UNICEF Ya Ce; Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Kananan Yara 45 Cikin Kwana Biyu Kacal A Gaza
Published: 17th, May 2025 GMT
Asusun kula da kananan yara “UNICEF” na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kashe yara 45 a Gaza cikin kwanaki biyu kacal
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kashe kananan yara 45 a Zirin Gaza a cikin kwanaki biyun da suka gabata, kuma wani abin tunatarwa shi ne cewa: Yara a Gaza na shan wahala da farko, suna fama da yunwa kowace rana kuma suna fuskantar hare-haren wuce gona da iri da muggan makamai kan mai uwa da wabi.
A cikin wata sanarwa da Asusun ya fitar a ranar Juma’a, ya jaddada yi kira da a kawo karshen wahalhalu da kashe-kashen yara a kullum.
A nata bangare, Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa: “Hare-haren sojojin gwamnatin mamayar Isra’ila na ci gaba da yin mummunan tasiri ga cibiyoyin kiwon lafiya, ciki har da asibitin Turai na Gaza da ke Khan Yunis, wanda yanzu ya daina aiki.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan
Wasu jerin shirye-shiryen neman ‘yancin kan Taiwan da hukumomin yankin suka gudanar a baya bayan nan, sun sha suka sosai daga al’ummomin kasa da kasa. Wani nazari da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa adadin mai rinjaye na wadanda suka shiga nazarin, watau kimanin kaso 89.8 sun yi ammana cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama wata matsaya da kasashen duniya suka amince da ita, inda suka soki hukumomin yankin Taiwan bisa shirinsu na neman ‘yanci da takala.
Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne cikin harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 13,650 suka bayar da amsa cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA