Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Yana fatan tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka za ta kai ga cimma yarjejeniya ta gaskiya

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshgan ya bayyana cewa: Iran tana fatan tattaunawarta da Amurka za ta kai ga cimma yarjejeniya ta gaskiya da za ta tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin.

A yammacin jiya Lahadi, a gefen taron dandalin tattaunawa na Tehran na shekara ta 2025, a wata ganawa da ministan harkokin wajen masarautar Oman Badar bin Abdullah al-Busaidi, Shugaba Pezeshkian ya yaba da irin kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma irin rawar da gwamnatin Oman take takawa wajen daukar nauyin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Yana mai cewa: “Suna fatan sakamakon kokari da kuma sahihan manufofin Sultan Haitham bin Tariq, wadannan shawarwarin za su kai ga cimma yarjejeniyar adalci da za ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.”

Shugaban na Iran ya jaddada wajabcin kara samun kusanci a tsakanin kasashen musulmi, yana mai cewa “masu kusanci da juna da fadada hadin gwiwarsu, haka nan masu fatan cutar da al’ummar musulmi za su zama masu haifar da sabani da rabuwar kai a tsakaninsu.”

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

ASCSN Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Nada Muhammad Dagaceri Shugaban Ma’aikata

Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati ta Najeriya ta yaba wa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa nada Alhaji Muhammad K. Dagaceri a matsayin shugaban ma’aikata na jiha.

Shugaban  ƙungiyar na kasa, kuma mataimakin shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa TUC, Kwamared Shehu Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya kai ziyara ga shugaban ma’aikata, Alhaji Muhammad Dagaceri, a ofishinsa.

Ya tabbatar wa shugaban ma’aikatan da cikakken goyon baya da haɗin kan ƙungiyar wajen cimma manufofin da aka tsara a matsayinsa na shugaban ma’aikatan jiharta Jigawa.

“Kungiyarna sa ran yin haɗin gwiwa da zai ƙara inganta aikin ma’aikata da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.” In ji shugaban ƙungiyar.

A jawabinsa, Alhaji Muhammad Dagaceri ya bayyana godiyarsa bisa wannan ziyara, tare da jaddada kudirin wannan gwamnati na samar da kyakkyawar alaka tsakanin ta da dukkan ƙungiyoyin masana’antu a fadin jihar.

Usman Muhammad Zaria

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Taya Wadanda Suka Yi Nasara A Zaben Cike Gurbi Murna
  • Iran Ta Bayyana Cewa: Tana Sanya Ido Kan Abin Da Ke Faruwa A Kudancin Caucasus Cikin Lura
  • Babban Sakataren Majalisar Tsaron Kasar Iran Ya Bayyana Cewa; Ba Zasu Amince Da Shiga Tsakanin Iran Da Iraki Ba
  • Amurka Ta Dakatar Da Bawa Falasdinawa A Gaza Visar Shiga kasar
  • Shugaban Iran na Shirin fara wata muhimmiyar ziyara a Armenia da Belarus
  • An kafa dokar hana zance tsakanin saurayi da budurwa a Kano
  • India Ta Dage Kan Maida martani da hana Shigowar Kayakin Amurka Kasar
  • GORON JUMA’A
  • Manufofin Hulda Da Kasashen Wajen Da Nijeriya Ke Bukata
  • ASCSN Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Nada Muhammad Dagaceri Shugaban Ma’aikata