Budurwa ta gantsara wa saurayinta cizo a mazakuta a Ribas
Published: 17th, May 2025 GMT
Wata mata da age zargin ta cije mazakutar saurayinta ta shiga hannun ’yan sanda.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta kama matar mai shekara 43 ne bayan ta yi wa masoyin nata wannan aika-aika ne a lokacin da suke rikici a cikin gida a unguwar Mile 3 da ke yankin Diobu a garin Fatakwal babban birnin jihar.
Lamarin wanda ya afku a ranar Alhamis, ya girgiza mazauna titin Bishop Okoye mai yawan jama’a lokacin da aka samu labarin lamarin.
A cewar majiyoyi, rikicin ya fara ne lokacin da masoyin matar ya nemi kwanciya da ita.
An bayar da rahoton cewa matar ta ƙi amincewa da buƙatar saurayin nata, inda ta zarge shi da yin amfani da ƙwayoyin masu ƙara kuzarin tsawaita saduwa.
Wani mazaunin garin da ya zanta da wakilin PUNCH da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Saurayin matar ya fusata ne, saboda masoyiyar tasa ta ƙi amincewa da buƙatarsa.
“Ana cikin haka, ta yi nasarar kama mazaƙutarsa da bakinta kuma ta gantsara masa cizo.”
Rahotanni sun ce kururuwar mutumin ta ja hankalin maƙwabta, inda wasu suka yi yunƙurin riƙe matar kafin ’yan sanda su shiga tsakani.
Majiyar ta ƙara da cewa, “Matar ta cije kan mazaƙutar mutumin gaba ɗaya.”
Jami’an rundunar ’yan sanda reshen Nkpolu ƙarƙashin jagorancin jami’in ’yan sanda na yankin ne suka ceto ta, inda aka tsare su.
An garzaya da wanda aka ciza zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba a cikin birnin domin kula da lafiyarsa cikin gaggawa.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ribas, Sufeto Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a.
“Eh, zan iya tabbatar da lamarin, an kama matar (wanda ake zargi) mai shekaru 43, kuma ana ci gaba da bincike,” in ji Iringe-Koko.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Saurayi
এছাড়াও পড়ুন:
Ba a ba mu dala 100,000 da gwamnati ta mana alƙawari ba — Super Falcons
Kyaftin ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, Rasheedat Ajibade, ta ce har yanzu ba a ba su dala 100,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi musu alƙawari bayan sun lashe gasar WAFCON a ƙasar Maroko ba.
Ajibade, ta bayyana takaicinta game da jinkirin biyan kuɗin da aka musu alƙawari.
Amurka za ta sayar wa Najeriya makaman N530bn don yaƙi da ta’addanci ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai“Ba mu karɓi kuɗin ba tukunna, amma ina fata za a biya mu. Duk alƙawuran da aka mana, yanzu dai ba mu samu komai ba.”
Ajibade ta jagoranci tawagar zuwa ga nasara, inda suka sake lashe kofin WAFCON a bana.
Bayan nasarar, Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ’yan wasan da masu horar da su lambar yabo ta ƙasa (Officer of the Order of Niger – OON).
Haka kuma ya yi musu alƙawarin bai wa kowannensu dalar Amurka 100,000 da gida mai ɗaki uku.
Lokacin da ya karɓe su a Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya yaba da jajircewarsu, da kuma ƙoƙarinsu, inda ya ce nasararsu ta ɗaga mutuncin Najeriya.