2025-07-04@02:43:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5225
«Gwamnan Bauchi»:
Kwamatin Harkokin Kananan Hukumomi na Majalisar Dokokin jihar Jigawa ya fara rangadin kwanaki biyu a karamar hukumar Roni a ci gaba da rangadin kananan hukumomin jihar 27 da kwamatin ya kaddamar. A jawabin sa a sakatariyar karamar hukumar Roni, Shugaban kwamatin Alhaji Aminu Zakari, ya ce tsarin mulkin kasa ya bai wa majalisa ikon dubawa...
Rasha ta zama ƙasa ta farko da a hukumance ta amince da gwamnatin ƙungiyar Taliban da ke mulkin ƙasar Afghanistan. Wannan na zuwa ne bayan Rashar ta karɓi takardun shaidar kama aiki na sabon jakadan Afghanistan, wanda hakan ya sa ta zama ƙasa ta farko da ta amince da gwamnatin Taliban a ƙasar. Ambaliya da...
Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta bayyana cewa, ambaliya da iska mai ƙarfi sun rushe da lalata gidaje 171 a yankunan jihar cikin watanni biyu da suka gabata, lamarin da ya haddasa asara da kuma mutuwar yara huɗu. Sakataren zartarwa na Hukumar SEMA, Malam Abdullahi Haruna Abdullahi ne ya bayyana hakan...
Majalisar riƙon ƙwarya ta Gwamnatin Mali ta bai wa Shugaban Mulkin Sojin ƙasar, Janar Assimi Goita, wa’adin mulki na shekara biyar, wanda za a iya sabunta shi fiye da sau daya ba tare da zaɓe ba. A bara ne Janar Goita ya yi alƙawarin maido da mulkin dimokuradiyya a ƙasar, sai dai hakan ba ta...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Harin Kan Cibiyar Makamashin Nukiliya Cin Amanar Diflomasiyya Ce
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran cin amanar diflomasiyya ce Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana harin da sojojin Amurka suka kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya a matsayin cin amanar diflomasiyya da kuma cewa wani mataki ne da...

Kwamandan Sojojin Iran Ya Ziyarci Gidan Babban Jami’in Sojin Kasar Da Ya Yii Shahada Lokacin Yakin Baya-Bayan Nan
Kwamandan sojojin kasar Iran ya jaddada cewa: Sojojin Iran sun shirya tsaf don kare juyin juya halin Musulunci da kasarsu A yayin ziyarar da ya kai wa iyalan shahidi kwamandan tsaron cikin gida na kasar Iran Kanal Mohammad Alizadeh; Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Jajirtattun sojojin kasar Iran...
Dele Momodu, sanannen ɗan jarida kuma jigo a jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa yawancin magoya bayan jam’iyyar sun fara ficewa daga cikinta, suna barin tsarin jam’iyyar a hannun ministan babban birnin tarayya. Dele ya bayyana hakan ne yayin wani shiri a Channels TV, inda ya nuna cikakken goyon bayansa ga sabon ƙawancen jam’iyyun adawa da...
Sojojin mamayar Isra’ila sun kai munanan hare-hare kan Falasdinawa da suka rasa gidajensu da fama da masifar yunwa, lamarin da ya yi sanadiyar shahadan mutane da dama Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan ‘yan gudun hijira da kuma wadanda ke jiran agaji a zirin Gaza, inda a daren...
Sanarwar ta ƙara da cewa, a yayin taron an sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Yankunan Karkara, sannan aka tattauna da masu ruwa da tsaki, tambayoyi da amsoshi, ra’ayoyi, da kuma alƙawura. A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya ce ya gaji matalauciyar gwamnatin...
Uwargidan shugaban ƙasa, Remi Tinubu ta bayar da gudummawar Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin ya rutsa da su a wasu yankunan Jihar Filato. Uwargidan shugaban ƙasar wacce ta bayyana bayar da tallafin a yayin ziyarar jaje da ta kai jihar a ranar Alhamis, ta ce kuɗaɗen da ta bayar ba na gwamnati ba ne,...
Wata Kotun Majistare da ke jihar Kano ta yanke wa fitaccen ɗan TikTok, Umar Hashim da aka fi sani da Tsulange, hukuncin ɗauri na shekara ɗaya bisa laifin aikata abinda ya saɓa da tarbiyya a bainar jama’a. Alƙaliyar kotun, Hadiza Muhammad Hassan, wadda ke zaune a Gyadi Gyadi, ta samu Tsulange da laifi na zubar...
Bashir Ahmad, hadimin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce shugaban yana cikin ƙoshin lafiya a birnin Landan. A cewarsa, labarin da ke yawo cewa Buhari na fama da mummunar rashin lafiya har yana kwance a ɗakin kulawa na musamman (ICU), ba gaskiya ba ne. Lakurawa Sun Kashe Mutane 15 a Sakkwato ‘Yan Sanda Sun...
Wasu ‘yan bindigar da ake zargi Lakurawa ne sun kashe mutane sama da 15 a wani sabon hari a Karamar Hukumar Tangaza ta Jihar Sakkwato. Wani mazauni kauyen Kwalajiya ya ce ‘yan bindigar Lakurawa sun zo kauyen a daren Lahadi har zuwa Asuba ta ranar Litinin inda suka kashe wasu mutane, a yayin da suka...
Wasu ‘yan bindigar da ake zargi Lukurawa ne a wani sabon hari sun kashe mutane sama da 15 a Qaramar Hukumar Tangaza ta jihar Sakkwato, ranar Litinin da ta gabata. Babban Jami’i a Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Qasa(Red Cross) reshen Sakkwato Alhaji Abubakar Ainu ya tabbatar wa Aminiya harin wanda ya yi matuqar...
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta hana yunqurin fasa wani shago da wasu vata-gari suka yi qoqarin yi a Unguwar Buba Shongo da ke cikin birnin Gombe, inda ta qwato wani babur da kayan da ake zargin an yi niyyar amfani da su wajen fasa shagon. A cewar sanarwar da mai Magana da Yawun...
A ci gaba da sauya sheƙar da ’yan Majalisar Wakilai na Tarayya ke yi a ranar Alhamis wasu mambobi bakwai daga Jihar Akwa Ibom sun sanar da sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC mai mulki. Cikin waɗanda suka sauya sheƙa sun haɗa da shida daga Jam’iyyar PDP da kuma ɗaya daga Jam’iyyar YPP. ’Yan Najeriya sun...
Birgediya Janar Abdulsalam ya roƙi jama’a da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai, duk da cewa rufe kasuwannin na iya kawo wata matsala ga rayuwar yau da kullum. “Gwamnati na ƙoƙarin ganin an rage tasirin da rufe kasuwannin ka iya haifarwa ga al’umma. Muna roƙon ku fahimce mu saboda zaman lafiya da tsaro,” in...
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wahalhalu sun yi yawa a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda har ya sa mutane suka fara fatan dawowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Yayin da yake magana a birnin Abuja, Amaechi ya ce Najeriya ta taɓarɓare matuƙa, inda ya ce sauyin gwamnati ne kawai zai magance matsaloli. Gwamnatin Yobe...
Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wahalhalu sun yi yawa a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda har ya sa mutane suka fara fatan dawowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari. Yayin da yake magana a birnin Abuja, Amaechi ya ce Najeriya ta taɓarɓare matuƙa, inda ya ce sauyin gwamnati ne kawai zai magance matsaloli. Gwamnatin Yobe...
Babban hafasan hafsoshin kasar Iran Major General Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa idan HKI ta kuskura ta sabonta yaki da kasar Iran ta zata fuskanci maida martani mafi tsanani. Janar Musawi ya bayyana haka ne a jiya laraba a lokacinda yake hira da tashar talabijan ta almayaden ta kasar Lebanon Ya kuma kara da cewa...
Dubabban falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan ne gwamnatin HKI ta kora daga gidajensu tun bayan ta fara wani shiri wanda ta kira Katangan karfe a farkon wannan shekarar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kungiyar Doctors without Borders wato MSF a takaice tana fadar haka a jiya Laraba. Rahoton ya...
A jiya laraba ce aka gudanar da taron addu’a da kuma girmama shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka farwa kasar Iran a ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da taron girmamawan ne a masallacin Imam Khomane (q) da...
Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da...
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa HKI zata gamu da maida martani mafi tsanani idan ta seke farfado da yaki da JMI, sannan sai sun yi nadamar fara yakin kamar yaki da kwanaki 12. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Qalibof yana fadar haka a jiya Laraba...
Gwamnatin Jihar Yobe, ta sanar da rufe kasuwannin garuruwan Katarko, Kukareta da Buni Yadi saboda barazanar matsalar tsaro. Wannan mataki na ɗaya daga cikin hanyoyin da gwamnatin ke ɗauka domin inganta tsaro a yankunan. Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 6, sun raunata wasu a...
Magoya bayan Liverpool da masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya na cikin jimami bayan ɗan wasan Portugal, Diogo Jota, ya rasu a wani hatsarin mota. Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Alhamis a yankin Zamora na ƙasar Spain. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 6, sun raunata wasu a Kwara NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun...
Aƙalla jami’an tsaro shida ne suka rasu bayan wata arangama da suka yi da ’yan bindiga a yankin Gada Woro a kan hanyar Patigi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a Jihar Kwara. Waɗanda suka rasu sun haɗa da ’yan banga guda biyar da ɗan sanda ɗaya. ‘Mutum 600 da suka bace a ambaliyar Mokwa sun...

Muhsin Rizai: Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Bayar Da Umarni Da Jagorantar Yakin “Wa’adussadiq 3”
Tsohon kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran Muhsin Rizai ya bayyana cewa; Jagoran juyin musulunci Ayatullah sayyid Ali Khamnei ne ya jagoranci da kuma bayar da umarnin yakin “Wa’adussadiq 3” akan HKI. Dr. Muhsin Rizai wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron girmama shahidai da aka yi a jiya Laraba a babban masallacin...
Minstan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya mayar da martani da kakkausar murya akan furucin jami’ar diplomasiyya ta tarayyar turai Kaya Jallas na cewa Iran ta dakatar da shirinta na makamashin Nukiliya, yana mai cewa; Jallas ta jahilci abinda dokokin NPT su ka kunsa. Abbas Arakci ya ce; Idan manufar ganawa da kwamitin hadin gwiwa...
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa; Batun makamin kungiyar ta Hizbullah na cikin gida ne, don haka ba za su taba mika makamansu ga abokan gaba HKI ba. Sheikh Na’im Kassim Wanda ya gabatar da jawabi a jiya Laraba da dare a yayin tarukan Ashura, ya bayyana cewa; Ba za mu...
Wani ɗan Ghana da aka yi ƙoƙarin yaudararsa shi ma ya tsere, ya koma Ghana, inda ya kai rahoto ga hukumomi, abin da ya haifar da haɗin gwiwar ƙasashen biyu don ceton Sammed. Sakamakonhaɗin gwiwar da ’yansanda suka yi a Abuja, an ceto Sammed. Adejobi ya ce an ɗauki matakai don kama waɗanda suka aikata...
Jaridun kasar Amurka sun bayyana cewa; Isra’ila ta kasa cimma manufofin da ta ayyana a yaki da Iran, sannan kuma ta kara zama saniyar ware a duniya. Mujallar “Foreign Policy” ta yi ishara da sakamakon yakin da take cewa, ya zamarwa Amurka da kawarta Isra’ila juyewar reshe da mujiya,domin harin da su ka kai wa...
’Yan Majalisar Wakilai daga jihohin Neja da Kwara sun shaida wa majalisar cewa mutum 600 da suka bace a ambaliyar garin Mokwa kuma har yanzu ba a gan su ba, za a dauka su ma sun mutu. Dan majalisa Joshua Audu Gana (Neja) da Saba Ahmed Umaru (Kwara) ne suka bayyana hakan a yayin gabatar...
Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne, sun kai hari ƙauyen Kwalajiya da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutum 15. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Talata, lokacin da mutum ke sallar Azahar. NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun kafin sanar da sabuwar ƙawance da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El’rufai da wasu manyan ‘yan siyasa ne aka fara zargin yi wa wannan haɗaka zagon ƙasa da kawo cikas ga tafiyar. Ɗaya daga cikin irin waɗannan zagon...
Tauraron Kannywood kuma mai sayar da maganin gargajiya, Abdullahi Alhikima ya magantu bayan da wasu ‘yan Kannywood suka caccake shi kan kalaman da ya yi a kansu. Aminiya ta rawaito cewa hatsaniyar ta samo asali ne bayan fitattun ‘yan Kannywood da suka hada da Abdul M Sharif, Nura M Inuwa, Abubakar Bashir Maishadda, Sadik Sani...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yau Laraba a taron manema labaru da aka gudanar cewa, kayayyakin Sin sun shiga kasuwar duniya, inda suka kara baiwa masu sayayya na kasa da kasa damar samun zabi. Jami’ar ta yi tsokacin ne bisa yadda batun wasu kayan shayi na kasar Sin ya...
Tsangayar Kwalejin koyar da aikin Jinya ta Jihar Jigawa dake garin Birnin kudu ta gudanar da bikin kaddamar da sabbin dalibai 116 da za su yi karatun difloma ta kasa da babbar difloma ta kasa karon farko na shekarar karatu ta 2024 zuwa 2025. A jawabinsa wajen taron kaddamar da daliban, kwamishinan ma’aikatar lafiya na...
Amurka ta dakatar da tallafin makaman da take bai wa Ukraine, tana mai bayyana damuwa kan raguwar makamanta a rumbun adana su. Mai magana da yawun Fadar Gwamnatin Amurka, Anna Kelly a watan sanarwar da ta fitar, ta ce a halin yanzu muradun Amurka ne kan gaba ta bangaren tsaro, don haka dole ne ta...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar Hamas ta sanar da karɓar tayin tsagaita wuta a yaƙin Gaza kuma tuni ta soma nazarin sabuwar yarjejeniyar aka gabatar mata. Hamas wadda ta nuna alamun samun masalaha ta bayyana cewa manufar yarjejeniyar ita ce kawo ƙarshen hare-hare Isra’ila da janye dakarunta daga yankin. Za mu ɗauki mataki kan mambobinmu da ke shirin shiga...
Jakadan Pakistan a kasar Sin, Khalil Rahman Hashimi ya ce, “sabuwar dokar ta bayar da karin kariya har ma da wani sauki na musamman ga kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin. Akwai tanade-tanade da dama a kasar Sin wadanda suke bayar da kwarin gwiwa ga kamfanoni masu zaman kansu don su iya bunkasa harkokinsu...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da cibiyar Fasaha ta Zamani ta Arewa maso Yamma da hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta gina a Kano, wadda matasa suka lalata a lokacin zanga-zangar ƙuncin rayuwa ta #EndBadGovernance a watan Agustan 2024. Ministan Harkokin Sadarwa Dr. Bosun Tijani, ne ya wakilci shugaban ƙasa a wajen bikin...

Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Irin Aniyar Da Gwamantinsa Ta Kudurta Wajen Kare Tsaron Kasa Da Al’ummarta
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun kuduri aniyar kare kan iyakokin Iran da tsaron kasar da kuma al’ummarta Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce: “Suna goyon bayan zaman lafiya, kuma ba su amince da yaki ba, amma a lokaci guda kuma, suna tabbatar da aniyarsu ta kare kan iyakokin Iran da tsaron kasarta...
Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ta jaddada cewa: Gudanar da masana’antun nukiliyar kasar za ta ci gaba da kuma fadada bunkasar da suke samu Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, dangane da yadda yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, ya jaddada cewa: Masana’antar nukiliya ba wani abu ba...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasarsa na da niyyar karfafa hadin gwiwa da Iran da kuma kara karfin tsaron kasar ta Iran Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Riyabkov ya jaddada cewa: Kasar Rasha za ta karfafa hadin gwiwa da Iran a dukkan fannoni, gami da kara karfin tsaron kasar...
Falasdinawa da dama ne suka yi shahada yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani sabon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna na Gaza Fararen hula Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata wasu masu yawa sakamakon kazamin harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna a...
Jagoran sabuwar jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya bayyana cewa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, zai jagorance su wajen karɓar mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. Jam’iyyar haɗakar, wacce ta ƙunshi fitattun ’yan siyasa, ta naɗa David Mark a matsayin Shugaba, tare da tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin Sakatare....
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum, mai shekaru 35 daga ƙauyen Kunji da ke Kwadon, bisa zargin mallakar jabun kuɗi. Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama Kawu ne a ranar 28 ga watan Yuni, 2025, a ofishin ’yan sanda na Lawanti, sannan aka kai shi ofishin Amada...

Yawan Kudin Shiga Da Sin Ta Samu A Fannin Sana’ar Manhaja A Watanni 5 Na Farko Na Bana Ya Wuce Yuan Triliyan 5.5
Yau Laraba, Hukumar Kula da Fasaha ta Kasar Sin (MIIT) ta ba da rahoton yanayin tafiyar masana’antar manhajoji ta kasar daga watan Janairu zuwa Mayun shekarar 2025 da muke ciki. A cewar rahoton, masana’antar manhaja da hidimar fasahar sadarwa ta Sin tana gudana yadda ya kamata. Da farko, yawan kudaden shiga da aka samu kan...