DRC: Kungiyar M23 Ta Kori Fararen Hula Zuwa Kasar Rwanda
Published: 18th, May 2025 GMT
Rahotanni daga kasar DRC sun ce a ranar Litinin din da ta gabata kungiyar ‘yan tawaye ta M23 ta kori fararen hula 181 daga garin Goma zuwa kasar Rwanda.
Kungiyar ta zargi fararen hular da ta kora da cewa, ba ‘yan kasa ba ne, asalinsu daga kasar Rwanda ne.
Bugu da kari an gabatar da wasu dubban mutane tare da iyalansu da ake daukar cewa masu laifi ne, da aka zuba su a cikin manyan motoci a yankin Karenga dake yankin Kivu ta arewa.
Mafi yawancin iyalan da aka dauka suna a yankin da yake karkashin ikon kungiyar ‘yan tawaye da Democratic Forces For Liberation of Rwanda ( FDLR).
Gwamnatin Rwanda da kuma kungiyar M23 suna zargin kungiyar FDLR da cewa, tana tafka laifuka a yankin da take rike da shi.
Rahotannin sun ambaci cewa, mafi yawancin wadanda aka kora din suna zaune ne a cikin hemomi na ‘yan hijira dake Sake, da ba shi da nisa sosai daga Goma.
Mai Magana da yawun hukumar ‘yan hijira ta MDD, ( UNHCR) Eujin Byun ta bayyana cewa; an mika mutane 360 zuwa kasar Rwanda a ranar Asabar din da ta gabata.
Ita dai kungiyar M23 wacce ta shimfida ikonta a mafi yawancin yankunan da suke gabashin DRC, tana samun cikakken goyon bayan Rwanda wacce ta aike mata da sojojin da sun kai 4000.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Rwanda
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinawa Kimani 40,000 HKI Ta Kora Daga Yankin Yamma Da Kogin Jordan
Dubabban falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan ne gwamnatin HKI ta kora daga gidajensu tun bayan ta fara wani shiri wanda ta kira Katangan karfe a farkon wannan shekarar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kungiyar Doctors without Borders wato MSF a takaice tana fadar haka a jiya Laraba.
Rahoton ya kara da cewa HKI tana son korar dukkan falasdinawa da suke rayuwa a yankin yamma da kogin Jordan ne don samun damar kafa kasar Yahudawa zallah kamar yadda suke fata.
Rahoton ka kara da cewa falasdinawa a garuruwan Tulkaram Jenin da kuma Nurushamne al-amarin ya fi shafa inda yahudawan suka kore falasdinawa akalla dubu 40,000 daga farkon wannan shekara ta 2025 sun kuma rusa gidajen wasu da dama.