A yau Jumma’a, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya yi hadin gwiwa da kawancen gidajen rediyon Turai na EBU wajen gabatar da rahoton Report ITU-R BT.2550, wato fasahar tsara shirye-shiryen bidiyo da rediyo ta hanyar amfani da fasahar sadarwa ta 5G, a shafin intanet na kwancen harkokin sadarwa na duniya wato ITU.

Lamarin da ya nuna cewa, CMG ya taka muhimmiyar rawa a fannin tsara shirye-shirye masu inganci, ya kuma kai matsayi na gaba a fannin fitar da fasahohin tsara shirye-shiryen zamani masu inganci. (Mai Fassara: Maryam Yang)

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: shirye shirye

এছাড়াও পড়ুন:

ETFund Ta Koka Kan Gibin Da Ake Samu A Sashin Lafiyar Najeriya

Biyo bayan wani rahoto da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta fitar na cewa sama da likitoci 16,000 ne suka bar Najeriya a cikin shekaru bakwai da suka gabata domin neman aiki a wasu kasashe, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na cike gurbin da likitocin suka haifar.

 

Da yake zantawa da manema labarai a Katsina, Shugaban Hukumar Kula da Ilimi ta Kasa (TETFund), Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce hukumar ta kaddamar da wani shiri na musamman domin horar da karin likitoci, ma’aikatan jinya, masu harhada magunguna da kwararrun dakin gwaje-gwaje a manyan makarantun kasar nan.

 

Ya ce tuni hukumar ta TETFUND ta zuba sama da Naira biliyan 100 a manyan makarantu goma sha takwas domin kara karfinsu na horar da dalibai a fannin ilimin likitanci, ta hanyar samar da dakunan karatu, dakunan gwaje-gwaje da sauran abubuwan da suka shafi ababen more rayuwa da ilimi.

 

Masari ya ce, wannan matakin shiri ne don ba da damar tsarin kiwon lafiya ya farfado daga ficewar ma’aikatan lafiya tare da kara karfin ma’aikata a fannin.

 

Ya bayyana cewa an zabo manyan makarantu guda uku a kowace shiyyar siyasar kasar nan saboda kowace cibiya ta samu Naira biliyan 4 don gudanar da ayyuka da kuma sayan kayan aikin da ake bukata domin kara karfin daukar dalibai da horar da dalibai a fannin ilimin likitanci.

 

Masari ya bayyana cewa sun dauki matakin ne saboda muradin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ganin an magance karancin ma’aikata a fannin kiwon lafiya da ke yin illa ga ayyukan hidima a fannin.

 

“A shekarun baya-bayan nan, likitoci da ma’aikatan jinya da yawa da masana harhada magunguna da kwararrun likitoci da sauran kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun bar kasar nan don neman aiki mai gwabi a kasashen waje.

 

Isma’il Adamu/Katsina

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gasar Wasannin Mutum Mutumin Inji Ta Duniya Ta 2025 Na Gabatar Da Sabbin Fasahohin Zamani
  • ‘Yan Majalisa Na Amsar Cin Hanci Har Naira Miliyan 3 Kafin Su Gabatar Da Wani Ƙudiri – Kamfani.
  • ‘Yan Majalisa Na Amsar Cin Hancin Har Naira Miliyan 3 Kafin Su Gabatar Da Wani Ƙudiri – Kamfani.
  • ‘Yan Majalisa Na Ba Da Cin Hancin Har Naira Miliyan 3 Kafin Su Iya Gabatar Da Ƙudiri – Kamfani.
  • ’Yansanda Sun Kama Mutum 2 Da Bindigogi Da Alburusai A Filato
  • Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ta Bayyana Rashin Gamsuwa Da Manufar Shugaba Trump Ta Korar Marasa Galihu
  • Larijani a Beirut: Iran A Shirye take ta taimaka ma Lebanon
  • An naɗa sabon Sarkin Alkaleri a Bauchi
  • Majalisar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Bisa Zargin Kara Farashin Takin Gwamnati
  • ETFund Ta Koka Kan Gibin Da Ake Samu A Sashin Lafiyar Najeriya