Zubar Da Jini Mafi Muni A Cikin Daren Jiya A Zirin Gaza, Inda Falasdinawa 80 Suka Yi Shahada
Published: 18th, May 2025 GMT
Dare da aka zubar da jini mafi muni a Gaza: Sama da Falasdinawa 80 ne suka yi shahada a sassa daban-daban na Zirin
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula a yankuna daban-daban na zirin Gaza, inda suka yi sanadiyyar shahadan sama da Falasdinawa 80, kuma mafi yawansu a wani kisan kiyashi da aka yi wa ‘yan gudun hijira a yankin Al-Mawasi na Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza, bayan da aka jefa bama-bamai da kona tantunansu a kusa da Asibitin kwararru na Kuwait, baya ga kisan kiyashi a duk fadin yankin.
Majiyoyin Falasdinawa sun ce an kona mutane 36, yawancinsu mata da kananan yara, bayan da sojojin mamayar Isra’ila suka yi ruwan bama-bamai a tantunansu, tare da cinna musu wuta. An kuma kai harin bama-bamai a gidaje hudu a yankin Abasan da biyu a Al-Fakhari.
Har ila yau sojojin mamayar sun kai hare-haren bama-bamai a wasu gidaje a tsakiyar zirin Gaza, inda suka kashe mutane 9 a Az-Zawayda da 3 a Deir al-Balah.
A arewacin Zirin Gaza, jiragen sama sojin mamayar sun kai hari kan gidajen fararen hula, inda suka kashe Falasdinawa 12 a gidan Nasser Jabalia al-Nazla, 8 a wani gida a Jabaliya al-Balad, da shahidai 7 a gidan al-Barawi a garin Beit Lahiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an tsaro sun tarwatsa taron kwamitin amintattun PDP
Jami’an tsaro sun hana mambobin Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar Adwa ta PDP gudanar da taron da suka tsara gudanarwa.
A safiyar Litinin din nan ne jami’ai da yawa ne suka kutsa cikin zauren da aka tsara gudanar da taron inda suka bukaci wadanda suka hallara da su watse.
Jami’an tsaro da aka jibge a hedikwatar babbar jam’iyyar adawar sun hana mambobin kwamitin amintattu gudanar da taronsu a hedikwatar jam’iyyar.
Har zuwa lokacin hada da wannan rahoto, wasu daga cikin ’yan kwamitin amintattun na PDP suna tattaunawa a kan halin da ake ciki.
Mun samu rahotannin cewa jami’an sun umurci mambohin su bar ofishin jam’iyar domin ganin ba a gudanar da wani taro a ofishin jam’iyar ba.