2025-05-15@21:32:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3794
«idan aka kwatanta da»:
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon rikici da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato. Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata gonaki, sace shanu, da kuma kai wa dabbobi hari, wanda mutane daga ɓangaren Fulani da Berom ke zargin juna da aikatawa. Ce-ce-ku-ce ya ɓarke kan bayyanar Sheikh Alƙali a shirin ‘Gabon talkshow’ Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS A cewar sanarwar da rundunar Operation Safe Haven ta fitar, matsalar ta fara ne a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, 2025, bayan wasu matasa da ake zargi sun kashe shanu da suka shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom....
Hukumar da ke yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC reshen shiyyar Kaduna ta gurfanar da wani Muhammad Kabir a gaban kotu tare da yanke masa hukunci, wanda ya kasance mai wallafa bidiyo a shafukan TikTok da Instagram. An gurfanar da Muhammad Kabir a gaban mai shari’a Rilwan Aikawa na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna bisa laifin wulaƙantawa da lalata takardun Naira. An kama wata mata kan safarar makamai zuwa Katsina Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato An kama Kabir ne a ranar Talata, 29 ga Afrilu, 2025 a Tudun Wada, Jihar Kaduna saboda yin wani bidiyo a shafinsa na TikTok da Instagram @youngcee0066 yayin da yake watsa takardar Naira a...
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da aka sace shanu da dama a wani sabon rikici da ya ɓarke a Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato. Sabon rikicin ya samo asali ne daga lalata gonaki, sace shanu, da kuma kai wa dabbobi hari, wanda mutane daga ɓangaren Fulani da Berom ke zargin juna da aikatawa. Ce-ce-ku-ce ya ɓarke kan bayyanar Sheikh Alƙali a shirin ‘Gabon talkshow’ Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS A cewar sanarwar da rundunar Operation Safe Haven ta fitar, matsalar ta fara ne a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, 2025, bayan wasu matasa da ake zargi sun kashe shanu da suka shiga gonakinsu a ƙauyen Dayan, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom....
Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Jigawa ta ce ta dauki mataki mai muhimmanci wajen tabbatar da kiyaye ka’idojin aikin jarida ta hanyar kafa Kwamitin Ladabtarwa da kuma Kwamitin Ilimi da Horaswa. A cikin wata sanarwa da Sakatariyar kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed ta fitar, ta bayyana cewa Kwamared Sabo Abdullahi Guri ne zai jagoranci Kwamitin Ladabtarwar tare da Kwamared Mati Ali, da Dr. Musa Idris Barnawa da Yusuf Sulaiman a matsayin mambobi, yayin da Muhammad Askira Musa zai kasance Sakataren kwamitin. Sanarwar ta bayyana cewa an dora wa kwamitin alhakin tabbatar da bin ka’idojin aikin jarida, warware matsalolin rashin ladabi ko sabawa doka cikin aikin, da kuma tabbatar da gaskiya da rikon amana a aikin jarida a...
Majalisar wakilai za ta binciki yadda aka samu mummunar faduwa a jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) ta 2025 da hukumar shirya jarabawar (JAMB) ta gudanar kwanan nan. Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa, Adewale Adebayo ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Da yake gabatar da kudirin, ya koka da cewa, da yawa daga cikin daliban, sun yi tafiya mai nisa domin zana jarabawar UTME a cibiyoyin jarabawar. Amma abin takaici, sai ga sakamakon ya fito da koma baya da yawa. Duk da cewa, hukumar JAMB ta amince cewa, tangardar na’ura ce ta janyo faduwar amma akwai bukatar a binciki hukumar. Idan za a iya tunawa, sakamakon jarabawar UTME na 2025 da JAMB...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da amfani da katangewar da ta yi wa Gaza a matsayin makamin kawar da wata al’umma. A wani rahoto data fitar yau Alhamis, kungiyar ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da yin amfani da shingen da aka yi wa Zirin Gaza a matsayin “wani makami na share al’umma,” yayin da hukumomin Isra’ila suka hana shigar da duk wani agajin jin kai cikin yankin Falasdinu tun ranar 2 ga Maris. Katange zirin da Isra’ila ta yi ya fi karfin dabarun soji, ya kai wani yunkuri na share al’umma inji Federico Borello, darakan zatarwa mai riko na kungiyar a cikin wata sanarwa da ya caccaki shirin Isra’ila na zaunar da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rasha da Ukraine sun tabbatar da aikewa da tawaga dukkansu domin gudanar da tattaunawa ta kai tsaye tsakanin kasashen dake rikici da juna. Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya aike da tawagar Ukraine zuwa birnin Istanbul na kasar Turkiyya domin ganawa da wakilan Rasha domin tattaunawa kan zaman lafiya, amma shi da kansa ba zai je can ba, kamar yadda wani babban jami’in Ukraine ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP. Jami’in ya ce “Shugaban ya yanke shawarar cewa Ukraine za ta shiga tattaunawa da Rasha a Istanbul amma Volodymyr Zelensky ba zai je Istanbul ba saboda taron “ba a matakin shugabanni ba. Ita ma fadar Kremlin ta sanar da jerin sunayen wakilan kasar don tattaunawa da Ukraine a Istanbul....
Shugaban Majalisar Dokokin Iran Mohammad Baqer Qalibaf ya ce kamata ya yi kasashen Iran da Aljeriya su hada kai wajen kai kayan agaji a zirin Gaza da yaki ya daidaita. Qalibaf ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar al’ummar kasar Aljeriya Ibrahim Boughali a ranar Laraba a birnin Jakarta na kasar Indonesiya, a gefen taron ‘yan majalisar dokokin na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta PUIC karo na 19. Ya jaddada muhimmancin samar da hadin kai wajen tunkarar hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke yi a Falasdinu da kuma maido da hakkokin al’ummar Falastinu da ake zalunta a zirin Gaza. Qalibaf ya yi kira ga kasashen musulmi da su hada kai su nemo...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A makon nan ne aka ga hotunan Sheikh Alƙali Zariya ya halarci zauren tattaunawa na fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, wanda ake kira ‘Gabon Talkshow’, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta. Gabon Talkshow dandali ne da jaruma Hadiza ke gayyatar mashahuran jarumai da mawaƙa domin tattauna game da rayuwarsu da ayyukansu a masana’antar nishaɗi. Tsaro: Tinubu ya ƙaddamar da rundunar tsaron daji a faɗin Najeriya Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS Bayyanar Sheikh Alƙali a wannan dandali ya jawo suka mai tarin yawa daga al’umma. Wasu na ganin bai dace da matsayin malami irinsa ya halarci irin wannan dandali ba, domin ba wajen ilmantarwa ba ne ko karantarwa. A cewar wasu, hakan zai...
An karrama Injiniya Dr. Mohammed Uba da lambar yabo ta kasa ta Rootswatch ta shekarar 2025, a matsayin girmamawa bisa gagarumin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma, aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa, da kuma kyakkyawan jagoranci. An mika wannan lambar yabo ne a yau a Cibiyar Karramawa ta Kasa da Kasa da ke Abuja. An karrama Dr. Uba tare da wasu shugabannin kananan hukumomi guda uku daga Jihar Jigawa da suka hada da Abdullahi Na Layi, Jarma na Garki, da Malam Madori, saboda hadin gwiwarsu wajen bunkasa ci gaban al’umma tun daga yankunan karkara. Taron ya jawo hankalin manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar, kuma ya kasance wata hanya ta ƙarfafa gwiwar shugabannin kananan hukumomi...
Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta kama wata mata mai shekara 21 mai suna Fatima Salisu da ake zargi da safarar makamai, biyo bayan samun bayanan sirri. Kakakin rundunar ’yan sanda, Ramhan Nansel ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis. Ganduje ya halarci Majalisar Wakilai don sheda ’Yan Majalisa 2 zuwa APC Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato Kakakin ya ce an kama Fatima ne da laifin safarar alburusai ta yankin Keana da Doma a cikin Jihar Nasarawa don taimakon masu aikata laifuka a Katsina, inda take zaune. “Cikin gaggawa kan bayanan sirri da aka samu, Kwamishinan ’yan sanda CP Shetima J. Mohammed, ya ba da umarnin tura sashin yaƙi da masu garkuwa da...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa sabuwar rundunar masu tsaron daji a faɗin ƙasar nan domin tinkarar matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a cikin dazukan Najeriya. A ƙarƙashin wannan sabon shiri, za a ɗauki sama da mutane 130,000 aiki da za su samu horo na musamman da kayan yaƙi na zamani domin kare dazuka guda 1,129 da ke sassa daban-daban na ƙasar nan. Hauhawar farashi ya ragu zuwa kashi 23.71 — NBS Mutum 2 sun shiga hannu zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Gombe Wannan na cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sunday Dare, ya fitar a shafinsa na X. Sanarwar ta bayyana cewa an...
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci zauren Majalisar Wakilai a ranar Alhamis domin ganewa idanunsa ficewar wasu mambobi biyu na Jam’iyyar adawa ta NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC. ’Yan majalisar biyu, sun haɗa da: Dan Majalisar Wakilai, Abdullahi Sani Rogo mai wakiltar mazaɓar Rogo/Karaye da kuma Ɗan Majalisar Wakilai Kabiru Alhassan Rurum mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Rano/Bunkure/Kibiya, sun sauya sheƙa a ranar Alhamis. Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato Dalilin da ya sa gwamna Bala ya yi ƙoƙarin mari na – In ji Minista Hakazalika mamba mai wakiltar mazaɓar Ijesha Oriade/Obokun na Jihar Osun, Wole Oke, ya kuma bayyana ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC....
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya sauka kaɗan a watan Afrilu 2025 zuwa kashi 23.71, daga kashi 24.23 da aka samu a watan Maris. Wannan na nuna cewa hauhawar farashi ya ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda a watan Afrilun 2024 aka samu kashi 33.69. Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato Wuta ta kashe ɓarawon wayar lantarki a Jigawa Wannan ragi da aka samu a watan Afrilu ya kai kusan kashi 10. Har ila yau, hukumar ta ce hauhawar farashi daga wata zuwa wata ya ragu a watan Afrilu, inda aka samu kashi 1.86, ƙasa da kashi 3.90 da aka samu a watan...
A wasu rahotanni sun ce an kashe makiyayi guda ɗaya da shanu sama da 100 a wasu hare-hare da aka kai hari kan makiyaya a wasu ƙauyuka biyu da ke ƙananan hukumomin Jos ta Kudu da Jos ta Arewa a Jihar Filato. Hare-haren da ake zargin wasu ’yan bindiga ne da suka buɗe wa makiyaya wuta a lokacin da suke kiwo, wanda ke nuna rashin tsaro a yankunan da aka daɗe ana fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, lamarin da ke janyo asarar rayuka. Dalilin da ya sa gwamna Bala ya yi ƙoƙarin mari na – In ji Minista Wuta ta kashe ɓarawon wayar lantarki a Jigawa Sakataren Ƙungiyar Miyetti Allah Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na...
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana abin da ya janyo saɓani tsakaninsa da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, a lokacin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai ziyara jihar. A watan Afrilu, rahotanni sun bayyana cewa Mataimakin Gwamnan Bauchi, Muhammad Auwal Jatau, ya mari Minista Tuggar a cikin mota yayin da suke kan hanyar zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi. Wuta ta kashe ɓarawon wayar lantarki a Jigawa Najeriya ba za ta koma mulkin soja ba — Gowon Amma Mataimakin Gwamnan ya musanta faruwar hakan. Da yake zantawa da BBC Hausa, Tuggar ya ce saɓanin ya samo asali daga wajen Gwamna Bala Mohammed ba daga wajen mataimakinsa ba. “Muna cikin mota tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa,” in ji...
Wutar lantarki ta kashe wani wanda ake zargin ɓarawon wayar rarraba wutar ne a harabar Sabuwar Sakatariyar Jihar Jigawa. ’Yan sanda sun sanar cewa an tsinci gawar mutumin ta maƙale ne a karkashin kankare da manyan wayoyin lantarkin ke ciki. Kakakin ’yan sanda a Jihar Jigawa, Shiisu Lawal Adamu ya ce a safiyar ranar Alhamis ne suka samu kira daga Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Jigawa game da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa tuni aka dauke gawar zuwa Babban Asibitin Dutse, domin gudanar da bincike.
A yau Alhamis ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuyriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i, ya bayyana damuwar kasar akan halin da ake ciki a birnin Tripoli na kasar Libya wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane masu dama, tare da yin kira da a kawo karshen zubar da jini. Dr. Baka’i ya yi ishara da nauyin da ya rataya a wuyan dukkanin wadanda suke da hannu a fadace-fadacen da suke faruwa a cikin babban birnin kasar ta Libya, sannan ya bukace su da su taimaka wajen dawo da zaman tsaro a cikin kasar. Haka nan kuma ya bukace su da su koma kan teburin tattaunawa mai maimakon amfani da karfi, su kuma kaucewa bai wa kasashen waje damar tsoma...
Shugaban kasar Amurka wanda yake Ziyara a kasar Katar ya sanar da cewa gwamnatinsa tana son ganin tattaunawar da ake yi da Iran ta yi nasara, kuma ya yi Imani da cewa ana gab da kulla yarjejeniya da ita. Shugaban kasar ta Amurka ya kuma ce da akwai ci gaba sosai a cikin tattaunawar da ake yi a tsakanin Amurka da Iran akan shirinta na makamashin Nukiliya. Shugaban kasar ta Amurka dai ya bayyana hakan ne dai a lokacin da yake Magana da manema labaru a birnin Doha na kasar Katar. Da yake Magana akan yakin kasar Ukiraniya da Rasha, shugaban kasar ta Amurka ya kuma bayyana imaninsa da kusancin kawo karshen yakin tare da cewa yana kokarin ganin an...
’Yan bindigar da suka yi garkuwa da Shugaban Jami’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Ose a Jihar Ondo, Nelson Adepoyigi, sun riƙe mutanen da suka kai musu kuɗin fansarsa, sa’annan suka ƙara ƙudin fansar da suka nema da ninki shiga. A ranar Litinin da dare ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da Honorabul Nelson Adepoyigi a ƙofar gidansa inda suka nemi kuɗin fansa naira miliyan 100 kafin daga bisani a daidaita a kan miliyan biyar. Majiyoyin sun a lokacin da yake ƙoƙarin shiga gida ne maharan suka far masa suka fito da shi daga cikin motarsu, sa’annan suka make shi da gungumen ice sa’annan suka tafi da shi. Wani makusanci ga waɗanda suka kai kuɗin ya bayyana cewa, “Bayan daidaitawa...
Maza sun fi mata yawa wajen kamuwa da cutar. Hukumar ta kuma tabbatar cewa ba a samu sababbin waɗanda suka kamu da cutar ba daga ma’aikatan lafiya ba a wannan makon. Haka kuma, tsarin haɗin gwiwa na yaƙi da cutar zazzaɓin Lassa na ƙasa na ci gaba da aiki don tsara matakan daƙile yaɗuwar cutar. NCDC ta gargaɗi al’umma cewa ko da yake an samu raguwar sabbin masu kamuwa da cutar, har yanzu akwai barazanar cutar musamman a jihohin da ke da yawan masu cutar. Ta kuma buƙaci jama’a su riƙa kiyaye tsaftar muhalli, kai rahoton alamomin cutar da wuri, da kuma nisantar ɓeraye domin su ne ke yaɗa cutar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
Tashar talabijin din almayadin ta watsa labarin dake cewa, daga safiyar yau Alhamis zuwa yanzu, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun haura 40,mafi yawancinsu daga yankin Khan-Yunus. Tun da safiyar yau Alhamis ne dai sojojin HKI su ka fara kai hare-hare a yankuna mabanbanta na Gaza da su ka hada da Khan-Yunus. ‘Yan sahayoniyar sun yi amfani da manyan bindigogi da kuma jiragen sama na yaki. Adadin wadanda aka tabbatar da sun yi shahada ya zuwa yanzu sun haura 40. Sai dai wasu rahotannin da suke fitowa daga Gaza din sun ce, adadin shahidan ya karu zuwa 82. Jiragen HKI suna kai wa yankin na Gaza hare-hare daga kduancinsa zuwa arewacinsa cikin hauka. A Khan-Yunus ‘yan Sahayoniyar sun...
Ɗan wasan Manchester United, Leny Yoro da Matthijs de Ligt da kuma Ayden Heaven ba suyi atisaye ba, bayan da ƙungiyar ke shirin buga wasan karshe a Europa League da Tottenham a makon gobe. Ranar Juma’a United za ta je Stamford Bridge domin karawa da Chelsea a Premier, amma dai hankalinta yana wasan da za ta kara ranar Laraba a birnin Bilbao. Yoro ya ji rauni ranar Lahadi a wasan da West Ham ta doke United 2-0, shi kuwa De Light a wasan Brentford ya ji rauni. Shi kuwa Heaven ya yi atisaye shi kaɗai, sai dai Jonny Evans da Toby Collyer sun yi atisaye tare da ƴan wasan United. Diogo Dalot ya motsa jiki shi kaɗai, wanda ke fatan...
Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga hukumomin gwamnati da shugabannin makarantu da su ba da fifiko wajen kula da duk wasu gine-ginen makarantu da aka gyara domin kiyaye abubuwan da kuma tabbatar da ci gaban fannin ilimi. Gwamna Dauda Lawal ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake kaddamar da sabuwar makarantar sakandaren Larabci ta mata ta gwamnati da aka gyara tare da inganta ta a garin Gusau. Ya bayyana cewa, aikin sauran makarantun da ake gudanarwa a fadin jihar, wani bangare ne na kokarin gwamnatinsa na farfado da tsarin makarantun kwana, tare da karfafa tsaro domin kare makarantu da kewayen su. A cewar Gwamna Lawal, inganta kayan aikin makarantu na da matukar muhimmanci wajen...
Kashi na biyu na maniyyata 415 daga jihar Kwara sun tashi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025. Da yake jawabi ga maniyyatan jihar kafin tafiyarsu, Amirul-Hajj na Jiha, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Ismail Yahaya- Alebiosu ya shawarce su da su kasance jakadu nagari na jihar yayin da suke kasar Saudiyya. Oba Yahaya- Alebiosu ya ce gwamnatin jihar ta samar da matakai daban-daban don tabbatar da annashuwa da kare lafiyar alhazai a tafiyar da suke yi a kasa mai tsarki. Mai baiwa gwamnan jihar Kwara shawara ta musamman kan harkokin addini, Alhaji Ibrahim Dan-Maigoro ya jagoranci tawagar maniyyata guda 415 zuwa kasar Saudiyya. An dauke Mahajjatan ne a jirgin Max Airline daga filin...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da jirgin farko na maniyyatan jihar Kano da ke niyyar gudanar da aikin hajjin bana. Gwamna Abba Kabir Yusif, wanda ya samu wakilcin mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya bukaci maniyyatan da su kasance jakadu na gari a jihar, su kuma yi addu’ar zaman lafiya, ci gaba, da hadin kan jihar Kano da Nijeriya baki daya. Ya jaddada kudirin gwamnati na tallafa wa duk maniyyata a duk tsawon zamansu a kasa mai tsarki. Tun da farko, Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II, ya shawarci alhazai da su kwantar da hankulansu, su kuma maida hankali wajen gudanar da ibada. A nasa jawabin babban daraktan hukumar jin dadin...
Majalisar dokokin jihar Kaduna ta amince da dokar hukumar kula da manyan makarantu ta jihar Kaduna, ta shekarar 2025, ya zama doka. Dokar dai na da nufin daidaita harkokin gudanar da manyan makarantun sakandire a fadin jihar domin daidaita tsarin ilimin zamani. Da yake jagorantar zaman majalissar, mataimakin kakakin majalisar Mista Henry Magaji Danjuma ya bayyana cewa sabuwar dokar za ta inganta yadda ake gudanar da manyan makarantun sakandire a jihar. Kudirin dokar ya biyo bayan gabatar da rahoton Barr. Mahmud Lawal Isma’ila, shugaban kwamitin hadin gwiwa kan ilimi da shari’a, kuma wakilin mazabar birnin Zaria. Ya bayyana cewa dokar ta zama dole ne ta hanyar gyare-gyaren nan a tsarin ilimin Najeriya. “A da, mun gudanar da...
Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta kammala shirye-shiryen kaddamar da wani shiri na sana’ar kiwon dabbobi da ya maida hankali kan matasa, wanda aka tsara domin horarwa da samar da kayan aiki da kuma samar da kudade ga masu son noma a fadin jihar. Kwamishiniyar Raya Dabbobi ta jihar, Misis Oloruntoyosi Thomas ta bayyana haka a lokacin da ta ziyarci sansanin wayar da kan matasa masu yi wa kasa hidima (NYSC) da ke Yikpata, karamar hukumar Edu ta jihar. Ta ce shirin wani bangare ne na kokarin da Gwamnatin Jihar ke yi na mayar da jihar ta zama wata matattarar kirkire-kirkire da kuma dabbobi. Kwamishinan ya bayyana cewa, ma’aikatar ta hada kai da hukumar NYSC domin samar...
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta hada kai da tsangayar sadarwa ta Jami’ar Bayero Kano, domin bayar da takardar shaidar difloma ga masu amfani da shafukan sada zumunta da ke da hannu wajen tallata manufofin Gwamna Abba Kabir Yusuf. Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana hakan a karshen taron yini biyu da aka gudanar a Kano. Kwamared Waiya ya ce horon na da nufin inganta yadda mahalarta taron ke amfani da kafafen sada zumunta wajen musayar bayanai da suka shafi ayyukan gwamnati. “Kwas din diflomasiyyar da aka gabatar zai inganta karfin mahalarta don yin amfani da dandamali na kafofin watsa labarun yadda ya kamata wajen yada bayanai kan manufofi...
Ɗaliban da suka rubuta jarabawar shiga jami’a (UTME) na shekarar 2025 da Hukumar Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta gudanar sun buƙaci a soke sakamakon ɗungurungum. Ɗaliban sun bayyana haka ne bayan da Hukumar JAMB ta amsa laifin kurakurai da aka samu da suka haifar da yawan rashin ƙoƙarin ɗalibai a jarabawar. Rashin kyawun sakamakon jarabawar, wadda sama da ɗalibai miliyan 1.5 suka kasa samun mako 200 ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya. A yayin da wasu suka ɗora laifin a kan matsalar na’ura, wasu kuma sun zargi rashin kyakkyawan shiri da kuma rashin iya kula da lokaci daga ɓanagaren dalibai. NAJERIYA A YAU: Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Ɗalibai A Jarabawa JAMB ta ɗauki alhakin faɗuwar ɗalibai...
Jagoran juyin juyala halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae, ya zargi kasashen yamma da goyon bayan kissan kare dangin da ke faruwa a gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda yake ganawa da wadanda suka shirya taro na farko don tunawa da likitoci shahidar a yanki mai tsarki na shekaru 8 tsakanin Sadam Hussain na kasar Iraqi wanda yake samun goyon bayan manya manyan kasashen duniya a lokacin da kuma jaririyar JMI a lokacin. Jagoran ya yi tir da dukkan yake yaken da kasashen yamma suke tallafawa a yammacin Asiya daga ciki har da yakin Gaza, inda HKI wacce take samun goyon bayan manya-manyan kasashen...

Shugaban Hukumar Makamin Nukliya Ta Kasar Iran Yace, Kasarsa Bata Buye Wani Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba
Shugaban hukumar Makamashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa kasarsa bata boye wani wuri inda take sarrafa makamashin Nukliya wanda bata fadawa hukumar IAEA ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Islami yana fadar haka a jiya Laraba, kuma don kare matsayin Iran na mallakar fasahar nukliya ta zama lafiya, wanda kasashen yamma suke zarginta da kokarin kere makaman nukliya. Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ya bayyana haka ne a gefen taro Makamashin Nukliya na kasar Iran karo na 31 wanda aka gudanar a nan birnin Tehran, ya kuma kara da cewa babu wata cibiyar sarrafa makamashin nukliya wanda Iran ta boyewa hukumar IAEA a da ko yanzu. Kuma da akwai...

Iran Da Kasashen Turai uku wato E3 Zasu Bude Tattaunawa A Tsakaninsu A Birnin Istambul A Gobe Jumma’a
Manya-Manyan Jami’an gwamnatin kasar Iran da tokwarorinsu na kasashen turai uku wadanda ake kira, E3 zasu fara tattaunawa a tsakaninsu dangane da tattaunawa dangane da makamashin nukliya tsakanin Iran da Amurka wanda ke ci gaba a halin yanzu. Kasashen E3 dai sun hhada da Faransa, Jamus da kuma Ingila wadanda suke sanyawa yarjeniyar JCPOA hannu a shekara ta 2015. Manufar taron ko kuma tuntubar juna tsakanin Iran da wadannan kasashe uku itace sanyasu a kan hanya kan yadda tattaunawar take tafiya, da kuma yadda ake son a gabatar da sauye-sauye wa yarjeniyar JCPOA, tunda Amurka ta waresu daga wannan tattaunawar. JMI tana ganin idan har an cimma wata yarjeniya da Amurka kan shirinta na makamashin nukliya ba zai bambanta sosai...

Wata Kotu A Amurka Ta Bukaci A Saki Wani Malami Mai Goyon Bayan Palasdinawa A Jami’ar Georgetown academic
A wata koma baya ga shirin gwamnatin Trump na dirar mikiya a kan Amurkawa magoya bayan Falasdinawa a Jami’o’iin Amurka, wata kotu ta kare hakkin bil\adama ya yanke hukuncin sallamar Dr. Khan Suri malami a Jami’ar Georgetown ta Amurka wanda jami’an tsaro na shige-da fice suka kama a cikin makonnin da suka gabata saboda jawabin da yayi a taron gangami na goyon bayan Falasdinawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kotun ta gwamnatin tarayya ta bukaci jami’an custom da kuma shige da fice na AMurka (ICE) suka sake Dr Khan Suri daga inda suke tsare da shi makonni 8 da suka gabata, ya koma Texas inda yake zama tare da iyalansa, daga Viginia inda ake tsare da...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da zargin da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayiwa JMI a lokacinda yake ziyarar aiki a birnin Riyar na kasar Saudiya a ranar talatan da ta gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Laraba ta kuma kara da cewa zargin da shugaba Trump yakewa JMI na kokarin wargaza tsarin zamantakewa a yankin Asiya da yamma ba gaskiya bane, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurka ne suke son dagula al-amura a yankin tare da goyon baya HKI ta kashe mutanen yankin a gaza da lebanonm da kuma siriya. Inda a gaza kadai ya zuwa yanzu ta kashe Falasdinawa fiye dubu 52.
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta yi amai ta lashe. Bayan ta musanta duk zarge-zargen da aka yi cewa tana da hannu a rashin kyawun sakamakon jarabawar da ta shirya, shugaban hukumar ya fito ya amsa laifin. Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce dalibai 379,997 abin ya shafa, kuma hukumar za ta sake shirya musu wata jarabawar. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan dalilan Hukumar ta JAMB. Domin sauke shirin, latsa nan
Ya ƙaryata zargin cewa an ci zarafin waɗanda ake zargin, yana mai cewa an bi doka da ƙa’idoji na ƙasa da na duniya a duk matakan binciken da aka gudanar. Ya ƙara da cewa bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta an shirya shi ne domin yaudarar jama’a da neman tausayi tare da ɓata suna da amincin rundunar. Nguroje ya yi gargaɗi game da yaɗa labaran ƙarya da ka iya janyo cikas ga binciken da ake yi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista
Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tinubu tana da ƙudirin kare ’yancin faɗin albarkacin baki da ’yancin kafafen yaɗa labarai, waɗanda ya ce su ne ginshiƙan dimokiraɗiyya a ƙasar nan. Ya ce: “Na bayyana ra’ayi na ga Jakaden, kuma na kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da kare ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma rashin takura wa ‘yan jarida wajen gudanar da aikin su. Za mu ci gaba da kare wannan. “Muna ganin aikin jarida da kafafen yaɗa labarai wani muhimmin ɓangare ne na dimokiraɗiyya. “Babu wata dimokiraɗiyya da za ta yi nasara ba tare da kafafen yaɗa labarai ba.” Sai dai kuma ministan ya buƙaci ‘yan jarida da su riƙa amfani da ‘yancin da suka...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya ce Najeriya ba za ta sake komawa mulkin soja ba. Ya bayyana haka ne a Babban Birnin Tarayya, Abuja yayin ƙaddamar da littafi mai suna “Military Factor in Nigerian History, 1960-2018”, domin murnar cika shekaru 70 da kafa ƙungiyar Tarihi ta Najeriya (HSN). JAMB ta ɗauki alhakin faɗuwar ɗalibai jarrabawar 2025, ta nemi afuwa Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Gowon ya ce duk da irin gudunmawar da sojoji suka bayar a tarihin Najeriya, musamman a lokacin yaƙin basasa da kuma samar da ababen more rayuwa bai kamata su sake tsoma baki a siyasa ba. Ya jaddada cewa dimokuraɗiyya, duk da kurakuran da ake...
Kasar Sin ta zage damtse kan wannan aiki inda ta kuduri aniyar yin ginin tashar da kayan da aka sarrafa da albarkatun duniyar wata, tare da tabbatar da cewa suna da ingancin da za a iya dogaro da su. Wannan zai zama ta harbi tsuntsu biyu da dutse guda, na farko zai saukaka sufurin jigila da kuma kula da gyaran tashar yadda ya kamata. Babban jagoran tsara aikin binciken duniyar watan, Wu Weiren ya ce kasar Sin ita ce ta farko a duniya da ta kera injin buga tubali ko bulon gini na kasar duniyar wata ta hanyar amfani da kayan aiki da aka sarrafa daga albarkatun duniyar watan. Injin yana aiki ne ta hanyar janyo makamashin hasken rana tare...
Ministan harkokin wajen Iran ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da Iran Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Amurka ita ce ta kawo cikas ga ci gaban al’ummar Iran ta hanyar kakaba takunkumai, matsin lamba da kuma barazanar soji da ba na soji ba, don haka ne Amurka ke haddasa matsalolin tattalin arzikin Iran. A gefen taron majalisar ministocin a yau Laraba, Araqchi ya bayyana cewa, abin da Trump ya fada game da kasashen yankin da suke son bin hanyar samun ci gaba da wadata shi ne, a hakikanin gaskiya irin tafarkin da al’ummar Iran suka bi a lokacin juyin juya halinsu, da kuma tafarkin da suka zaba na...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Jaddada Bukatar Hukunta Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya yi kira da a kakaba takunkumi ga gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma kafa ‘yantacciyar kasar Falasdinu Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Muhammad Baqir Qalibaf ya yi kira ga kasashen musulmi da su kakaba takunkumin siyasa da tattalin arziki da na soji kan gwamnatin yahudawan sahayoniyya domin kawo karshen kisan kiyashin da take yi a Gaza. Ya yi kira da a kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta kuma Qudus a matsayin babban birninta tare da baiwa Falasdinawa ‘yan gudun hijira ‘yancin komawa kasarsu ta gado. Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana hakan ne a yau Laraba, yana mai jaddada cewa: A yau, tsarin rayuwa da tattalin arzikin gwamnatin...
Bukatun da shugaban Amurka ya fara gabatarwa shugaban gwamnatin Siriya al-Julani a gamuwarsu ta farko Fadar shugabanci ta Amurka White House ta bayyana cikakken bayani kan ganawar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi da shugaban gwamnatin rikon kwarya ta Siriya, Ali al-Julani, a birnin Riyadh fadar mulkin kasar Saudiyya a ranar Laraba. A cikin wata sanarwa da fadar White House ta fitar ta ce: Trump ya karfafa al-Julani da yin abin da ya bayyana a matsayin wani babban aiki ga al’ummar Siriya, wato sanya hannu kan yarjejeniyar kyautata alakar jakadanci da gwamnatin yahudawan sahayoniyya, a karkashin tsarin da kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da Morocco suka kulla alaka da gwamnatin mamayar Isra’ila a shekara ta 2020. Trump ya kuma...
Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Jigawa ta naɗa Kwamared Sani Muhammad Gumel da Kwamared Usman Mohammed Usman a matsayin mambobin majalisar kungiyar na musamman (Ex-Officio). Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatariyar ta kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed, ta sanya wa hannu kuma ta rabawa manema labarai a Dutse. Ta bayyana cewa, an yi waɗannan naɗe-naɗen ne a matsayin girmamawa da yabo ga jajircewarsu, ƙwarewa, da kuma gudummawar da suke bayarwa wajen haɓaka aikin jarida a Jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya. Aisha Abba Ahmed ta ƙara da cewa, duka waɗannan mutane biyu sun dade suna nuna ƙwazo da biyayya ga manufofi da burin ƙungiyar. Ta ce, ana sa ran waɗannan mambobin na...
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, kasar za ta kara inganta kula da duk wani abu mai nasaba da sarrafawa ko samarwa a bangaren ma’adanan kasa masu matukar muhimmanci, don hana fitarwa ba bisa ka’ida ba, da kuma kiyaye tsaron kasa. Mai magana da yawun ma’aikatar wanda ya bayyana haka a yau Laraba, ya ce, karfafa yadda ake kula da fitar da albarkatun ma’adanai masu muhimmanci zuwa ketare yana da muhimmanci ga tsaron kasa da muradun ci gaba. Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe JAMB: Tangarɗar Na’ura Ne Ya Haifar Da Gagarumar Koma Baya A Sakamakon UTME Na 2025 A ranar Litinin da ta gabata ne, wani taron kasa da aka...
A hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila kai kan yankunan Zirin Gaza a cikin dare daya sun kashe Falasdinawa 51 Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai kan arewaci da kudancin zirin Gaza tun daga tsakiyar daren Laraba ya kai Falasdinawa 51, ciki har da 45 a arewacin zirin Gaza. Wannan sabon tashin hankalin na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke gudanar da ziyarar aiki a yankin gabas ta tsakiya. Kamfanin dillancin labaran Falasdinawan “WAFA” ya watsa rahoton cewa: Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren bama-bamai da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a kudanci da arewacin zirin Gaza...
Idris ya ce: “Wannan ba kawai ƙaddamar da littafi ba ne, amma bikin rayuwa da jarumtaka, daidaito, da jajircewa ga tsarin dimokiraɗiyya suka bayyana. “Ko da yake Alhaji Sule Lamiɗo babban jigo ne a jam’iyyar adawa kuma sau da dama mai suka ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR), har yanzu yana daga cikin manyan ginshiƙai na cigaban siyasar Nijeriya.” Ministan ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya yarda da siyasar da ke bai wa kowa dama, inda ake maraba da ra’ayoyi mabanbanta, kuma suna da muhimmanci ga tattaunawa kan makomar ƙasa. “Kowane ɗan ƙasa, ba tare da la’akari da dangantakar sa da jam’iyya ba, yana da gurbin zama a teburin tattaunawa kan makomar ƙasa.” Idris...

Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya
Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean wato CCF, tare da ba da muhimmin jawabi. Inda Xi ya sanar da cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasashen Latin Amurka da Caribbean wajen fara gudanar da manyan ayyuka guda biyar, domin neman ci gaba da farfadowa tare, da kuma raya makomar al’umma ta bai daya. Masana sun bayyana cewa, jawabin da ya yi, ya kunshi shirin raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean, tare da ba da jagoranci kan aikin. Ban da haka kuma, yayin taron na wannan karo, an zartar da “Sanarwar Beijing”, da “Shirin...
Shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewar an samu kura-kurai a sakamakon jarrabawar UTME ta shekarar 2025 da aka saki kwanan nan. A yayin wani taron manema labarai a Abuja, Farfesa Oloyede, ya fashe da kuka yayin da yake bai wa ɗalibai haƙuri, inda ya nuna nadamarsa kan wahalar da suka sha. Mutum 2 sun shiga hannu zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Gombe ’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara A cewar JAMB, matsalolin fasaha sun shafi sakamakon ɗalibai 379,997. Waɗannan matsaloli sun fi shafar jihohin Kudu maso Gabas da kuma Jihar Legas. A Legas, ɗalibai 206,610 daga cibiyoyi 65 ne suka fuskanci matsalar, yayin da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta cafke wasu maza biyu bisa zargin yi wa ƙananan yara mata fyaɗe a lokuta daban-daban a jihar. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce sun kama wani mutum mai shekara 47, da zargin yi wa ‘yar matarsa mai shekara biyu fyaɗe a Tudun Wada, Shamaki a ranar 5 ga watan Mayu. ’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Bayan samun rahoton daga matarsa, rundunar ’yan sandan ta garzaya gidansu inda ta kama wanda ake zargin, sannan suka kai yarinyar Asibitin Ƙwararru na Gombe domin duba lafiyarts. Ya ce...
Oloyede, wanda ya bayyana tangardar a matsayin “zagon kasa” ga shirin jarabawar UTME ta 2025, ya ce, wadanda abin ya shafa za su fara samun sako a wayar salularsu daga Hukumar daga ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025. Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME ta shekarar 2025, sama da miliyan 1.5 aka bayar da rahoton, sun samu maki kasa da 200 daga cikin mafi girman maki 400, lamarin da ya haifar da damuwa a bangaren ilimi na kasar. UTME ta wannan shekara, ta gamu da koma baya sosai, wanda ya haifar da damuwa tsakanin ɗalibai, iyaye, da malamai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo Ya ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani ƙauye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, ’yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su. Ya kuma ruwaito yadda wani yaro mai fama da cutar farfaɗiya ya mutu bayan...
Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo Ya ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani ƙauye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, ’yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su. Ya kuma ruwaito yadda wani yaro mai fama da cutar farfaɗiya ya mutu bayan...
Tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa da shi da Sule Lamido har yanzu suna kan kujerar mulki, da sun fito ƙarara sun ƙalubalanci Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Amaechi ya bayyana haka ne a wajen ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Sule Lamido mai suna ‘Being True to Myself’ da aka gudanar a Abuja. Ko yanzu aka yi zaɓe Tinubu ne zai yi nasara — Oshiomhole DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya “Da mun fito da ƙarfinmu, mun ƙalubalanci gwamnati, mun kalubalanci shugaban ƙasa,” in ji Amaechi. “Haka muka saba a lokacin muna Gwamnoni. Muna da kishin ƙasa da ƙwarin gwiwar sauya al’amura.” Ya bayyana yadda dangantakar siyasar da ke tsakaninsa da Lamido, inda ya ce duk...
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce zuba jarin Euro miliyan dari da goma sha ɗaya da tayi akan aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani zai rage cunkoson ababen hawa da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar. Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka da Ababen More Rayuwa ta Jihar Kaduna, Ibrahim Hamza, ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki kan aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani wato BRT da aka gudanar a Kaduna. Aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani yana da nufin inganta zirga-zirgar ababen hawa a birane, rage cunkoso, da kuma inganta rayuwar jama’ar Jihar Kaduna. Kwamishina Ma’aikatar Aiyyuka da Ababen More Rayuwa, Ibrahim Hamza ya tabbatar da kudurin gwamnati na sauya...
Tsohon Shugaban APC na ƙasa, Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa ko yau aka yi zaɓe, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai yi nasara. Oshiomhole wanda shi ne mai wakiltar shiyyar Edo ta Arewa a Majalisar Dattawan Nijeriya ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da gidan talabijin na Channels a safiyar wannan Larabar. DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Majalisar Dattawa ta buƙaci a tura ƙarin sojoji zuwa Borno da Yobe Tsohon gwamnan na Jihar Edo ya faɗi hakan a lokacin da yake tsokaci kan sauya sheƙar da Sanatocin Kebbi uku suka yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Ya ce, Tinubu ya ɗauki ƙwararan matakai domin daidaita Nijeriya, yana mai cewa kafin gwamnatinsa manoma a wasu sassan ƙasar...
Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta bukaci Gwamnatin Jiha da kananan hukumomin jihar goma sha uku da su gaggauta bayar da kayayyakin tallafi ga wadanda guguwar iska ta shafa a fadin jihar. Majalisar ta bayyana cewa hakan na da muhimmanci domin inganta rayuwar wadanda abin ya shafa da rage musu radadin halin da suke ciki. Shugaban Majalisar, Dr. Danladi Jatau, ne ya bayyana hakan bayan Hon. Hudu A Hudu ya gabatar da batun a matsayin lamari mai muhimmanci ga jama’a, yayin zaman majalisar da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar. Shugaban majalisar ya ce abin jimami ne kwarai yadda guguwar iska ta lalata gidaje, makarantu, gine-gine da wasu muhimman kayayyaki da suka kai daruruwan miliyoyin Naira tare da jikkata mutane...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karba-karba wani tsari ne da ya tanadi kewayarwar ludayi a tsakanin kudanci da arewacin Najeriya wajen rike shugabancin kasa. Manufar tsarin, wanda babu shi a Kundin Dokokin Najeriya, ita ce tabbatar da daidaito da haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa. Sai dai yunkurin samar wa tsarin mazauni ta yadda shugabanci zai riƙa kewaya a tsakanin shiyyoyi shida na kasar nan bai samu shiga ba a Majalisar Wakilai. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan wannan tsari na karba-karba da tasirinsa. Domin sauke shirin, latsa nan
Masana sun ce wannan mataki zai iya sauya tsarin kasuwanci da ci gaban fasaha a duniya, musamman a yankin Larabawa. Bayan kammala taron a Saudiyya, ana sa ran zai wuce Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin ci gaba da tattaunawa da shugabannin yankin kan batutuwan tsaro da haɗin gwiwar tattalin arziƙi. Yarjejeniyar ta samu karɓuwa daga ɓangarorin da dama, inda wasu ke ganin hakan zai ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman wajen yaƙi da ta’addanci da bunƙasa fasahar zamani. Sai dai wasu na nuna damuwa kan yawan makaman da Saudiyya ke saye daga Amurka, suna mai cewa hakan na iya ƙara tsananta rikice-rikice a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
A jiya Talata sojojin HKI su ka kai wani mummunan hari akan asibitin Gaza na “Turai” da kuma zagayensa da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da kuma jikkata wasu da dama. Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama wajen kai wadannan munanan hare-haren akan Asibitin da ake kir ana turai, da kuma gefensa a kudu maso gabashin birnin Khan-Yunus. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; jiragen saman na HKI sun kai hare-haren ne ta hanyar harba makamai masu linzami akan bangare da kuma kula da matsalolin gaggawa na asibitin da kuma bangaren dake kula da asibitin da gyara abubuwan da su ka baci. Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wasu hare-haren a...
Rahoton MDD ya sanar da cewa, fiye da mutane 48,000 ne, ambaliyar ruwan saman da aka yi a Somaliya ya yi wa illa, yayin da wasu da adadinsu ya kai 17 su ka rasa rayukansu. Hukumar MDD mai kula da ayyukan jin kai da cewa ( OCHA) ce ta sanar da hakan,tana mai kara da cewa da akwai yiyuwar a kara samun saukar mamakon ruwa sama a tsakiyar kasar, nan da wasu kwanaki masu zuwa. Wannan ambaliyar dai wacce ta shammaci mutanen kasar, a lokacin da kungiyar agajin kasar ta sanar da cewa, tana da karancin kayan da ake da bukatuwa da su domin kai daukin gaggawa idan hakan ta faru. Kasar Somaliya ta fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani a...
A yau Laraba ne dai shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf ya birnin Jakarta na kasar Indonesia, da zummar halartar taron wakilan majalisun kasashen da suke mambobi a kungiyar kasashen musulmi. Taron na wannan karon a kasar Indonesia shi ne karo na 19 da kungiyar ta kasashen musulmi take yi a matakin wakilan majalisun, kasashe mambobi. An bude taron ne dai daga jiya Talata 13 ga watan Mayu, zai kuma ci gaba har zuwa ranar 15 gare shi. Tun a jiya ne dai wakilan Iran su 4 daga majalisar shawarar musulunci ta kasar su ka isa birnin na Jakarta domin halartar taron.
Rundunar “Sarayal-Kudus” ta kungiyar jihadul-Islami ta harba makamai masu linzami akan sansanonin ‘yan share wuri zauna na “Asqalan” da “Ushdud”. A jiya Talata ne dai rundunar ta Sarayal-Qudus’ ta sanar da harba makamai masu linzamin kaan sansanonin ‘yan share wuri zauna, a matsayin ci gaba da mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin na HKI akan al’ummar Falasdinu. Sanarwar da rundunar ta fitar ta kunshi cewa: Harin nata yana a matsayin mayar da martani ne akan kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu a Gaza. A wani labarin na daban, rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas ta sanar da cewa ta yi taho-mu-gama da sojojin mamaya a unguwar “Shuja’iyya” dake gabashin birnin Gaza. Sojojin HKI suna ci...
Gwamnatin jihar Kwara ta shirya wani gagarumin horo ga likitocin kiwon lafiya a fadin cibiyoyin kiwon lafiya na jihar kan yadda za a shawo kan cutar zazzabin cizon sauro. Da yake sanar da bude horon a Ilorin, daraktan kula da lafiyar jama’a na jihar, Dokta Oluwatosin Fakayode, ya jadadda bukatar gaggawar gano cutar da wuri da kuma gaggauta magance cutar zazzabin cizon sauro, musamman a cikin mutane masu rauni kamar yara ‘yan kasa da shekaru biyar da mata masu juna biyu. A cewarsa shirin ya kasance wani bangare na faffadan kokarin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a jihar, gami da shirye-shiryen yakin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na 2025 (SMC). Dokta Fakayode ya bayyana cewa horon...
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta baiwa mutane 311 tallafi a karkashin shirin tallafa wa mata da matasa kan harkokin noma da nufin bunkasa dogaro da kai da ’yancin tattalin arziki a fadin jihar. Da take jawabi a yayin kaddamar da gagarumin bikin a Gusau, babban birnin jihar, Hajiya Huriyya ta jaddada kudirinta na gwamnati na bunkasa sabbin manoma, ‘yan kasuwa, da matasa da suka samar da su don kawo sauyi a fannin noma. Ta bayyana cewa daga cikin 311 da suka ci gajiyar tallafin, 201 mata ne yayin da 110 kuma samari ne, wadanda dukkansu za su samu cikakken goyon baya a karkashin shirin. “Kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai samu jarin...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umurci shugabannin kananan hukumomin jihar 44 da su tabbatar da cewa Kansilolinsu sun shiga dukkan ayyukan da aka gudanar a kananan hukumominsu . Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da kansilolin kananan hukumomi 484 daga kananan hukumomi 44 na jihar. Taron wanda ya gudana a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati, da nufin karfafa alaka tsakanin gwamnatin jihar da majalisun kananan hukumomi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatin sa tana da hankali kuma ba ta da almundahana, kuma ba za a amince da duk wani nau’i na almundahana ba. Ya kuma bukaci kansilolin da su yi aiki tukuru don ganin sun rike amanar...
Majalisar Dattawa ta buƙaci rundunar sojin Nijeriya ta tura ƙarin sojoji da manyan makaman yaƙi zuwa jihohin Borno da Yobe, bayan farfaɗowar hare-haren ‘yan ta’adda na Boko Haram a jihohin. Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin ƙasar, ciki har da kashe kimanin sojoji goma a garin Marte da ke ƙaramar hukumar Monguno ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, da kuma wani harin da suka kai Gajiram na Ƙaramar Hukumar Nganzai, da sanyin safiyar ranar Talata. Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo Trump ya janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria A wani ƙuduri da mai tsawatarwa majalisar, Sanata Tahir Munguno, ya gabatar a ranar Talata,...
A yanzu haka ana zargin wasu dakarun sojin sun ɓace tun bayan kai harin na ranar Litinin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo, ya musanta dalilin da tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar a littafinsa dangane da soke zaɓen 1993. Tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriyar ya ce dalilin da IBB ya bayar cewa shi ne abin da ya sa ya rushe zaɓen 1993, “ba gaskiya” ba ne. Janar Babangida a littafinsa mai suna “A Journey in Service” ya yi zargin cewa marigayi Janar Sani Abacha ne ke da alhakin rushe Zaɓen 12 ga watan Yunin 1993. Trump ya janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria ‘Duk da hauhawar farashi tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka’ Alhaji Sule Lamido ya faɗi hakan ne a littafin tarihinsa da ya rubuta mai suna “Being True to...
Babban kwamadn dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ko (IRGC) Manjo Janar Hussain Salami ya bayyana cewa dakarun kare juyin jya halin musulunci a nan Iran a shirye suke don fuskantar duk wani kuskureb da makiya zasu yin a kawowa kasar Hare-hare. Janar Salami ya bayyana haka ne a jiya Talata a lokacinda yake wani Jawabi a birnin Mashad na arewa maso gabacin kasar Iran. Janar Salami yana wannan maganane bayan da shugaban kasar Amurka Dunal Trump wanda yake ziyarar wasu kasashen larabawa a yankin yammacin Asiya, na cewa idan an kasa cimma dai-daito tsakanin Iran da Amurka a tattaunawa kan shirinta na makashin nukliya to Iran ta shiryawa yaki. Salami ya kara da cewa sun san...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai dagewa kasar Siriya dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata, kuma zai gana da shugaban gwamnatin riko na kasar Ahmad Sharaa wanda aka fi sani da Julani. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a wata tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar Saudiya a birnin Riyad na kasar Saudiya, inda ya fara ziyarar aiki a can tun jiya Talata. Shugaban ya kara da cewa: A yanzu lokaci yayi da mutanen kasar Siriya zasu huta, don zamu dauke dukkan takunkuman da muka dorawa kasar Siriya. Saboda zata samar da huldar Jakadanci da HKI kuma babu wata cuta da zata sami kasar daga Siriya. Wannan yana zuwa...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan na farko Hiroyuki Namazu a nan birnin Tehran a jiya Talata inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran da suka shafi kasashen biyu na harkokin kasuwanci da kuma wasu bangarori, sannan tare da tattauna irin sauye-sauyen da ake samu a yankin da kuma abinda ya zama lazimi ga kasashen biyu su yi a wannan halin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasashen biyu sun kara jaddada bukatar kasashen su karfafa dangantaka da ke tsakaninsu. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan ya fada a taron kwamitin hadin guiwa na kasashen biyu kan cewa kasar Japan ta zabi zurfafa dangantaka da kasar Iran...
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa karfin bangaren sojojin tabbatar da zaman lafiya na majalisar a duniya, yana dai dai da karfin dukkan kasashen da suke bawa kudaden da ake tafiyar da ayyukansu ne. Don haka ya bukaci kasashen da basu biya rabonsu na kudade karo-karon da ake yi don tafiyar da ayyulan zaman lafiya a duniya bas u yi hakan da gaggawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto babban sakataren yana fadar haka a jiya talata ya kuma kara da cewa a halin yanzu majalisar tana tafiyar da ayyukan zaman lafiya har 11 a kasashen duniya wadanda suka hana da nahiyar Afirka Asia da kuma turai. Guterres ya kara da cewa majalisar tana da...
Ya ce, “Samar da motocin aiki ga jami’an tsaron zai bayar da ci gaba wajen sawwaƙa masu zirga-zirga, kai ɗauki a kan lokaci da ƙara ƙarfafa masu gwiwa wajen samar da tsaro da bin doka da oda. “Wannan taro na yau, wani ci gaba ne na ƙoƙarin gwamnatina wajen ƙarfagawa, tare da inganta ayyukan jami’an tsaron da ke aiki a duk faɗin jihar. “Wannan kuma yana ɗamfare ne da alƙawuran da muka yi, tare da jajircewar mu wajen samar da duk abin da za mu iya don tunkarar dukkan nau’o’in rashin tsaro, samar da zaman lafiya, kare rayuka da dukiyar jama’ar jihar mu. “Wannan ƙoƙari namu yana ƙara nuna hobbasan gwamnatin mu wajen ƙarfafa wa jami’an tsaron mu don...
Babu wata ’yantacciyar kasa da za ta hakura da muradunta domin wata ta biya bukatunta na son rai. Yayin da Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kasashe haraje-harajen kwastam na babu gaira ba dalili, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kin amincewa da salon cin zali, inda ta sha nanata cewa, sai ta ga abun da ya ture wa buzu nadi, a yakin cinikayya da Amurkar ta tayar. Lallai tsayuwar kasar Sin ya ba kasashe masu tasowa kwarin gwiwa, kuma ya nuna cewa, lokaci ya wuce da za a rika yi wa ’yantattun kasashe danniya da cin zali domin biyan bukatu na kashin kai. Hakika kasar Sin ta gina tubali mai karfi da ta dora tattalin arzikinta a...

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaba Donald Trump ya sanar da janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria. Trump ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ƙarin haske kan wannan matsaya a birnin Riyadh na Saudiyya inda yake ziyarar aiki. ‘Duk da hauhawar farashi tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka’ HOTUNA: Trump na ziyara a Saudiyya Trump ya ce zai bai wa Syria damar tsayawa da ƙafafunta, bayan buƙatar gaggawa da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman ya miƙa. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Trump ya soma yada zango a Saudiyya a rangadin kwanaki huɗu da yake yi a ƙasashen Gabas ta Tsakiya. Trump ya ɗauki matakin da ya ba wa kowa mamaki na janye takunkumin da Amurka...
Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi kira ga rundunar sojin Nijeriya da ta gaggauta tura jami’anta da sabbin kayan yaki na zamani zuwa jihohin Borno da Yobe sakamakon sabon hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a yankin. An yi wannan kiran ne biyo bayan sabbin hare-haren ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, ciki har da kashe sojoji sama da 10 a garin Marte da ke karamar hukumar Monguno ta jihar Borno, a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu. Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya ‘Yan ta’addan sun kuma sake kai wani hari da sanyin safiyar Talata a Gajiram...
Kazalika, shugabannin kasashen biyu sun kuma gana da manema labarai a tare. Bangarorin biyu dai sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan karfafa gina al’ummar Sin da Brazil mai makoma guda domin kara tabbatar da samuwar duniya mai cike da adalci, wacce za ta kasance mai dorewa cikin nagarta, da kara hada karfi da karfe wajen karfafa damawa da sassa daban-daban a sha’anin duniya, tare da ba da sanarwar hadin gwiwa game da rikicin Ukraine. Kafin ganawar dai, shugaba Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, sun shirya bikin maraba ga Lula da uwargidansa a dandalin da ke wajen kofar gabas na babban zauren taron al’umma. (Bilkisu Xin/Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Iran ta yi tir da sabbin takunkuman da ta danganta da na rashin adalci da Amurka ta kakaba mata. Amurka dai ta kakaba wa Iran sabbin takunkuman, ne duk da ci gaba da tattaunawar nukiliyar da ake yi tsakanin kasashen biyu. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ayyana wasu ‘yan kasar Iran guda uku da wani kamfani mai suna Fuya Pars Prospective Technologists, bisa zargin cewa suna da hannu wajen gudanar da bincike da kuma ayyukan da suka shafi makaman nukiliya. Amurka, ta ce takunkumin ya shafi toshe duk wasu kadarori na mutanen a Amurka tare da hana mu’amalar kasuwanci da su. Sabon takunkumin ya zo ne kwana guda bayan Iran da...
A kasar Mali a rushe dukkan jam’iyyun siyasa na kasar a hukumance. bisa ga bukatar shugaban kasa da aka amince da shi a wannan Talata, yayin wani taron majalisar ministocin kasar, an rusa jam’iyyun siyasa a duk fadin kasar. An kuma haramta tarurruka da sauran ayyukan jam’iyyun siyasar da kungiyoyin dake da alaka da siyasa ko kuma su fuskanci takunkumi. Gwamnatin rikon kwarya ta ayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan soke kundin tsarin mulkin jam’iyyun siyasa. Dole ne a samar da sabuwar doka musamman don tafiyar da harkokin siyasar Mali, inji karamin minsitan kula da sauye-sauyen al’amuran siyasa a gidan talabijin na kasar.
Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar a Jabalia da Khan Younis na Falasdinu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren na Isra’ila, yana mai cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa. A yayin da yake bayyana goyon bayansa ga al’ummar Falastinu da ake zalunta, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kakkausar suka kan mummunan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai kan matsugunan ‘yan gudun hijira da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira a Jabalia da Khan Younis, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da kananan...
Bankin Duniya ya sanar da cewa duk da ƙalubalen hauhawar farashin da Nijeriya take fuskanta, tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru a shekarar da ta gabata. Babban bankin ya ce tattalin arzikin Nijeriyar ya samu haɓaka a kusan shekaru goma a 2024, inda a watanni uku na karshen 2024 aka samu haɓaka sosai. HOTUNA: Trump na ziyara a Saudiyya Majalisa ta yi watsi da kudurin dokar mulkin karba-karba Hakan na ƙunshe cikin wani rahoto da babban jami’in tattalin arzaki na Bankin Duniya a Nijeriya, Alex Sienaert, ya fitar ranar Litinin a Abuja. Sienaert ya bayyana cewa tattalin arzikin ya ƙaru da kashi 4.6 a watanni uku na ƙarshen 2024, inda ya kuma yi nuni da cewa zai ci gaba da haɓaka...

Gwamna Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya sake jaddada cewa bikin ya nuna wani muhimmin mataki a ƙoƙarinsa na ƙarfafa wa al’ummar Zamfara masu ƙaramin ƙarfi. “Saboda haka, cikin farin ciki na tsaya a gabanku domin ƙaddamar da wannan muhimmin shiri. “Ya ku jama’a, da baƙi, an tsara wannan shiri ne domin bayar da tallafin kuɗi na Naira 75,000.00 kowanne ga masu cin gajiyar shirin su 448,141. “Kamar yadda Kwamishina Kainuwa ya bayyana a baya, daga cikin adadin da ake sa ran, mutane 279,534 sun cika mafi ƙarancin abin da ake buƙata don karbar Naira 75,000 kowannen su, sauran waɗanda suka ci gajiyar shirin za a tantance su kuma za a ba su nasu da zarar an kammala,...
Shugaban Amurka, Donald Trump ya isa ƙasar Saudiyya a ziyararsa ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya, inda tuni ya sauka a Riyadh a jirgin Air Force One. Shugaban na Amurka ya yi zaman farko da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, kafin su shiga wani zaman sirri. Bom ya kashe jami’an ilimi 2 a Borno Ya kashe abokinsa saboda hula a Kano Trump zai gana ne da Mohammed bin Salman a filin jirgin sama na Sarki Khalid da ke Riyadh a kusa da hotunan wasu daga ckin mambobin iyalan sarauta na Saudiyya Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ma zai kasance a cikin taron. Bayan Saudiyya, Trump dai na shirin kai ziyara ƙasashen Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa daga...
Majalisar Wakilai ta yi watsi da kudurin dokar da ke neman sanya tsarin mulkin karba-karba a tsarin shugabancin Najeriya. Kudurin dokar na neman wajabta yin karba-karbar kujerar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a tsakanin yankunan siyasan Najeriya guda 10.
Jaridar “Telegraph” da ake bugawa a Birtaniya ta buga labarin dake cewa; gwamnatin Benjamine Netanyahu ta bai wa kungiyar leken asiri ta waje, umarnin bin diddigin abubuwan da gwamnatin Amurka take yi a cikin sarari da boye. Rahoton ya kuma kara da cewa; Netanyahu yana kokarin fahimtar abubuwan da gwamnatin Donald Trump take yi ne a boye, kuma menene manufofinta. Da ma a baya, tashar talabijin din “Fox News” ta nakalto tsohon jami’in hukumar leken asirin HKI yana cewa; Donald Trump ya janye taimakon da yake bai wa Tel Aviv. Har ila yau, jami’in na HKi ya ce; Tel Aviv tana cikin kidima saboda dalilai da dama da su ka hada da kasa sanin yadda za ta yi da Yemen.

Batun Zuba Hannun Jari A Amurka Ne Babbar Ajandar Ziyarar Shugaba Donald Trump Zuwa Kasashen Larabawan Yankin Tekun Pasha
A yau Talata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki a karon farko tun da ya zama shugaban kasa. Baya ga kasar Saudiyya shugaban kasar ta Amurka zai kuma kai Ziyara zuwa kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da zummar bunkasa alaka da larabawan yankin tekun Pasha kamar yadda majiyar bangarorin biyu take ambatawa. Bugu da kari, kafafen watsa labarun Amurka sun ce, a yayin wannan ziyarar tashi, shugaban kasar Amurkan, zai yi kokarin samarwa kasarsa hannun jari da kasashen larabawa masu arziki za su zuba. Tun a baya dai Donald Trump ya bukacin ganin Saudiyya kadai ta kara yawan hannun jarinta a cikin Amurka da zai kai dala tiriliyan 1. Kafar watsa...
Wasu ma’aikatan lafiya biyu sun rasu, wasu da dama sun jikkata bayan motarsu ta taka bom a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri a Jihar Borno. Ana zargin mayakan Boko Haram ne suka dasa bom din a wani hari da kungiyar ta kai a kan babbar hanyar a ranar Litinin. Shaidu sun bayyana cewa, wadanda suka mutun suna zaune ne a gaban motar jigilar mangoro, kirar Toyota Hiace da ta dauko su daga Damboa zuwa Maiduguri. Sun kara da cewa tashin bom din ya haifar da sabuwar damuwa game da lafiyar matafiya a kan hanyar. Yadda ISWAP ta kashe sojoji ta kwashe makamai a sansanin soji a Borno ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a Filato Ya kashe abokinsa...
A yau Talata ne dai aka bude taron karawa juna sani karo na 31 a birnin Mashhad wanda shi ne karo na 31 da zai mayar da hankali akan yadda za a ci moriyar wannan fasaha ta fuskokin zaman lafiya. Hukumar makamashin Nukiliya ta Iran ce dai ta tsara wannan taron kara wa juna sanin wanda ya sami halartar masana wannan fage. Wasu batutuwa da za a tattauna a wurin taron sun kunshi; Bututun tace sanadarin Uranium, shi kanshi makamashin da kuma hanyoyin tafiyar da da kula cibiyoyin dake aikin tace da sarrafa makamashin na Nukiliya.
Ya ƙara da cewa dole ne ɗaliban da abin ya shafa su fice daga ɗakunan nan da zarar sun kammala jarrabawar zangon da ake ciki. Jami’ar ta ja hankalin iyaye da ɗalibai da su nemi ɗakunan kwana ne kawai daga cikin jerin waɗanda jami’ar ta amince da su, kamar yadda ofishin Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da Rayuwar Ɗalibai ya wallafa. Ta gargaɗe su cewa ba za ta ɗauki alhakin duk wani abin da zai faru a wajen da ba ta amince da shi ba ba. Haka kuma, jami’ar ta bayyana cewa tana aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an rufe ɗakunan bisa doka da oda. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Idan aka ga tana da tasiri, ana iya tsawaita ko kuma daidaita matakin. Masana tattalin arziƙi sun bayyana cewa wannan ci gaba zai iya taimakawa wajen farfaɗo da cinikayya tsakanin manyan ƙasashen biyu, kuma zai taimaka wa ƙasashe masu tasowa da ke dogara da su wajen kasuwanci da kayan masarufi. Rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China ya fara ne tun daga 2018 lokacin da kowanne ɓangare ke ƙara haraji a kan kayayyakin juna, lamarin da ya haifar da hauhawar farashi da rikicin masana’antu a duniya. Matakin rage harajin da suka ɗauka yanzu na iya zama sabon shafi na fahimtar juna da haɗin gwiwa a tsakanin manyan ƙasashen biyu na duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
“Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici wajen tantance daga inda ɗan takarar PDP zai fito ya janyo rabuwar kai a cikin jam’iyyar, lamarin da ya taimaka wajen rage ƙarfinta a zaɓen 2023. Masana siyasa na ganin wannan gargaɗi na Wike na iya sake haifar da muhawara a jam’iyyar, musamman yayin da ta ke shirin fuskantar babban zaɓen 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Mayaƙan Boko Haram sun kashe sojoji da ba a san adadinsu ba tare da yin awon gaba da wasu da dama bayan wani ƙazamin hari da suka kai a sansanin soji da ke yankin Marte a Jihar Borno. Majiyoyin soji sun ce mayaƙan ƙungiyar sun fi karfin sojojin, inda suka kwashi makamai masu tarin yawa sa’annan suka cinna wa ma’ajiyar makamai da ke sansanin sojin wuta. Mazauna yankin sun bayyana cewa da misalin ƙarfe 3 na asuba, kafin wayewar garin ranar Asabar ne Boko Haram ta ƙaddamar da harin. Wani soja da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce, “ISWAP ta ƙwace Marte, an kashe sojoji da dama, an kama wasu, amma wasu sun samu sun tsere zuwa Dikwa, inda...
Amma sai yanzu gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa a hukumance. Masana tattalin arziƙin sun bayyana cewa kammala biyan wannan bashi wata alama ce ta daidaituwar tsarin kuɗi na ƙasar da kuma yunƙurin rage dogaro da lamuni daga ƙasashen waje. Wasu sun ce hakan na iya ƙara jawo amincewar ƙasashen duniya da hukumomin ba da lamuni ga Nijeriya, musamman idan aka yi la’akari da ƙoƙarin da gwamnatin Bola Tinubu ke yi na farfaɗo da tattalin arziƙi. Wani ƙarin bayani daga ma’aikatar kuɗi ya ce an biya bashin ne a matakai daban-daban tun daga shekarar 2021, kuma an kammala biya a farkon shekarar 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Masarautar Zazzau ta tabbatar da rasuwar Alhaji Ramalan Yero, mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Muktar Ramalan Yero. Sanarwar da ta fito daga bakin Sarkin Fadan Zazzau, Alhaji Abbas Ahmed Fatika, inda ya ce marigayin ya rasu da yammacin ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya. NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar s unguwar Kaura da ke cikin birnin Zariya, a Jihar Kaduna. Masarautar ta aike da ta’aziyyarta ga iyalan mamacin da ɗaukacin al’ummar Jihar Kaduna bisa wannan rashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
An gurfanar da wani mutum a gaban kotun Musulunci kan zargin yi wa matar maƙwabcinsa dukan kawo wuƙa a Jihar Kano. Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun da ke zama a unguwar Kurna Asabe cewa wanda ake zargin ya kuma ji wa matar auren munanan raunuka. Ya yi wa matar wannan aika-aika ne bayan wata taƙaddama, inda ya ji mata munanan raunuka a fuska da wasu sassan jikinta. Alƙalin kotun, Khadi Alhaji Jibrin Ɗanzaki, ya ba da umarnin tsare mutumin a gidan yari sannan ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga watan nan na Mayu. Ya kashe abokinsa saboda hula a Kano Matashi ya kashe saurayin ƙanwarsa a Kano NAJERIYA A YAU: Matsalar lantarki: ’Yan Najeriya sun...