Gwamnatin kasar Masar na shirin yin arangama ta soji da haramtacciyar kasar Isra’ila

Kafofin yada labaran Isra’ila, musamman tashar talabijin ta 14, sun watsa wani rahoto cewa: Gwamnatin kasar Masar na kokarin karfafa karfinta na soji a tsibirin Sinai, tana mai gargadin abin da ta bayyana a matsayin “yiwuwar rugujewar yarjejeniyar zaman lafiya” da aka rattaba hannu tsakanin kasashen biyu a shekara ta 1979.

Tashar talabijin ta NAN ta nakalto Eliyahu Dekel, tsohon shugaban hukumar leken asirin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma masani kan al’amuran Masar na cewa: Masar na cikin gaggawar shirin tunkarar rikicin soji, yana mai cewa “yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu a shekarar 1979 ta kasance cikin yanayi na rugujewa tun lokacin da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar, kuma babu wata magana daya da ba a karya ba,” in ji shi.

A wata hira da aka yi da shi kan shirin na Oded Menashe, Dekel ya kara da cewa, nazarin hotunan tauraron dan adam ya nuna yadda ake gina filayen tashi da saukar jiragen sama na soja guda uku a yankin Sinai, baya ga gada da mashigar ruwa kusan 60 da ke kan mashigin Suez, yana mai bayyana hakan a matsayin wani yanayi na soji mai cike da damuwa.

Ya yi nuni da cewa, tun a shekara ta 2007, Masar ta kara kaimi kan ayyukan soji a yankin, wanda ya yi la’akari da shi a matsayin “shirin da take yi na yiyuwar arangama da sojojin mamayar Isra’ila.”

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya

An gudanar da taron tattaunawa na duniya kan kirkire-kirkire da bude kofa da ci gaba na bai daya, jiya Juma’a a birnin Lagos na Nijeriya. Yayin taron wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da karamin ofishin jakadancin Sin dake Lagos suka shirya, ministan kula da harkokin matasa na Nijeriya Ayodele Olawande da shugaban CMG Shen Haixiong, sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo.

A cewar ministan na Nijeriya, cikin shekaru 5 da suka gabata, dubban matasan kasar sun ci gajiyar tallafin karatu da shirye-shiryen horo da na musaya da Sin ta samar, kuma wannan hadin gwiwa da ake yi a aikace ya kara fahimta da aminci tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, a shirye ma’aikatarsa take ta karfafa hadin gwiwa da sassa masu ruwa da tsaki na kasar Sin wajen ci gaba da fadada shirye-shiryen musaya da na hadin gwiwa da suka shafi matasa.

A nasa bangare, Shen Haixiong ya ce a matsayinta na babbar kafar yada labarai dake watsa shirye shiryenta ga sassa daban daban na duniya, tashar talabijin ta CCTV dake karkashin CMG da abokan huldarta, za su yayata shawarar Sin ta jagorantar harkokin duniya da gabatar da tafarkin Sin na zamanantar da kanta da karfinta na kirkire kirkire a sabon zamani ga al’ummar duniya. (Mai fassara: FMM)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar November 1, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung  November 1, 2025 Daga Birnin Sin Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
  • MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
  • Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
  • Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma