Babu Wani Dan Jarida Da Aka Hana Shiga Taron Gwamnonin Arewa – CPS Ibrahim Musa
Published: 17th, May 2025 GMT
Sai ya ce “Na riga na amsa wannan tambayar amma har yanzu kana sake maimaita ta. Idan dai za a iya tunawa, ‘yan jarida 43 mazauna Kaduna ne suka halarci taron, ciki har da wasu ‘yan jarida daga wasu jihohin da suka raka gwamnonin nasu. Don haka, ba daidai ba ne a ce na hana ‘yan jarida shiga taron gwamnonin Arewa.
Duk jaridun kasar nan sun je a wurin. Duk gidajen rediyo da talbijin na Kaduna suna wurin. Duk wakilan manyan gidajen Talabijin da Rediyo da ke wajen Kaduna su ma suna nan. Kada ka dauki maganata a wani bangare daban, je ka bincika. Duk wadannan labarai ne irin na teburin mai shayi.
Ni kuma ban sani ba. Abin da na sani shi ne, idan kai dan jarida ne da ke Kaduna kuma ba ka cikin ’yan jarida 43 da aka gayyata ko kungiyoyin yada labarai, to akwai bukatar ka bincika shin ka cancanci a kira ka da dan jarida ko a’a. Akwai bambanci tsakanin ‘yan jarida da masu rubutun ra’ayin a Intanet. Kuma a cikin ‘yan jarida, akwai flotsam da jetsam da ake kira Press Center Press Corps, PCPC a takaice.
Menene asalin abin da ya faru a ranar Asabar da ya zama wasu dandali na intanet na kira a tsige ka a matsayin babban sakataren yada labarai?
Da farko ina yi wa Gwamnatin Jihar Kaduna hidima bisa yardar Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani. Zai iya cire ni ba tare da wani ya tambaye shi ya yi haka ba. Haka nan zai iya cire ni ba tare da dalili ba. Bayan na fadi haka, bari in amsa tambayarka.
A taron Gwamnonin Arewa kafin na karshe, sama da ‘yan jarida 100 ne suka halarci taron! Hakan ya zarce adadin bakin da dukkan ma’aikatan da gidan gwamnatin Kaduna suka gayyata. Mafi munin abin da ya faru, shi ne yadda wasunsu ba sa gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, sun koma zawarcin manyan mutane suna yin abin da shi ne ra’ayinsu.
Bayan taron, wasu ’yan uwana Sakatarorin Yada Labarai ko SA Media, sun koka, a madadin shugabanninsu. Don haka, a wannan karon, na dauki matakin daidaita lamarin lambar ta hanyar rubuta sunaye da kungiyoyin yada labarai na duk masu aiko da rahotanni da ’yan jarida na gida a cikin gidajen jaridu da na lantarki.
Jerin sunayen ya kai 43. Don haka, na aika da jerin sunayen ga Babban Jami’in Tsaron mu wanda ya aika da shi zuwa bakin kofar shiga fadar gwamnati wato ‘Gate’. Sai na bi diddigin wadanda na san mun gayyata. Don haka, idan ba sunanka a cikin wannan takarda kuma ba ka sami takardar gayyata ba, ba za a ba ka izinin shiga Gidan Gwamnati kai tsaye ba.
Kai duk da jerin sunayen mutane 43, sai da mkua samu matsala wajen shigar da su duka zauren majalisar inda gwamnoni da sarakunan gargajiya ke taro. An yi ta gwabza fada a kofar shiga zauren majalisar. Don haka, za ku iya tunanin idan ma an ce an gayyaci ‘yan jarida 100 ko fiye da hakan!
An zarge ku da cewa ba kowa kuka dauka ba, me ya sa yin hakan ya zama da wuya?
Yin hakan ba kawai wahala ba ne amma ba zai yiwu a dauki kowa da kowa ba. Na samu labarin cewa akwai ‘yan jarida kusan 400 a Kaduna, ta yaya zan iya daukar su duka?
Don Allah a gaya min, ku taimake ni. Yawan ’yan jarida, idan adadin ya yi daidai wannan ba matsala, amma ba zan iya daukar duk ‘yan jarida daga dukkan kafofiin yada labarai ba.
Ba za ka iya rubuta dandalin jaridun da suke a Online ba, ku tattara labarai daga wasu ku sake bugawa kuma kuna tsammanin zan dauke ku. Kuna iya daukar labarin ku watsa don kanku, za mu iya ba da labari idan bukatar hakan ta taso, zan iya ba da taimako. Amma ba zan iya daukar mutumin da ba zai iya rubuta labari ba, kawai don ya zo ya nuna min katin shaidar da shi ya yi domin kashin kansa.
NUJ tana da ayyuka da yawa da za ta yi wajen tsaftace sana’ar. Wasu daga cikin labaran da aka buga na cike da kura-kurai na nahawu da ya kamata a ce dan jarida ya san su. Wani abin damuwa shi ne wasu daga cikinsu sun shafe kusan shekaru 30 a aikin jarida, amma duk da haka, ba su da gogewa a aikin nasu. Abin takaici, sauran kwararru a harkar suna karanta labaran.
Amma kuma dole ne in yaba wa shugaban NUJ na kasa, Alhassan Yahya, da ya shiga lamarin, domin jin abin da ke faruwa, bayan jin labarin cewa wai na hana shiga, nan take ya kira ni kuma na yi masa bayanin abin da ya faru, na kuma bukaci ya kira wakilin kowace jarida ta kasa don jin ko akwai wanda aka hana shi yada labarin.
Na kuma mika jerin sunayen ‘yan jaridar da aka gayyata a gare shi. Saboda dattaku ya roki cewa mu yi kokarin ganin mun sasanta lamarin cikin lumana.
Ta yaya za ku warware wannan batu?
Babu abin da za a daidaita a nan. Idan da suna aiki da kafofin yada labarai masu inganci, da na kai karar kafofinsu ga kotu, ko kuma na kai kararsu ga NUJ ko Majalisar ‘yan Jarida ta Nijeriya. Amma kamar yadda na fada a baya. Sai dai kuma zan tuntubi lauyoyina domin su kai su kara domin an yi min kazafi a matsayina na Malam Ibraheem Musa.
‘Yancin fadin albarkacin baki ba lasisin bata suna bane. Mutane da yawa masu mutunci da manyan abokan aiki sun zo min suna fada min cewa in yi watsi da abin da aka rubuta a kaina domin duk wanda ya yi mu’amala da ni zai iya tabbatar da amincina.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Arewa Jarida yada labarai
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi
Gwamnonin jihohin kudu maso yammacin Najeriya sun bada sanarwan cewa lokacin kafa yansandan jihohi ya yi, har’ila yau dakuma karfafa kula da dazuzzukan kasar saboda magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar.
Jaridar Daily Trust ta nakalto gwamnonin na fadar haka a jiya Litinin bayan taron gwamnonin shiyar kudu maso yammacin kasar da suka gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo. Gwamnonin 6 sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika masu gadin dazuzzuka a shiyar kudu maso yammacin kasar don tabbatar da tsaronsu , sannan gwamnonin jihohin guda shida ne zasu dauki nauyin kula da jami’an tsaron. Labarin ya kara da cewa shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ne ya karanta jawabin bayan taron gwamononin 6. Sauran gwamnonin sun hada da Dapo Abiodun na jihar Ogun, Biodun Oyebanji na jihar Ekiti, Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo, Ademola Adeleke na jihar Osun, wanda mataimakinsa , Yerima Kola Adewusi ya wakilta sai kuma gwamna mai masaukin baki Seyi Makinde na jihar Oyo. Taron gwamnonin ya yabawa gwamnatin tarayyar kan kokarin da take yi na magance matsalolin tsaro a arewacin kasar, suna kuma gabatar da alhininsu gareta saboda abubuwan bakin ciki da suka faru a jihohin Kebbi, Naija da kuma Kwara.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen November 24, 2025 Yara 50 Da Aka Sace A Najeriya Sun Tsere Daga Hannun Barayin Daji November 24, 2025 Habasha: Bayan Shekaru 10,000 Dutsen Hayli Gubbi Ya Yi Aman Wuta November 24, 2025 Iran Ta Mika Ta’aziyyarta Ta Shahadar Kwamandan Mayakan Hizbullah November 24, 2025 Hizbullah Ta Sanar Da Shahadar Kwamandan Jihadi Haisam al-Tabtabai November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci