Kafofin Yada Labarai Na Amurka Sun Bayyana Kuzari Da Ci Gaban Da Fina-finan Kasar Sin Ke Samu A Bikin Cannes
Published: 18th, May 2025 GMT
Kamar yadda mujallar ta bayar da rahoto a kai, rumfar fina-finai ta kasar Sin ta zama wata alama da ke nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kyautata cudanyar al’adu da hadin gwiwar kasa da kasa a harkar fina-finai. Kana, bisa samun karuwar jawo hankulan kasashen duniya da kuma kafa kwakkwarar turbar fasahar kirkira ta gwaninta da iya tsara labarin fim, sashen fina-finan na kasar Sin ya mike haikan wajen taka rawa sosai a duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Ziyarci Gidajen Tarihin Kasar Sin Sau Biliyan 1.49 A Shekarar 2024
Hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sin ta bayyana cewa, gidajen tarihi na sassan kasar sun gudanar da bukukuwan nune-nunen kayayyaki 43,000, da tarurrukan ilimi 511,000.
An bayyana wadannan alkaluman ne a yau Lahadi a wani bikin tunawa da ranar gidajen tarihi ta duniya a gidan adana kayayyakin tarihi na babban mashigin ruwa wato Grand Canal a Beijing.
A cikin shekarar 2024, an yi rajistar sabbin gidajen tarihi 213 a kasar Sin, inda hakan ya kara yawan adadin gidajen tarihi na kasar zuwa 7,046, kamar yadda hukumar kula da su ta bayyana.
Kazalika, ta kara da cewa, kasar Sin tana kara fadada manufofinta na shiga gidajen tarihi ba tare da biyan kudi ba, inda sama da kashi 91 cikin dari na dukkan gidajen tarihinta ke ba da iznin shiga kyauta. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp