2025-05-18@16:16:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4665
«a ƙoƙarin»:
Wani mutum da ake nema ruwa a jallo bisa zargin garkuwa da mutane an kama shi a sansanin alhazai da ke Abuja. Wata majiya daga jami’an tsaro ta tabbatar wa wakilinmu cewa an kama wanda ake zargin, mai suna Yahaya Zango, yayin da ake tantance takardun maniyyatan da ke shirin tafiya Ƙasar Saudiyya domin aikin Hajjin bana. ’Yan sanda sun ceto tsohuwa mai shekara 80 a hannun ’yan bindiga a Jigawa.Shin PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta nan da zaɓen 2027? Rahotanni sun bayyana cewar Zango yana zaune ne a unguwar Paikon-Kore da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gwagwalada a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Jami’an tsaro sun bayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo saboda zarginsa da hannu...

Kafofin Yada Labarai Na Amurka Sun Bayyana Kuzari Da Ci Gaban Da Fina-finan Kasar Sin Ke Samu A Bikin Cannes
Kamar yadda mujallar ta bayar da rahoto a kai, rumfar fina-finai ta kasar Sin ta zama wata alama da ke nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kyautata cudanyar al’adu da hadin gwiwar kasa da kasa a harkar fina-finai. Kana, bisa samun karuwar jawo hankulan kasashen duniya da kuma kafa kwakkwarar turbar fasahar kirkira ta gwaninta da iya tsara labarin fim, sashen fina-finan na kasar Sin ya mike haikan wajen taka rawa sosai a duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Aƙalla mutane bakwai sun mutu yayin da wasu 11 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a ƙauyen Essa da ke kan hanyar Agaie-Badeggi, ƙaramar hukumar Katcha, jihar Neja. Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa motar ɗauke da hatsi ta gwamnatin tarayya ce, kuma fasinjojinta maza ne kimanin 36, daga Legas zuwa Kano. Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato An Tsinci Gawarwakin Yara Biyar Cikin Tsohuwar Mota A Nasarawa Hatsarin ya faru ne da ƙarfe 3 na daren ranar Lahadi, lokacin da direban ya yi ƙoƙarin ƙetare wani ɓangare mara kyau na hanyar da ake ginawa. Daraktan hukumar kula da sufuri na Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar...
Aƙalla mutane bakwai sun mutu yayin da wasu 11 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a ƙauyen Essa da ke kan hanyar Agaie-Badeggi, ƙaramar hukumar Katcha, jihar Neja. Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa motar ɗauke da hatsi ta gwamnatin tarayya ce, kuma fasinjojinta maza ne kimanin 36, daga Legas zuwa Kano. Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato An Tsinci Gawarwakin Yara Biyar Cikin Tsohuwar Mota A Nasarawa Hatsarin ya faru ne da ƙarfe 3 na daren ranar Lahadi, lokacin da direban ya yi ƙoƙarin ƙetare wani ɓangare mara kyau na hanyar da ake ginawa. Daraktan hukumar kula da sufuri na Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta ceto wata tsohuwa mai shekaru 80 da aka sace a Jihar Kano, bayan wani samame da suka kai Ƙaramar Hukumar Garki. A yayin samamen, sun kashe mutane biyar da ake zargi masu garkuwa da mutane ne, sannan sun kama wasu biyar. Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso Rahoton ya ce samamen ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar 16 ga watan Mayu, 2025 bayan samun sahihan bayanan sirri. Waɗanda suka sace tsohuwar, Hajiya Hajara daga Ƙaramar Hukumar Minjibir, a Jihar Kano, su 12 ne ɗauke da bindigogi, kuma sun zo ne a kan babura. Rundunar ta haɗa...
Yanayin da ’ya’yan shugabanni suke yin fito-na-fito da masu ƙalubalanta ko yin tambaya a kan abubuwa ko matakan da iyayensu suka ɗauka, sai ƙara muni yake yi a fagen siyasar Najeriya. Abin da da ke ƙara zama ruwan dare a Najeriya shi ne yadda a duk lokacin da mutane suka tambayi shugabanni ko suka ƙalubalanci wani aiki ko mataki da suka ɗauka ko abin da suka faɗa, ’ya’yan shugabannin ke fito su yi ɓaɓatu, wani lokaci ma har da cin mutunci. Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso Shin PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta nan da zaɓen 2027? Yaran suna zargin masu neman bayanin, kamar saɓo suka yi, sun manta cewa a matsayin iyayensu na...
