Fira Ministan Libiya Ya Tantance Bangarorin Da Kula Da Hakkin Tsaron Kasar Ya Rataya A Wuyarsu
Published: 19th, May 2025 GMT
Fira ministan gwamnatin rikon kwaryar Libiya ya bayyana cewa: Babu wata cibiyar tsaro a Libya sai dai cibiyoyi na yau da kullum da suka hada da sojoji da ‘yan sanda
Abdul Hamid Dbeibah, shugaban gwamnatin rikon kwaryar gwamnatin hadin kan kasa, ya ce: “Babu wani wuri a kasar Libya, sai dai cibiyoyi na yau da kullum, ciki har da sojoji da ‘yan sanda,” Dbeibah, ya fadi haka ne biyo bayan al’amuran tsaro da suka faru a babban birnin kasar, Tripoli, a ranar litinin bayan kisan Abdul Ghani al-Kikli, wanda aka fi sani da “Ghaniwa,” kwamandan kungiyar da ake kira “Stability Support Apparatus”.
Bayanin na Dbeibah ya zo ne a yayin wani taron tsaro da aka gudanar a makon da ya gabata tare da mukaddashin ministan harkokin cikin gida, Imad al-Tarabulsi, karamin sakatare na ma’aikatar tsaro, Abdul Salam al-Zoubi, da daraktan sashen leken asiri na soji. Mahalarta taron sun ba da cikakken bayani kan matakan aiwatar da shirin tsaro na babban birnin kasar.
Dbeibah ya kara da cewa: “Dukkan sansanonin soji da kayayyakin aiki a kasar dole ne su kasance karkashin ma’aikatar tsaro da sojojin kasar Libya kadai,” yana mai jaddada cewa “babu wata kungiya da ke dauke da makamai a wajen wannan tsarin da ke da hakki, kuma horon hukumomin shi ne ka’idar da ba za a kebe kowa ba.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Tana Da Dokoki Da Ka’idoji Sama Da 180 Dake Kare Nakasassu
Yau Talata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai na jerin taruka masu jigon “Kammala shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 mai inganci”.
Yayin taron, jami’in kungiyar nakasassu ta Sin ya bayyana cewa, yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, an kiyaye hakki da moriyar nakasassu na kasar yadda ya kamata.
A halin yanzu, kasar tana da dokoki da ka’idoji sama da 180 da suka shafi kare nakasassu, ciki har da “Dokar gina muhalli marar shinge”, kuma akwai dokoki da ka’idoji 41 na kasa da suka kara tanade-tanade don kare hakkoki da muradun nakasassu a lokacin tsarawa da gyara abubuwan da suka shafi muhalli.
Bugu da kari, a lokacin aiwatar da “shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 mai inganci”, an aiwatar da wani shirin na tsawon shekaru uku (2022-2024) domin taimakawa nakasassu wajen samun ayyukan yi, inda yawan nakasassun dake samun ayyukan yi ya karu akai-akai. Ban da haka kuma, a cikin wannan wa’adi, nakasassu fiye da miliyan 9 ne aka ba su ayyukan yi a fadin kasar, kuma adadin sabbin ayyukan yi na nakasassu a birane da kauyuka ya kai miliyan 2.31. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp