Sojojin Libiya Sun ‘Yantar Da Fursunoni Daga Gidajen Yarin Sirri Da Ake Tsare Da Su Ba Bisa Ka’ida Ba
Published: 18th, May 2025 GMT
Sojojin Libiya sun ‘yantar da fursunoni da dama daga gidajen yari na sirri da ke karkashin dakarun Tallafawa da Wanzar da Kwanciyar hankali na Kasar
Sojojin kasar Libya a birnin Tripoli fadar mulkin kasar sun ‘yantar da fursunoni da dama da ake tsare da su a gidajen yari na sirri karkashin hukumar “Tallafawa da wanzar da zaman lafiya” bayan sun kwace iko da wasu helkwatar tsaro a babban birnin kasar.
‘Yanto fursunonin ya biyo bayan fitar da faifan bidiyo da sojojin Libiya da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar suka yi ne da ke nuna lokacin da aka ‘yantar da fursunonin. Hotunan sun nuna akwai dakunan tsare mutane ba bisa ka’ida ba da kuma gidajen yari da ake amfani da su a cikin hedkwatar hukumar, wanda ya wuce ikon hukumomin shari’a na kasa.
A wani labarin kuma, Fira Ministan gwamnatin hadin kan kasa, Abdul Hamid Dabaiba, ya fitar da kuduri mai lamba (226) na shekara ta 2025, dangane da kafa kwamitin gaggawa da zai binciki yanayin gidajen yari da na tsare tsare a kasar, biyo bayan wadannan bayanai masu ban mamaki.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a gidajen yari
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Yi Luguden Bama-Bamai Kan Falasdinawa Da Suka Janyo Shahada Da Jikkata
Falasdinawa da dama ne suka yi shahada yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani sabon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna na Gaza
Fararen hula Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata wasu masu yawa sakamakon kazamin harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna a zirin Gaza tun da sanyin safiyar Laraba.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa: Akalla fararen hula 6 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata a lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai harin bama-bamai a kan tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin Al-Mawasi da ke Khan Yunis. Sannan wasu Fararen hula 10 da suka hada da kananan yara suka sami raunuka, wanda ake ganin yanki ne mai aminci ga iyalan da suka rasa matsugunansu. Duk da haka, an sha kai hare-haren bama-bamai kansa a cikin ‘yan makonnin nan.
Shaidun gani da ido sun kara da cewa; wasu Falasdinawa hudu ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon harin da ‘yan mamaya suka kai wa wani gida na dangin Zeno da ke titin Jaffa a tsakiyar birnin Gaza.