HKI Ta Bude Kofofin Shigar Kayakin Agaji Zuwa Cikin Gaza A Karon Farko Bayan Kimani Watanni 2.5
Published: 19th, May 2025 GMT
Gwamnatin HKI ta bude kofofin shigar kayakin Agaji zuwa cikin zirin Gaza bayan takurawan kasashen duniya daga ciki har da kawayen ta kan cewa ba zasu iya ci gaba da ganin Falasdinawa suna mutuwa saboda da yunwa ba.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta nakalto wata majiyar jami’an gwamnatin HKI na fada a yau litinin kan cewa zasu fara barin kayakin agaji su shiga zirin Gaza daga yau zuwa shawarar da zasu dauka nan gaba.
Labarin ya kara da cewa a safiyar yau litinin tawagar motoci dauke da kayakin abinci da magungun sun shiga zirin gaza ta kofar Karim Abusaleh, sannan MDD zata kula da shigowar kayakin agaji zuwa zirin na Gaza, a fadin tashar radiyo ta sojojin HKI.
Wasu majiyoyin HKI sun bayyana cewa shugaban kasar Amurka Donal Trump ya takurawa firai Ministan HKI kan ya bar abinci ya shiga Gaza amma bai yi masa magana a kan dakatar da budewa juna wuta ba. Hakama wasu kasashen turai sun yi baraza ga Natanyaho kan wannan al-amarin.
A halin yanzu dai masu tsatsauran ra’ayi a gwamnatin HKI suna bada shawarori daban-daban don rama kungiyar Hamas da makamanta ko kuma kwace ikon Gaza daga hannunta. Wasu sun bada shawara kan cewa kasar Masar ta karbi iko da Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rokar Kasuwanci Ta Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan Adam 6 Zuwa Sararin Samaniya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp