2025-05-20@22:24:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2868
«Magungunan Gargajiya»:
Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa ya zama wajibi ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da yaki da rashin tsaro a kafatanin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Birgediya Janar Mohammad Bello Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 279 ga Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta Najeriya (NURTW reshen jihar Jigawa karkashin shirinta na tallafawa masu sana’o’i. Kwamishinan Muhalli, Sabunta Makamashi da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Nura Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan...
A ziyarar da ya kai jerin kogon Longmen, mai shekaru sama da 1,500 wanda UNESCO ta sanya cikin jerin wuraren tarihi da aka gada na duniya, wanda kuma shi ne ke wakiltar matsayin koli na fasahar sassaka kan dutse ta kasar Sin, shugaban ya bayyana muhimmancin karewa da gado da ma yayata al’adun gargajiya na...
Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta sanar da dakatar da duk wani nau’in tallan magungunan gargajiya a cikin fina-finai, a kan titi ko amfani da lasifika. Wannan na cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, wadda Jami’in Yaɗa Labaran Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya raba wa manema...
Zainab Ishaq Muhammad, wadda aka fi sani da ‘Queen Zeeshaq’ za ta shiga daga ciki a ranar Lahadi mai zuwa. Duk da cewa ba a yayata batun auren ba, Aminiya ta tabbatar da ganin katin gayyata da ke nuna za a ɗaura auren nata da angonta, Hussain Muhammad Koya, a ranar 25 ga watan Mayu,...
Cikakkue bayanai daga baya… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da aikata fashi da makami tare da ƙwato motocin sata guda huɗu, bayan wani samame da suka kai. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun samu nasarar ne a ranar 10 ga watan Mayu, 2025, inda tawaga ta musamman ƙarƙashin...
A yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar bude dandalin hadin gwiwa na Shanghai ko SCO na 2025, game da rage talauci da wanzar da ci gaba, wanda ke gudana a birnin Xi’an, na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin. Cikin sakon na sa shugaba Xi ya bayyana cewa,...
Ya misalta rashin basaraken da cewa, ba rashin ne kawai ga iyalai ko al’ummar masarautarsa ba, a’a rashi ne ga illahirin masarautar Bauchi da ma jihar Bauchi baki ɗaya. Gwamna Muhammad ya misalta Alhaji Garba a matsayin babban basaraken gargajiya wanda aka sani da hikima, tawali’u, da sadaukar da kai ga hidimta wa al’ummarsa....
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da sayen ƙarin motoci guda 10 don taimaka wa sojoji da ’yan sa-kai wajen yaƙi da ’yan Boko Haram da ISWAP. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai Kala-Balge, inda ya gana da ƙungiyoyi daban-daban. An kashe makiyaya 2 a wani hari...
A ganin mista Akanbi, manufofin kasashen yamma ne dalilin da ya haifar da tafiyar hawainiyar tattalin arzikin Najeriya da na sauran kasashe dake nahiyar Afirka. Misali, kamfanonin kasashen yamma sun samu damar mamaye bangaren hakar ma’adinai na Najeriya, kana sun takaitawa kasar damar sarrafa ma’adinai, da ta raya masana’antu. Ban da haka, matsayin musamman na...
Wasu makiyaya biyu sun rasu bayan da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka buɗe musu wuta a kusa da ƙauyen Tahore, da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da mamatan ke dawowa daga kasuwar Maikatako a kan babur. Yadda ’yan sanda...
Mahajjata da jami’ai sun yaba da wannan gaskiya da rikon amana. Wasu sun ce hakan ya ƙara musu ƙwarin gwiwa ga tsaron mahajjata da amincin tsarin aikin hajji. “Alhamdulillah, Hajiya ta samu kuɗinta gaba ɗaya,” in ji wani jami’in sansanin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Ado Aliero ya shahara wajen kai hare-hare, sace mutane da kashe-kashe a Jihar Zamfara da wasu sassan Arewa Maso Yammacin Nijeriya. An daɗe ana nemansa ba a samu nasarar kama shi ba, saboda ƙungiyarsa na da haɗin kai da goyon baya daga wurare da dama. Ko da yake hukumomin Saudiyya ba su tabbatar da sunayen...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ba Ta Da Alkiblar Siyasa
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da wani yanki na siyasa mai zaman kansa Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniya ba su da wata kafa ta siyasa mai cin gashin kanta, a maimakon haka dole ne a fahimci matsayinsu...
Wani harin kwanton bauna da rundunar sojin al-Qassam suka kai kan sojojin mamayar Isra’ila a Beit Lahiya ya yi sanadiyar halaka tare da jikkatan sojojin mamaya masu yawa Rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta sanar da cewa: Mayakanta sun kai wani kazamin harin kwantan bauna a yankin al-Atatra da ke...
Gwamnatin kasar Masar na shirin yin arangama ta soji da haramtacciyar kasar Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, musamman tashar talabijin ta 14, sun watsa wani rahoto cewa: Gwamnatin kasar Masar na kokarin karfafa karfinta na soji a tsibirin Sinai, tana mai gargadin abin da ta bayyana a matsayin “yiwuwar rugujewar yarjejeniyar zaman lafiya” da aka...

Shugaban Kasar Colombia: Ayyukan Kasar Sin Sun Nuna Wani Sabon Salo Na Ci Gaban Zamantakewar Al’ummar Bil’adama
Kwanan baya, yayin taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawar Sin da CELAC, shugaban kasar Colombia, Gustavo Petro ya ziyarci kasar Sin, inda kuma ya zanta da kafar CMG a shirin “Hira da shugabanni”. Yayin tattaunawar, shugaba Petro ya ce ya sha ziyartar kasar Sin cikin shekaru 20 da suka gabata. Ya kuma yi...
Mutane sun koma kwana a cikin jejin a sakamakon hare-haren ’yan bindiga a yankin Ƙaramar Hukumar Ƙaura Namoda da ke Jihar Zamfara. Mazauna yankunan sukan dawo cikin gari su yini, idan dare ya yi kuma su shiga daji su kwana, sakamakon ƙaruwar hare-haren ’yan ta’adda, inda suka kashe mutum huɗu suka yi garkuwa da wasu...
Da yammacin jiya Litinin, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci birnin Luoyang na lardin Henan. A yayin ziyarar, Xi ya ziyarci kamfanin Bearing Group na Luoyang, da gidan ibada na “Farin Doki”, da kuma ramin dutse na Longmen. Ya fahimci yadda aka inganta ci gaban masana’antun samar da...
An dauke kashin farko na maniyyata 550 daga jihar jigawa zuwa Saudiyya a filin jirgin Nuhu Muhammadu Sunusi domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan jim kadan bayan tashinsu zuwa kasa mai tsarki. Ya bayyana cewa maniyyatan sun fito ne daga kananan hukumomi...
Dubun wani ɗan bindiga ta cika a yayin da yake shirin shiga jirgi tare da sauran maniyyata aikin Hajji a Jihar Sakkwato. Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama ɗan ta’addan mai suna Sani Galadi ne a yayin da ake yi wa maniyyata tantancewar ƙarshe kafin hawa jirgi zuwa Ƙasa Mai Tsarki a Filin Jirgi...
Dubun wani ɗan bindiga ta cika a yayin da yake shirin shiga jirgi tare da sauran maniyyata aikin Hajji a Jihar Sakkwato. Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama ɗan ta’addan mai suna Sani Galadi ne a yayin da ake yi wa maniyyata tantancewar ƙarshe kafin hawa jirgi zuwa Ƙasa Mai Tsarki a Filin Jirgi...
Wani jami’in hukumar, Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa tsare-tsaren da hukumar ta ɗauka sun taimaka sosai, inda komai ke tafiya cikin kwanciyar hankali a Saudiyya. An fara jigilar maniyyatan ne a ranar 9 ga watan Mayu 2025 a filin jirgin sama na Owerri da ke Jihar Imo. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Jami’an tsaron ƙasar Saudiyya sun kama wasu mata biyu da ake zargin cewa mata da kuma mahaifiyar jagoran ’yan bindiga da gwamnatin Najeriya ke nema ruwa a jallo, Ado Aliero, bayan sun je aikin Hajji. An kama matar Aliero da mahaifiyar tasa ne a birnin Madina bayan sun je yin ziyara gabanin fara aikin Hajji....
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, tattaunawar dake tsakanin Iran da Amurka za ta iya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen dandalin tattaunawa na Tehran, Araghchi ya ce kasashen yankin suna goyon bayan tattaunawar da...
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yayi tattaunawa ta wayar tarho mai aramashi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, inda suka tattauna kan batutuwa da dama ciki har da yunkurin fara tattaunawar tsagaita bude wuta nan da nan tsakanin Rasha da Ukraine. Kamfanin dillancin labaran Rasha na RIA shi ma ya ambato, shugaban Kremlin...
Kasashen duniya 22 sun bukaci Isra’ila da ta gaggauta dawo da cikakken tallafin da take baiwa zirin Gaza. Tireloli tara na taimakon jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ne aka ba su izinin shiga zirin Gaza a ranar Litinin, wanda ake wa kallo a matsayin digo ‘’ digo a cikin teku,” in ji shugaban kula...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kula da lafiya na nufin yin abubuwa da ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka da kuma tabbatar da cewa jiki na aiki yadda ya kamata. Wannan ya haɗa da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, da dai sauran su. Sai dai a wannan zamani ’yan...
Bayan da mahukuntan kasar Sin suka kaddamar da yadda harkokin tattalin arzikin kasar suka gudana a watan Afrilun bana a ranar 19 ga wata, mataimakin shugaban zartaswa na kamfanin Novonesis na kasar Denmark, Morten Enggaard Rasmussen ya tattauna da wakilin CMG, inda a cewarsa, alkaluma sun nuna karfin tattalin arzikin kasar Sin. Ya ce Kamfaninsa...
Mai dakin Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta sake jaddada kudurin gwamnatin jihar na ganin an kawar da tu’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar. Ta bayyana hakan ne a lokacin da ta karɓi shugabannin Hukumar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Hana Safarar Mutane ta Jihar Zamfara, waɗanda suka kai mata ziyarar...
Jami’an Sashen Binciken Laifuka na Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Nasarawa (SCID) sun kama wani mai garkuwa da mutane a Kasuwar Shinge da ke Lafia, bisa rahotonnin sirri da suka samu. An samu nasarar cafke wanda ake zargin bayan shafe dogon lokaci rundunar na nemasa ruwa a jallo saboda laifuka da dama da suka hada...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, yankin Taiwan na kasar Sin ba shi dalili ko iko ko kuma hujjar halartar babban taron hukumar lafiya ta duniya (WHA), har sai sai gwamnatin tsakiya ta kasar ta amince masa. Kakakin ma’aikatar ne ya bayyana haka yau Litinin, lokacin da yake tsokaci kan matakin da WHA ta...
Shugaban kasar Lebanon Josept Aoun ya bayyana cewa gwamnatinsa tana son ta maida makamai a kasar Lebanon karkashin ikon hukuma kadai. Aoun ya ce kungiyar Hizbullah tana iya shiga harkokin siyasa na kasar Lebanon amma makamai na gwamnatin ne kadai. Jaridar ‘The National Ta Kasar Amurka’ ta n akalto shugaban yana fadar haka a kasar...
Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Gombe, Asma’u Muhammad Iganus, ta ce gwamnati za ta tabbatar da an yi wa ’yar shekara biyu, Maryam Buba da ake zargin mijin mahaifiyarta, Muhammad Magaji mai shekara 47, da yi mata fyaɗe. Kwamishiniyar tare da tawagarta sun kai ziyara gidan iyalan yarinyar da ke unguwar...
Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Gombe, Asma’u Muhammad Iganus, ta ce gwamnati za ta tabbatar da an yi wa ’yar shekara biyu, Maryam Buba da ake zargin mijin mahaifiyarta, Muhammad Magaji mai shekara 47, da yi mata fyaɗe. Kwamishiniyar tare da tawagarta sun kai ziyara gidan iyalan yarinyar da ke unguwar...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta kira mataimakin jakadan kasar Burtania a Tehran zuwa ma’aikatar don gabatar mata da korafi kan yadda jami’an tsaron kasar Burtaniya suke kama yan kasar Iran ma zauna birnin London tare da tuhumarsu da ayyukan Leken asiri wa JMI. Tashar talabjin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a...
Aƙalla mutum uku aka kashe, yayin da aka sace 26 a wani sabon harin da ’yan bindiga suka kai yankin Ƙaramar Hukumar Kaura Namoda, a Jihar Zamfara. Harin ya faru ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar a ƙauyukan da suka haɗa da Sabon Gari da Kungurki. Mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Edo ta yi murabus Hajji:...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin ganin cewa garin Marte bai koma hannun ’yan Boko Haram ba. Zulum, ya kai ziyara garin Marte domin duba halin da ake ciki da kuma yadda za a tabbatar da zaman lafiya. Mawaƙan APC sun zargi gwamnatin...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da taron tattaunawa ta Tehran wanda aka bude a ranar Lahadi 18 ga watan mayu a nan Tehran. A ranar Lahadi 18 ga watan Mayu da muke ciki ne aka bude taron tattaunawa da ta Tehran ta farko a nan Iran,...
Iyalan sarkin Okoloke na jihar Kogi, Oba James Dada Ogunyanda, sun yi kira ga al’umma don taimakawa wajen tara kuɗin fansa Naira miliyan ₦50 da masu garkuwa suka buƙata. An sace Sarkin ne daga fadarsa a Yagba West LGA ranar Alhamis da ta wuce. Duk da cewa sun tara miliyan ₦25 ta hanyar sayar da...
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi bankwana da maniyyata 966 da za su je aikin Hajjin bana, inda ya buƙace su da su kiyaye dokoki da tsarin ƙasar Saudiyya. Gwamnan, ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Abubakar Ibrahim Njodi, wanda ya gargaɗi maniyyatan da cewa duk wanda ya karya doka zai fuskanci...
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi bankwana da maniyyata 966 da za su je aikin Hajjin bana, inda ya buƙace su da su kiyaye dokoki da tsarin ƙasar Saudiyya. Gwamnan, ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Abubakar Ibrahim Njodi, wanda ya gargaɗi maniyyatan da cewa duk wanda ya karya doka zai fuskanci...
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara ta yi kakkausar suka ga gwamna Dauda Lawal kan kalaman da ta bayyana a matsayin bata gari dangane da kokarin gwamnatinsa na magance ‘yan fashi da makami da kuma bayar da tallafi ga wadanda ‘yan fashin suka kashe. Hakan ya biyo bayan wani faifan bidiyo ne...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Yana fatan tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka za ta kai ga cimma yarjejeniya ta gaskiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshgan ya bayyana cewa: Iran tana fatan tattaunawarta da Amurka za ta kai ga cimma yarjejeniya ta gaskiya da za ta tabbatar da dorewar zaman lafiya a...
Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da nuna wasu manyan fina-finai masu dogon zango 22 sakamakon zarginsu da saɓa ƙa’idar hukumar. Cikin wata sanarwa da jami’in hul da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar ya ce shugaban hukumar Abba Al-Mustapha ne bayar da umarcin saboda a cewarsa masu shirya fina-finan sun saɓa ƙa’idojin...

Wata ‘Yar Jarida Ta Nuna Mamaki Kan Nuna Damuwa Da Ciwon Biden Maimakon Kisan Gillar ‘Yan Sahayoniyya
A lokacin da kasashen Yamma suka yi biris da kisan gillar da ake yi a Gaza, kuma suna kuka kan cutar da tsohon shugaban Amurka Biden ke fama ita Marubuciya kuma ‘yar jarida kasar Autraliya Caitlin Jahnstone a cikin wani makala da ta rubuta ta siffanta abin da ta kira matsayin munafuncin ƙasashen yamma wajen...
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce ta samu gagarumar nasara wajen shiga sahun kasashen duniya a ranar cutar hawan jini ta duniya. Kwamishinan lafiya Dr Abubakar Labaran ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a taron tunawa da ranar hawan jini ta duniya, wanda aka gudanar a Kano. ...
Fira ministan gwamnatin rikon kwaryar Libiya ya bayyana cewa: Babu wata cibiyar tsaro a Libya sai dai cibiyoyi na yau da kullum da suka hada da sojoji da ‘yan sanda Abdul Hamid Dbeibah, shugaban gwamnatin rikon kwaryar gwamnatin hadin kan kasa, ya ce: “Babu wani wuri a kasar Libya, sai dai cibiyoyi na yau da...
Allah ya yiwa fitaccen ɗan jarida kuma wakilin Gidan Rediyon Muryar Amurika (VOA) a jihohin Borno da Yobe, Haruna Dauda Biu rasuwa a ranar Lahadi a Maiduguri. Marigayin, wanda ya kuma kasance tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jarida (Correspondents Chapel) na jihar Borno, ya rasu ne bayan doguwar jinya. Na Dauki Karramawar Jaridar LEADERSHIP Da Matukar...