ISWAP ta kashe manoma sama da 50 a Borno
Published: 18th, May 2025 GMT
Aƙalla manoma 50 ne suka rasu, sakamakon wani mummunan hari da ‘yan ta’addan ISWAP suka kai garin Malam Karanti da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa, a jihar Borno.
Majiyoyi sun ce mayaƙan sun afka wa manoma yayin da suke noma da kamun kifi, duk da cewar suna biyan haraji kafin yin noma.
Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma Tsafta a gidan aure: Abubuwan da kowace mace ya kamata ta sani“Sun mallaki takardun izini daga kwamandan ISWAP da ke kula da yankin Malam Karanti har zuwa Dawashi.
Sai dai harin ya faru ne a lokacin da kwamandan bai kasance a yankin ba, inda wasu daga cikin mayaƙan suka zargi manoman da leƙen asiri, inda suka ce suna taimaka wa abokan gabansu.
Wannan ne dalilin da ya sa suka kai harin.
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a harin ya ce: “Mun fara girbin wake ne lokacin da suka zo. Sun kewaye mu, suka ce duk wanda ya yi yunƙurin tserewa za su harbe shi.
“Wasu daga cikinmu sun yanke shawarar guduwa duk da hakan. Sun kashe sama da mutum 50, da yawa daga cikinsu an yanka su.
“Sannan sun kama wasu daga cikinmu. Yau ma sun je Dawashi sun kashe mutane, amma ba a san adadin waɗanda suka kashe ba tukuna.”
Gwamnati da hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa dangane da wannan mummunan hari ba.
Wannan hari ya zo cikin watanni biyar kacal bayan wani makamancin sa da aka kai ƙauyen Dumba, inda manoma aƙalla 40 suka rasa rayukansu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram hari ISWAP
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Jinjina Wa Matsayar Da Pakistan Ta Dauka Akan Harin Da HKI Ta Kawo Wa Iran
Janar Abdurrahim Musawi wanda ya tattauna ta wayar tarho ta kwamandan sojojin jamhuriyar musulunci ta Pakistan, Asim Munir, ya yi jinjina akan mataki na jarunta da Pakistan din ta dauka akan harin da HKI ta kawo wa Iran, haka nan kuma yadda ta nuna goyon bayanta ga Iran.
Janar Musawi ya kuma yi ishara da matsayar gwamnati da al’ummar Pakistan akan ta’addanci na HKI, kamar kuma yadda ya bayyawa kwamandan sojojin kasar ta Pakistan yadda Amurka ta taimakawa HKI a tsawon kwanaki 12 na yakin.
Har ila yau, janar Musawi ya ce; Tare da cewa mun rasa kwamandoji masu girma a farkon harin ta’addancin, sai dai kuma duk da haka, mun hana ‘yan sahayoniyar cimma manufofinsu.
A farkon yakin dai, kasar Pakistan ta bakin shugabanninta sun yi tir da harin na HKI, tare da nuna cikakken goyon bayansu ga jamhuriyar musulunci ta Iran wacce su ka bayyana a matsayin ‘yar’uwa kuma makwabciya.