Dole Ne Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Samar Da Ayyukan Yi Da Rage Talauci — Bankin Duniya
Published: 17th, May 2025 GMT
Habakar matsayi na kasafin kudi ya inganta a cikin 2024, ta hanyar habaka kudaden shiga. Gibin kasafin kudi ya ragu daga kashi 5.4 na kudin shiga a shekarar 2023 zuwa kashi 3.0 na kudin shiga a shekarar 2024, babban ci gaban da aka samu sakamakon karuwar kudaden shiga na daukacin tarayyar kasar, wanda ya karu daga naira tiriliyan 16.
Rahoton ya kara da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya tsaya tsayin daka amma ana sa ran zai fadi zuwa matsakaicin shekara da kashi 22.1 cikin 100 a shekarar 2025, yayin da tsayin daka mai tsayi ya tabbatar da amincin manufofin kudi tare da rage tsammanin hauhawar farashin kayayyaki.
Ko da yake, ya nuna cewa kalubalen shi ne don karfafa kwanciyar hankali na tattalin arzikin kasa da habaka yanayin tattalin arziki ta hanyar zurfafa gyare-gyare mai fa’ida.
“Akwai bukatar tattalin arziki ya samar da karin ayyukan yi masu inganci da kuma rage talauci a tsakanin al’umma.”
Mukaddashin Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Taimur Samad ya ce, “Nijeriya ta samu ci gaba mai ban sha’awa don maido da kwanciyar hankali a fannin tattalin arziki, tare da ingantuwar yanayin kasafin kudi, yanzu Nijeriya na da damar inganta adadi da ingancin kashe kudade na ci gaba, kara saka hannun jari kan rayuwar Dan’adam, kariyar zamantakewa, da ababen more rayuwa.
“Rarraba dukiyar al’umma na iya fara kaucewa tsarin da ba a dawwama a baya, a maimakon haka wajen biyan manyan bukatu na ci gaban Nijeriya, ciki har da gwamnati ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da muhimman ayyukan gwamnati da kuma zama mai ba da damar ci gaban kamfanoni masu zaman kansu.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Bankin Duniya Nijeriya Tattalin Arziki
এছাড়াও পড়ুন:
Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025
Ministan gidaje da raya birane da karkara na kasar Sin Ni Hong, ya ce yanayin sashen samar da gidaje na Sin ya kara inganta tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, yayin aiwatar da manufar raya kasa karo na 14, inda jimillar adadin sayar da sabbin gidaje na kasuwa ya kai fadin sakwaya mita biliyan biyar.
Ni Hong, ya bayyana hakan ne a yau Asabar, yayin wani taron manema labarai. A cewarsa, sama da Sinawa miliyan 110 sun amfana daga babban tsarin gyaran tsofaffin gidaje cikin shekarun biyar. Kazalika, tsofaffin gidaje dake unguwanni sama da 240,000 a sassan biranen Sin, sun mori shirin gyaran fuska cikin wa’adin. Don haka gaba daya, yanayin ingancin muhallin biranen Sin ya kara inganta yadda ya kamata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA