Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Dandalin SCO Na 2025
Published: 20th, May 2025 GMT
A yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar bude dandalin hadin gwiwa na Shanghai ko SCO na 2025, game da rage talauci da wanzar da ci gaba, wanda ke gudana a birnin Xi’an, na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin.
Cikin sakon na sa shugaba Xi ya bayyana cewa, rage talauci wanda batu ne da ya shafi duniya baki daya, buri ne na daukacin kasashen duniya.
Hakan ya shaida ingancin turba mai halayyar musamman da kasar Sin ke bi wajen rage talauci, tare da rubuta wani sabon babi a tarihin bil’adama ta fuskar yaki da fatara. Daga nan sai shugaban na Sin ya jaddada cewa, karancin ci gaba shi ne tushen talauci, kuma dandalin SCO ya aiwatar da managartan matakai a fannin rage talauci, da wanzar da ci gaba a shekarun baya bayan nan, kuma hakan ya haifar da tarin sakamako masu gamsarwa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: rage talauci
এছাড়াও পড়ুন:
Yankin Taiwan Ba Shi Da Iko Ko Hujjar Halartar Taron WHA
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, yankin Taiwan na kasar Sin ba shi dalili ko iko ko kuma hujjar halartar babban taron hukumar lafiya ta duniya (WHA), har sai sai gwamnatin tsakiya ta kasar ta amince masa.
Kakakin ma’aikatar ne ya bayyana haka yau Litinin, lokacin da yake tsokaci kan matakin da WHA ta dauka na kin sanya bukatar Taiwan ta halartar taron a matsayin ‘yar kallo, cikin ajandarta.
A cewar kakakin, an shafe wani lokaci yanzu, hukumomin jam’iyyar DPP da wasu kasashe suna kokarin mayar da hannu agogo baya, inda suke kalubalanta da kokarin hargitsa kudurin MDD mai lamba 2758, domin kalubalantar manufar Sin daya tak a duniya. Ya ce, wannan ba kalubale ne ga cikkaken ‘yancin kasar Sin da iko kan yankunanta ba, kalubale ne ga matsaya ta adalci da kasa da kasa suka cimma da kuma tsarin odar duniya, bayan yakin duniya na II. Ya ce, kasa da kasa sun amince da matakin Sin na kin amincewa Taiwan ta halarci taron na bana, lamarin da ya nuna cewa, yarda da manufar Sin daya tak a duniya, shi ne burin al’umma da ya dace da yanayin da ake ciki, kuma shi ne abu mafi dacewa. Bugu da kari, kakakin ya ce, yadda kasa da kasa suka amince da manufar kasar Sin daya tak a duniya, abu ne da ba za a iya kalubalanta ba. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp