Aminiya:
2025-10-13@17:52:55 GMT

Gwamnatin Kano ta haramta ‘Ƙauyawa Day’ a lokacin bikin aure

Published: 17th, May 2025 GMT

Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano, ta dakatar da dukkanin cibiyoyin gudanar da taro da ke faɗin jihar, tare da haramta gudanar da bikin ‘Kauyawa Day’ gaba ɗaya.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne, ya bayyana hakan a ranar Asabar, bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar.

ISWAP ta yi wa manoma 15 yankan rago a Borno Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo a Ribas

Ya ce wannan mataki na cikin sabuwar doka da majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da ita, kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanya wa hannu.

“Daga yanzu, duk wanda ya shirya wani taro da sunan Kauyawa ko Villagers Day, ya karya doka,” in ji El-Mustapha.

Sabuwar dokar ta bai wa hukumar ikon sanya ido da kula da dukkanin cibiyoyin taro da ayyukan DJ a jihar.

Saboda haka ne aka dakatar da dukkanin cibiyoyin taro har zuwa wani lokaci.

An ɗauki wannan mataki ne bayan ƙorafe-ƙorafe daga wasu ƙungiyoyin addini da na al’adu kan yadda ake gudanar da bikin Ƙauyawa Day.

Galibin waɗannan bukukuwa matasa da ’yan mata ne ke shirya su, amma ana zargin suna haifar ɗabi’un da ba su dace ba.

El-Mustapha, ya buƙaci shugabannin al’umma da jami’an tsaro su taimaka wajen tabbatar da wannan doka.

“Muna roƙon sarakunan gargajiya, ‘yan sanda, Hisbah da masu tsaron unguwanni su haɗa kai da mu wajen tabbatar da bin wannan umarni,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gwamnatin Kano umarni

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da kyautar motoci ƙirar Hilux guda shida da babura 30 domin taimaka wa sojoji wajen yaƙi da ’yan bindiga a faɗin jihar.

Gwamnan, ya miƙa motocin da baburan ga Kanal Hussaini Rabi’u Toro na rundunar sojoji ta takwas a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.

’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi

Ya ce wannan kyauta na cikin ƙoƙarin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da walwalar al’umma.

“Tsaro shi ne babban abin da gwamnatina ta mayar da hankali a kai. Ba za mu yi wasa da harkar tsaro ba.

“Za mu ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da dukkanin abin da suke buƙata,” in ji Gwamna Idris.

Ya ƙara da cewa, an fara bai wa sojoji ne kyautar, amma sauran hukumomin tsaro su ma za su samu irin wannan tallafi nan ba da jimawa ba.

Da yake bayani a wajen taron, Kanal Hussaini Toro, ya gode wa gwamnan bisa wannan taimako, inda ya cewa hakan zai ƙara musu ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Sojoji sun yi matuƙar farin ciki da wannan tallafi. Zai taimaka wajen inganta aikinmu na tabbatar da tsaro a Jihar Kebbi,” in ji Kanal Toro.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Sandan Jihar Neja Sun Tabbatar Da Masu Sa-kai Kan Sahihiyar Kariya.
  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Kungiyar ‘Yan Dako Ta Kasa Ta Nada Sabon Sakatare A Jigawa
  • Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro
  • An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Ka Tattauna Batun Falasdinu
  • Al’ummar Karamar Hukumar Dutse Sun Bukaci Gwamnatin Jigawa Ta Yashe Madatsar Ruwa Ta Warwade
  • Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina
  • Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida
  • Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya