’Yan sanda sun cafke ’yan fashi 6, sun ƙwato motocin sata 4 a Kano
Published: 20th, May 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata fashi da makami tare da ƙwato motocin sata guda huɗu, bayan wani samame da suka kai.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu nasarar ne a ranar 10 ga watan Mayu, 2025, inda tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin CSP Rabiu Gidado ta kama wani da ake zargi, Saidu Abubakar, a Jihar Filato.
An same shi da wata mota ƙirar Toyota Corolla samfurin 2016 da aka sace wa wani mazaunin unguwar Naibawa a Kano.
Yayin gudanar da bincike, Abubakar ya amsa cewa yana cikin wata ƙungiyar masu satar motoci da fashi da makami, kuma ya bayyana yadda suke aiwatar da ta’asarsu.
Kiyawa, ya kuma ce a ranar 16 ga watan Mayu, jami’an rundunar sun kama wani Ibrahim Isa a Kano, yana ƙoƙarin sayar da wata mota ƙirar Howo concrete mixer da aka sace a Ƙaramar Hukumar Kazaure a Jihar Jigawa.
Kakakin ya ce dukkanin waɗanda ake zargin na taimaka wa bincike, kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda yan fashi Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Mai shekara 70 ya kashe ƙanwarsa kan gadon gona a Jigawa
Wani mummunan lamari na kisan gilla ya afku a ƙauyen Galadanchi da ke Ƙaramar hukumar Dutse a Jihar Jigawa.
Rundunar ’yan sandan jihar ta kama wani tsoho mai shekara 70 bisa zargin kashe ƙanwarsa saboda rikici kan filin gado.
Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a BornoCikin wata sanarwa da kakakin rundunar y’an sandan jihar, SP Lawan Adam Shi’isu ya fitar ya ce tsohon mai suna Adamu Yakubu – ɗan asalin ƙauyen Galadanchi ne wanda ya samu saɓani da ƙanwarsa mai suna Hannatu Hashimu, mai shekara 45, kan rabon gadon wata gona da suka gada.
Bayanan binciken farko da ’yan sanda suka fitar, ya nuna cewa wanda ake zargin ya jefi ƙanwar tasa da sanda ne a lokacin da suka yi zazzafar gardama a tsakaninsu kan rabon gadon.
Rikicin dai ya fara ne kamar da rashin jituwar musayar kalamai, amma ya rikiɗe zuwa tashin hankali.
Inda tsohon da ake zargin ya kai wa ƙanwar tasa duka da sanda, wanda ya yi sanadin mutuwar Hannatu Hashimu. Kamar yadda bayanan ’yan sanda ya nuna.
”Marigayiyar ta fita daga gidan a fusace, ta koma gidan aurenta, da zuwanta kuma ta faɗi ta suma, nan take aka garzaya da ita asibiti inda likitocin Babban Asibitin Dutse suka tabbatar da mutuwarta”, cewar ’yan sandan.
Rundunar ’yan sandan sun kama tsohon da ake zargin, inda yanzu haka suke gudanar da bincike.