2025-05-18@21:55:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 14

«kasar Rwanda»:

    Rahotanni daga kasar DRC sun ce  a ranar Litinin din da ta gabata kungiyar ‘yan tawaye ta M23 ta kori fararen hula 181  daga garin Goma zuwa kasar Rwanda. Kungiyar ta zargi fararen hular da ta kora da cewa, ba ‘yan kasa ba ne, asalinsu daga kasar Rwanda ne. Bugu da kari an gabatar da wasu dubban mutane  tare da iyalansu da ake daukar cewa masu laifi ne, da aka zuba su a cikin manyan motoci a yankin Karenga dake yankin Kivu ta arewa. Mafi yawancin iyalan da aka dauka suna a yankin da yake karkashin ikon kungiyar ‘yan tawaye da Democratic Forces For Liberation of Rwanda       ( FDLR). Gwamnatin Rwanda da kuma kungiyar M23 suna zargin kungiyar FDLR da...
    Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun amince su dakatar da faɗa a gabashin ƙasar har sai an kammala tattaunawar sulhu da ke gudana a halin yanzu wanda Qatar ke shiga tsakani. Wannan dai ita ce yarjejeniyar sulhu ta baya-bayan nan tun bayan da ƴan tawayen suka ƙara kai farmaki a gabashin ƙasar inda hukumomi suka ce an kashe mutane 7,000 tun daga watan Janairu. A ranar Larabar da ta gabata ce, ɓangarorin biyu suka ba da sanarwar yin aiki tare don samar da zaman lafiya, bayan shafe sama da mako guda suna tattaunawa, wanda suka ce an gudanar cikin aminci tare da mutunta juna. A watan da ya gabata, shugaban ƙasar...
    Shugaban kasar Burundi ya yi gargadin cewa Rwanda na da shirin kai wa kasarsa hari, bayan da sojojin Burundi suka taimakawa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) a yakin da take yi da ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda. Shugaban kasar ta Burundi Evariste Ndayishimiye ya bayyana cewa, ya samu “sahihan bayanan sirri” da ke nuni da shirin Rwanda na kai wa Burundi hari, ko da yake bai bayar da karin bayani kan shirin da yake yin zargin a kansaba, wanda Rwanda ta musanta. “Mun san cewa yana da shirin kai hari Burundi,” in ji Ndayishimiye a wata hira da wata kafar yada labarai yayin da yake magana kan shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, yana mai jaddada cewa “‘yan...
    A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Rwanda ya fitar, ta zargi kasar ta Belgium da tsoma baki a harkokin cikin gidanta. Bugu da kari, sanarwar ta bai wa jakadan kasar Belgium a Kigali sa’o’i 48 da ya fice ya bar kasar.  Sanarwar ta kunshi cewa: A kodayaushe kasar Belgium tana kaskantar da Rwanda,tun kafin rikicin kasar DRC, da kuma bayansa, alhali kasar ta Belgium tana da dogon tarihi ta keta, musamman akan Rwanda.” Kasar Belgium dai ta dakatar da taimakon da take bai wa Rwanda saboda rawar da Kigali take takawa a rikicin kasar DRC. A wani jawabi da shugaban kasar ta Rwanda ya yi a ranar Lahadi ya bayyana cewa; Kasarsa za ta kare manufofinta da hana...
    Gwamnatin jamhuriyar demokradiyyar congo ta ware kudi da sun kai dalar Amurka miliyan 5 akan duk wanda ya kamo mata shugabannin  kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 da su ka hada Corneelle Nangaa, Sultani Makenga da kuma Betrand Bisimwa. Sai dai duk da kudade masu tsokar da DRC din ta sanya akan shugabannin kungiyar su uku, abin da kamar wuya,saboda ganin yadda wannan kungiyar take ci gaba da kutsawa cikin manyan birane tana shimfida ikonta a cikinsu. A halin yanzu biranen Goma da Bukavu da suke a gabashin wannan kasa sun shiga karkashin ikon mayakan kungiyar ta M 23. Dubban mutane ne dai su ka rasa rayukansu yayin da wasu dubun dubata kuma su ka bar gidajensu zuwa inda za...
    Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a karon farko ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda kan goyon bayan da take bai wa mayakan kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin ya kuma nemi ksar ta Rwanda da ta”gaggauta” janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango. Kudurin na ranar Juma’a “ya kuma yi kakkausar suka ga hare-haren da kuma ci gaban da kungiyar M23 ke ci gaba da yi a arewacin Kivu da Kivu ta Kudu tare da goyon bayan dakarun tsaron kasar ta Rwanda”. A wani labarin kuma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi kira da a tsagaita bude wuta nan take a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Kenya...
    Manyan jami’an MDD dake aiki a nahiyar Afirka sun yi gargadi a yayin taron gaggawa na kwamitin tsaro akan cewa hare-haren da ‘yan tawaye masu samun goyon bayan Rwanda suke kai wa a gabashin DRC, zai iya haddasa yakin da zai  hada kasashe da dama na yankin. ‘Yar sakon musamman ta MDD a DRC, Bintu Keita ta fadi cewa: “Ya zama wajibi ga kwamitin tsaron ya dauki matakan gaggawa domin hana barkewar yakin da zai hada kasashen yankin. Shi kuwa dan sakon musamman na MDD a yankin tekun Victoria Huang Xia cewa ya yi; “Yadda mayakan kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 ta kwace manyan garuruwan da suke a gabashin kasar ta DRC a cikin makwannin bayan nan yana nuni...
    Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango ta yanke shawarar rufe sararin samaniyarta ga “dukkan jiragen sama na farar hula ko na gwamnati masu rijista dake zaune a Rwanda”. A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Kwango, matakin ya “hana shawagi da sauka a cikin kasar ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, saboda dalilai na rashin tsaro da ke da nasaba da rikicin masu dauke da makamai.” A taswirorin zirga-zirgar jiragen sama na duniya, jiragen sama daga Kigali na kasar Rwanda, yanzu haka na kaucewa shiga sararin samaniyar Kongo. Bayanai sun ce wani jirgin da ya tashi daga babban birnin kasar Rwanda zuwa birnin Landan na kasar Birtaniyaa ranar Talata, an tilas ya sauya hanyarsa don yin aiki da dokar, wanda a yanzu ya shafi “dukkan jiragen...
    Shugabannin kungiyoyin raya kasashen gabashi da kuma kusanci na Afrika (EAC da SADC), sun yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a gabashin Jamhuriyar DR Congo. Bangarorin sun bayyana hakan a wani taron hadin guiwa da suka gudanar a birnin Dar es Salaam, na kasar Tanzania a jiya Asabar. A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, sun kuma bukaci da bude manyan tituna da filin jirgin saman Goma, da kuma tattaunawa kai tsaye tsakanin Kinshasa da kungiyar M23. Saidai taron, bai yi Allah wadai da Rwanda ba kan shigar ta cikin rikicin ba. Taron na hadin gwiwa ya tabbatar da hadin kai da jajircewa wajen ci gaba da marawa DRC baya a kokarin da take yi na kare...
    Yau Asabar shugabannin kasashen raya tattalin arzikin kasashen Gabashi da Kudancin Afrika EAC da SADC za su gana a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya domin tattauna rikicin gabashin DRC. Shugaban kasar Kenya, William Ruto, dake jagorantar kungiyar EAC, ya sanar da halartar takwarorinsa na Congo da Rwanda. Tun da farko a ranar Juma’a, ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun gana domin samun nasarar wannan tattaunawar, inda fadar shugaban kasar ta Kwango ta gabatar da bukatunta da suka hada da : tsagaita bude wuta nan take, janyewar dakarun M23 da na Rwanda daga yankin Congo, da sake bude filin jirgin saman Goma, da mayar da birnin ga hannun halastattun hukumomi. A ranar Juma’a, a wani taro a Malabo, Kungiyar...
    A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA. MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe, yayin da rahotanni ke cewa faɗa na kara yaɗuwa zuwa wasu sassan ƙasar, sannan take hakkin ɗan’adam na ƙara munana. Jakadan Congo a Geneva ya ce gwamnatin ƙasar na buƙatar MDD ta gudanar da cikakken bincike kan hakan. Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun yi amannar cewa ƴan tawayen M23 da sojojin Rwanda da na Congo duk sun aikata munanan laifuka. Sai dai har yanzu Rwanda...
    Shugabna Pual Kagame na kasar Rwanda ya bayyana cewa ba zai dakatar da goyon bayana da yake bawa kungiyar yan tawaye ta M23 ba, wadanda a cikin yan kwanakin da suka gabata sun kwace wurare da dama a arewacin Kivu na kasar DMC daga cikin har da birnin Goma babban birnin lardin. Shafin yanar gizo na ‘Afirca News’ ya nakalto kagami yana cewa ya a shirye yake ya shiga yaki da kowa saboda kare matsayinsa. A yau Alhamis dai mayakan M23 sun kammala kwace iko da birnin Goma babban birnin yankina kuma a halin yanzu sun nosa zuwa garin Bukavu babban birnin lardin Kivu ta kudu. Wannan dai shi yaki mafi girma wadanda ake yi a yankin KIvi tun shekara...
    Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin na (PSC) zai gudanar da wani zaman gaggawa a yau Talata kan halin da ake ciki a yankin, wanda ke fama da yakin da ake yi tsakanin dakarun Kongo da mayakan M23″ in ji Paschal Chem-Langhee, mai magana da yawun kwamitin, yayin da al’amura ke kazanta a Goma, babban birnin gabashin DRC. Kafin nan daruruwan ma’aikatan MDD da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo sun tsere zuwa makociyar kasar, Rwanda, yayin da gomman sojojin Kongo din suka “mika wuya” ga jami’an tsaron Rwanda a ranar Litinin, bayan ‘yan...
    Shugaban kasar Kenya William Ruto a wata sanarwa da ya fitar ya sanar da cewa, zai gudanar da wani babban taro na musamman na kungiyar kasashen gabashin Afirka EAC a cikin sa’o’i 48 masu zuwa tare da halartar shugaban kasar Congo Félix Tshisekedi da shugaban Rwanda Paul Kagame. Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan tawayen M23 ke ci gaba da dannawa kan birnin Goma inda ake ta musayar wuta. A cewar wasu majiyoyin MDD da na tsaro, sojojin Rwanda da mayakan M23 sun shiga birnin a ranar Lahadi, in ji kamfanin dillancin labaran Faransa. Yakin da ake gwabzawa a kusa da Goma da kuma harbe-harbe da aka yi a birnin ya kuma sa mazauna babban birnin...
۱