Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taro Na 34 Na Kasashen Larabawa
Published: 17th, May 2025 GMT
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga shugaban Iraqi Abdul Latif Rashid, wanda kuma shi ne shugaban karba-karba na majalisar shugabannin kasashen kungiyar Larabawa, tare da taya murnar kaddamar da babban taron kungiyar na 34, a birnin Baghdad na Iraqi.
Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru sama da 80 da kafata, kungiyar kasashen Larabawa ta kasance mai mayar da hankali kan inganta hadin kai da karfafa yankin Larabawa da furta matsalolin kasashen da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take ta hada hannu da kasashen Larabawa wajen zurfafa aminci da ingiza hadin gwiwar moriyar juna da kara musayar al’adu da musaya tsakanin jama’a da hada hannu a tafarkin da kowannensu ya dauka na zamanantar da kansa da gina al’ummar Sin da ta Larabawa mai makoma ta bai daya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp