi karo na 59, na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD a jiya Juma’a, a madadin walikan kasashe fiye da 70, game da raya hidimomi ga nakasassu ta hanyar fasahar AI, inda ya yi kira ga raya fasahar AI don inganta fasahohi, da karfin hidimomin da ake samarwa nakasassu, da kuma sa kaimi ga sassan kasa da kasa, ta yadda za su iya more fasahohin bunkasa fasahar AI. A cikin jawabin nasa, ya gabatar da shawarwari uku. Na farko ya ce kamata ya yi a mai da hankali ga bukatun dan...
Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya tunasar da karamar hukumar Roni game da bukatar gina wani rukuni mai dauke da ajujuwa guda biyu ga makarantun ‘ya’yan Fulani makiyaya domin inganta rayuwar su. Shugaban kwamatin, Alhaji Aminu Zakari, ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki biyu da kwamatin ya yi a karamar hukumar Roni. Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jihar Jigawa, ya ce tanadin gina ajujuwan ga makarantun ‘ya’yan Fulani makiyaya na kunshe cikin kasafin kudin kananan hukumomi. Ya kuma bayyana gamsuwa da bin kyakkyawan tsarin sadarwa tsakanin bangaren zartaswa da na kamsiloli ta yadda bangaren kamsiloli ya nemi bayani kan jerin ayyukan raya kasa da karamar hukumar ta...
Ya kuma yi watsi da koke-koken da suke yi na rashin adalci a tsarin mulki, inda ya bayyana hskan hakan da “labaran tatsuniya na siyasa” da ake amfani da su don yaudarar jama’a. A cewarsa, gwamnatin Shugaba Tinubu tana da ƙarfi, tsari da kuma goyon bayan jama’a. “Duk wanda ke shirin tunkarar 2027, zai fi dacewa ya tara a 2031,” in ji Dare. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jita-jita ta fara ƙarfi cewar Sanata Ibrahim Lamiɗo da ke wakiltar Sakkwato ta Gabas a Majalisar Dattawa, na shirin ficewa jam’iyyar APC zuwa ADC. Wannan jita-jita ta fara ƙarfi ne bayan da wasu ‘yan siyasa suka haɗu don kafa sabuwar jam’iyya mai suna ADC da nufin kayar da APC a zaɓen 2027. Gonakin Koko: Mata sun yi barazanar zanga-zanga tsirara a Kuros Riba Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP A cewar wasu, Sanata Lamiɗo ba ya mu’amala da gwamnatin APC a jihar inda alaƙarsa ta fi ƙarfi da ‘yan adawa. Wannan ne ya sa ake ganin ba zai tsaya takara a APC ba a 2027. Wani ɗan siyasa da ya nemi a sakaya sunansa ya...

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa
Taron farko na tsarin hadin gwiwar kungiyar BRICS, tun bayan shigar Indonesia da sauran abokan huldar kungiyar 10, ya ja hankulan sassan kasa da kasa. Har ma wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta nuna cewa kaso 91.2 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi na ganin hadin gwiwa karkashin tsarin hadakar BRICS, ya zamo wani muhimman karfi na ingiza nasarar samar da duniya mai mabanbantan tasiri, wadda za ta wanzu bisa daidaito da adalci, da kuma tsari mai game dukkanin sassa, da tattalin arziki da dukkanin duniya za ta ci gajiyarsa. Kasashe mambobin BRICS, sun yi aiki tukuru wajen ingiza tsarin cinikayya da kudaden juna, da gina tsarin hada-hadar kudade mai zaman kansa,...
“Ni na san fina-finan da aka haska a gidajen Gala da aka samu fiye da Naira miliyan daya a rana daya, wasu kuma har miliyan biyu, yanzu idan ka duba tun daga Kano har Nijar za ka dinga ganin gidajen Gala, haka zalika daga nan Kano har zuwa birnin Legas ma akwai su, saboda haka; me zai hana mu rika amfani da wannan dama wajen fadada adadin kudaden shiga da wannan masana’anta mai albarka take samu? Daga karshe, ya bukaci hadin kai daga dukkanin wasu masu ruwa da tsaki, wajen ganin wannan haka ya cimma ruwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Rahotanni daga kudanci Lebanon sun ce, sau uku jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare a kan gidajen mutane da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu da dama. A garin Shaqra’dake yankin Bint-jubail, jiragen sama marasa matuki sun kai hare-hare da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane biyu da raunuka, kamar yadda ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar. Har ila yau wani jirgin maras matuki na abokan gaba ya kai wani harin akan wata mota a yankin “Safful-Hawa” da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya. A garin Shab’a kuwa ‘yan sahayoniyar sun kai hari akan wani gida, wanda ya yi sanadiyyar jikkatar mutanen dake cikinsa. Majiyar asibiti a garin Marja’iyyun ta ce an kai...
Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun fitar da bayani a lokacin tunawa da sace jami;an diplomasiyyar Iran 4 a birnin Beirut, wanda ya kunshi cewa: Ya zama wajibi ‘yan sahayoniya su kwana da sanin cewa; Duk laifukan da su ka aikata a baya za a yi musu sakamako a kansa,kuma duk wani sabon wuce gona da iri, zai gaggauta zuwa karshensu ne.” Sanarwar ta kuma ce: Muna tunawa ne da zagayowar cikar shekaru 42 daga wancan aikin ta’addanci, da a yanzu kwanaki kadan ne su ka wuce na kawo karshen yakin da HKI da Amurka su ka kallafa mana na tsawon kwanaki 12. Yaki ne wanda martani mai karfi da jamhuriyar musulunci ta Iran ta mayar yake kara fito...
Wasu ƙungiyoyin mata a ƙauyukan Bendeghe-Ekiem da Abiya da ke Ƙaramar Hukumar Etung, a Jihar Kuros Riba, sun yi barazanar gudanar da zanga-zangar tsirara idan gwamnati ba ta janye ƙudirin sayar da gonakin koko ba. Matan sun ce wannan shawara da gwamnati ta ɗauka ba su aminta da ita ba, domin gonakin koko su ne tushen rayuwarsu, wanda da su suke cin abinci, suke biya wa ’ya’yansu kuɗin makaranta. Kwankwaso ba zai yi mana takara a 2027 ba — NNPP Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a Kano Aminiya ta samu rahoton cewa gwamnati na shirin sayar da hannun jarinta a wasu manyan gonakin koko da ke wannan yanki, wanda hakan ya fusata matan da sauran al’ummar ƙauyukan da...