Yanayin da ’ya’yan shugabanni suke yin fito-na-fito da masu ƙalubalanta ko yin tambaya a kan abubuwa ko matakan da iyayensu suka ɗauka, sai ƙara muni yake yi a fagen siyasar Najeriya. Abin da da ke ƙara zama ruwan dare a Najeriya shi ne yadda a duk lokacin da mutane suka tambayi shugabanni ko suka ƙalubalanci wani aiki ko mataki da suka ɗauka ko abin da suka faɗa, ’ya’yan shugabannin ke fito su yi ɓaɓatu, wani lokaci ma har da cin mutunci. Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso Shin PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta nan da zaɓen 2027? Yaran suna zargin masu neman bayanin, kamar saɓo suka yi, sun manta cewa a matsayin iyayensu na...
Hukumar kula da al’adun gargajiya ta kasar Sin ta bayyana cewa, gidajen tarihi na sassan kasar sun gudanar da bukukuwan nune-nunen kayayyaki 43,000, da tarurrukan ilimi 511,000. An bayyana wadannan alkaluman ne a yau Lahadi a wani bikin tunawa da ranar gidajen tarihi ta duniya a gidan adana kayayyakin tarihi na babban mashigin ruwa wato Grand Canal a Beijing. A cikin shekarar 2024, an yi rajistar sabbin gidajen tarihi 213 a kasar Sin, inda hakan ya kara yawan adadin gidajen tarihi na kasar zuwa 7,046, kamar yadda hukumar kula da su ta bayyana. Kazalika, ta kara da cewa, kasar Sin tana kara fadada manufofinta na shiga gidajen tarihi ba tare da biyan kudi ba, inda sama da kashi 91 cikin...
A wancan lokacin, Sarkin Abuja shi ne Marigayi Sulemanu Barau, wanda ya rasu a shekarar 1979. Saboda hikimarsa da hangen nesa, ya ga cewa zai fi dacewa mutanensa su samu ‘yanci da asali ta hanyar kasancewa cikin wata jiha a kasar tarayya, fiye da su kasance a cikin wani yanki da ake kira kasar kowa ba tasa ba, kamar yadda ake kallon FCT a yanzu. A sakamakon haka, kashi 80 cikin dari na kasar da ke karkashin Masarautar Abuja da sunanta gaba-daya, aka mika wa gwamnatin tarayya domin gina FCT. Wannan kaso ya yi daidai da 80 cikin dari na jimillar fadin FCT a yanzu. Sauran kashi 20 cikin dari kuwa, an samo su ne daga tsohuwar Jihar Filato da...
Gwamnati dai ta nisanta kanta daga labarin na karya, inda ta kwatanta batun da cewa, “mai tada hankali da rashin izini”. Gwamnatin jihar ta kuma gargadi dukkan masu rike da mukaman siyasa da su daina bayyana ra’ayoyinsu da sunan Gwamnati kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi siyasa ba tare da tantancewa ba. LEADERSHIP ta fahimto cewa, wannan matakin ya biyo bayan wani labari ne da aka yada da cewa, Sanata Kwankwaso ya ki amincewa da tayin da shugaba Tinubu ya yi masa na tsunduma shi cikin jam’iyyar APC, inda ake zargin Sanatan ya bayyana cewa, ya gwammace ya bar siyasa maimakon ya koma jam’iyya mai mulki. Ba da dadewa ba, wannan labarin na karya ya samu...
Shugaban karamar hukumar Kaiama, Honarabul Abdullah Danladi ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Lahadi yayin wata tattaunawa da LEADERSHIP ta wayar tarho. Danladi ya ce ya jagoranci tawagar gwamnati domin jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa. Ya kara da cewa, gwamnati za ta kafa wani kwamiti wanda za a dora masa alhakin tilasta wa fasinjojin jirgin ruwa yin amfani da rigar tsira don dole. Danladi ya ce gwamnati za ta kuma dakatar da tafiye-tafiye da daddare a wani bangare na matakan kawo karshen yawaitar haduran Kwale-kwale da ake fama da shi a yankunan da ke zagaye da ruwa. Shi ma mai martaba Sarkin Kaiama, Alh Muazu Omar ya nuna alhininsa kan wannan lamari da ya...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin dakatar da wani hadiminsa, Ibrahim Rabi’u nan take daga muƙaminsa. Abba ya dakatar da hadimin ne wanda yake ɗauko masa rahoto a ma’aikatar sufuri, saboda wasu kalamai da ya furta kan tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Kwale-kwale ya nutse da mutum 37 a Kwara Ainihin abin da ya faru da ɗan wasan Nijeriya Taiwo Awoniyi Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Asabar, 17 ga watan Mayun 2025. Dawakin Tofa ya ce Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ne ya fitar da sanarwar dakatarwar, wadda ta fara aiki nan take. Baya ga haka, gwamnatin...
Iran ta yi kira da a kawo karshen neman shafe wata al’umma daga kan doron kasa tare da kawo karshen rashin hukunta shugabannin ‘yan sahayoniyya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan hare-hare da laifukan da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take ci gaba da yi a cikin ‘yan kwanakin nan a zirin Gaza, yana mai kira da a kawo karshen kisan kiyashi da rashin hukunta shugabannin gwamnatin ‘yan shayoniyya da kuma gurfanar da su a gaban kuliya don hukunta su. Baqa’i ya yi ishara da laifuffukan da ba a taba ganin irinsa ba da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta yi kan al’ummar Falastinu da ba su da kariya a Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan, ya...
Wani hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 37 a ƙauyen Gbajibo-Mudi da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara. Hatsarin wanda ake fargabar ya auku ne a sanadiyar ɗaukar fasinjoji fiye da kima ya faru ne da yammacin ranar Alhamis da ta gabata. Shin PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta nan da zaɓen 2027? Ainihin abin da ya faru da ɗan wasan Nijeriya Taiwo Awoniyi Lamarin na zuwa ne watanni bakwai bayan aukuwar makamancinsa wanda ya janyo asarar fiye da mutum 106 a jihar. A cewar wani mazaunin yankin, kwale-kwalen wanda ya ɗauko fasinjoji kimanin 150 ya kife ne a tsakiyar ruwa. Bayanai sun ce waɗanda lamarin ya rutsa da su na komawa gida ne bayan cin kasuwa a tsallake...
Hukumomin kasar za su fitar da gamsasshen bayani mai dauke da sababbin tsauraran matakan, wadanda za su kunshi na mallakar izinin karatu da aiki a Birtaniya. Sakataren harkokin baki na Birtaniya Ybette Cooper ta bayyana wa BBC cewa lokaci ya yi da za su rage daukar ma’aikatan jinya daga kasashen waje. Ta ce wannan matakin zai taimaka wajen rage kusan mutum 50,000 wadanda ba kwararru ba ne sosai da suke shiga kasar daga kasashen ketare a duk shekara. Firaministan ya ce sababbin matakan za su taimaka wajen “sake mallake bakin iyakokin kasarmu.” Idan aka dabbaka sabbin matakan nan da gwamnatin kasar za ta dauka, ‘yan kasashen mutane daga kasashen Nijeriya da Pakistan da Sri Lanka za su fuskanci kalubale wajen...
An zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutane 3 da ake zargi da kai harin ta’addanci a hubbaren Shah Cheragh Shugaban hukumar shari’a ta lardin Fars (a kudancin Iran) ya sanar da cewa: Kotun Musulunci a birnin Shiraz ta yanke hukunci kan wasu mutane 7 da ake tuhuma da hannu a harin ta’addancin da aka kai a hubbaren Shah Cheragh (Ahmad ibn Imam Musa al-Kazim, amincin Allah ya tabbata a gare shi). Haka nan kuma yayin da yake ishara da hukuncin da aka yanke wa mutanen bakwai da suka kai harin ta’addanci a hubbaren Shahragh, Hujjat al-Islam Sayyid Sadrullah Raja’i Nasab ya ce: A cikin hare-haren ta’addancin da aka kai a hubbaren Shahragh, baya ga manyan wadanda suka kai...
Sojojin Yemen sun kai hari filin jirgin saman Ben Gurion da makami mai linzami guda biyu da kuma jirgin sama mara matuki ciki Sojojin Yemen sun sanar a yau Lahadi cewa: Sun kai hari kan filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makamai masu linzami guda biyu da kuma jirgin sama maras matuki ciki. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta bayyana cewa: Sojojin Yemen sun kai hari da makami mai linzami kan filin tashi da saukar jiragen sama na Ben Gurion da ke Jaffa da makami mai linzami guda biyu, daya daga cikin makami mai linzami na Falastinu 2 da kuma makami mai linzamin Dhu al-Fiqar....
Dare da aka zubar da jini mafi muni a Gaza: Sama da Falasdinawa 80 ne suka yi shahada a sassa daban-daban na Zirin Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula a yankuna daban-daban na zirin Gaza, inda suka yi sanadiyyar shahadan sama da Falasdinawa 80, kuma mafi yawansu a wani kisan kiyashi da aka yi wa ‘yan gudun hijira a yankin Al-Mawasi na Khan Yunus da ke kudancin zirin Gaza, bayan da aka jefa bama-bamai da kona tantunansu a kusa da Asibitin kwararru na Kuwait, baya ga kisan kiyashi a duk fadin yankin. Majiyoyin Falasdinawa sun ce an kona mutane 36, yawancinsu mata da kananan yara, bayan da sojojin mamayar Isra’ila suka yi...

Sojojin Libiya Sun ‘Yantar Da Fursunoni Daga Gidajen Yarin Sirri Da Ake Tsare Da Su Ba Bisa Ka’ida Ba
Sojojin Libiya sun ‘yantar da fursunoni da dama daga gidajen yari na sirri da ke karkashin dakarun Tallafawa da Wanzar da Kwanciyar hankali na Kasar Sojojin kasar Libya a birnin Tripoli fadar mulkin kasar sun ‘yantar da fursunoni da dama da ake tsare da su a gidajen yari na sirri karkashin hukumar “Tallafawa da wanzar da zaman lafiya” bayan sun kwace iko da wasu helkwatar tsaro a babban birnin kasar. ‘Yanto fursunonin ya biyo bayan fitar da faifan bidiyo da sojojin Libiya da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar suka yi ne da ke nuna lokacin da aka ‘yantar da fursunonin. Hotunan sun nuna akwai dakunan tsare mutane ba bisa ka’ida ba da kuma gidajen yari da ake amfani da su...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sauran sassan da aka gyara da kuma saka kayan aiki sun haɗa da sashen Kulawa da Mata (ANC), ɗakin tiyata, ɗakin X-ray, sabon ginin hukunta asibiti, masallaci, gidan Babban Daraktan Lafiya (gidaje mai ɗakuna 3), da kuma sashen kula da yara, da dai sauransu. A yayin jawabinsa a wajen ƙaddamar da aikin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, an kammala gyaran gine-ginen tare da sanya dukkan kayan aikin kiwon lafiya cikin kwangilar cikin watanni 12. Gwamnan ya ce, “A shekarar da ta gabata ne aka fara gyaran wannan asibitin, kuma wani kamfanin cikin gida ne aiwatar da kwangilar. “Saba hannun jarin ya mayar da asibitin zuwa wurin kiwon lafiya na zamani tare da na’urori na zamani, wannan ba...
An yi wa ɗan wasan gaba na ƙungiyar Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi allurar barci mai nauyi domin taimaka masa murmurwa daga tiyatar da aka yi masa. Bayanai sun tabbatar cewa an garzaya da ɗan wasan ɗan asalin Nijeriya asibiti ne domin yi masa tiyata a ranar Litinin, bayan ya samu mummunan rauni a cikinsa a wasan da suka tashi canjaras, 2-2 da Leicester a Gasar Premier ta Ingila. Motar da aka shekara 10 ana tara kuɗinta ta ƙone bayan awa 1 da sayen ta Shin PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta nan da zaɓen 2027? Alamu sun nuna cewa rayuwar ɗan wasan mai shekara 27 ba ta cikin haɗari, kuma allurar barcin da aka yi masa za ta taimaka ne...
A cewarsa, baban dalilin da ya sa suke wannan aiki shi ne, domin a rage wa al’umma musamman masu karamin karfi wahalwalun da suke sha wajen neman lafiya. Malam Hussaini ya yi kira ga sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da su ba da tasu gudummawa wajen irin wannan aiki ta yadda za su taimaka wa kokarin gwamanti kan harkokin kiwon lafiya. Wasu daga cikin wadanda suka amfana da wannan taimako na aikin kaba sun yaba da kokarin wannan gidauniya, inda suka ce hakan zai taimaka wa kokarin gwamanti da sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da su yi ko yi da wannan gidauniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Babbar Jam’iyyar hamayya ta PDP ta ce, ta soma ɗaukar matakan ɗinke ɓarakar da ta dabaibaye ta a ’yan shekarun nan. Matakin baya-bayan nan shi ne na taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar ta gudanar. Guguwar raba Masarautar Katsina ta kunno kai Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma Shin ko hakan zai kawo ƙarshen matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan faɗuwa zaɓen 2023? Daga cikin matsalolin da suka kunno kai a cikin babbar Jam’iyyar adawa ta PDP tun bayan faduwarta zaɓe a 2023 shi ne yin baram-baram a kan yadda za ta dinke barakar da aka samu a lokacin zaben fidda-gwani da rikicin shugabanci a matakai daban-daban da kuma kasa tsayawa da kafarta domin samar...
Bayan da wani matashi ɗan shekara 33 ɗan kasar Japan mai suna Honkon ya yi tarin kuɗi na tsawon shekaru 10 don siyan motar da yake mafarki — na wata sabuwar mota ƙirar Ferrari 458 Spider — sai ya zauna yana kallon yadda motar take ƙonewa cikin sa’a ɗaya da tuƙa ta a karon farko. Kafofin sada zumunta na ƙasar Japan sun yi sharhi game da rahoton baƙin ciki na Honkon, matashin da ya kasance mai shirya wakoki, wanda ya kashe makudan kuɗi game da mafarkin sayan motarsa ta Ferrari, sai dai ya kalle ta tana ci da wuta a ranar da ya tuƙa ta a karon farko. ISWAP ta kashe manoma sama da 50 a Borno Guguwar raba Masarautar...

Kyakkyawan Tunanin Kwankwaso Na Kafa Jami’ar Kimiyya Ta Wudil Ta Zama Alkairi Ga Al’umma – Alhaji Abdukadir
Ya ce da Kwankwaso bai yi tunanin samar da jami’ar Wudil ba, da wannan alherin ba za a same shi ba, suna gode wa sauran wadanda suke ba da gudummawa wajen habakar wannan jami’ar. Alhaji Abdukadir ya yi kira ga magoya baya da masu tasowa cewa idan suka sami dama su yi koyi da jagoran Kwankwasiyya, wanda ya kafa jami’o’i guda biyu a Jihar Kano bayan makarantu na gaba da sakandare guda 24 da ya samar da kuma tura dalibai talakawa karatu kasashen waje da mafi yawa sun gama suna amfanar da ci gaban al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya caccaki kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan a ziyarar da ya kai a kasashen yankin Gulf na Farisa, yana mai cewa kalaman abin kunya ne a gare shi da dukkan Amurkawa, kuma bai cancanci amsa ba. Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar masu bayar da ilimi daga sassan kasar. Ya kara da cewa wasu kalaman na Trump ba su ma isa a mayar da martani ba, yana mai kiransu da cewa abin kunya ne ga shi kansa shugaban Amurka da kuma wulakanci ga al’ummar Amurka. ‘’Ikirarinsa na cewa yana son samar da zaman lafiya da tsaro, zencen...
An gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu a sassa daban-daban na duniya, a yayin zagayowar cika shekaru 77 da ranar ‘’Nakba’’ cewa da masifa. A Faransa da Ingila duk an gudanar da wannan zanga zanga a wasu sassan kasar. A cikin jerin gwanon, an daga allunan da ke dauke da sakonni irin su “Falasdinu za ta rayu!” » ko “Dakatar da kisan kiyashi a Gaza”. “Nakba ba wani lamari ne da ya faru a baya ba, yana ci gaba da faruwa ta hanyar korar jama’a, da amfani da bama-bamai,” kan al’ummar Gaza. Masu zanga-zangar sun yi Allah wadai da tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza tun bayan barkewar yakin kisan kiyashi da Isra’ila ta kaddamar a...
Iran ta yi kakkausan suka game da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa kan kasar Yemen tana mai danganta su da babban laifin yaki. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa hare-haren da gwamnatin Isra’ila ke kai wa kan ababen more rayuwa na tattalin arzikin kasar Yemen da kuma cibiyoyin jama’a sun zama “laifi na yaki da cin zarafin bil’adama.” A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Asabar, Esmail Baghai ya yi kakkausar suka kan hare-haren da gwamnatin Isra’ila ke kaiwa kan manyan tashoshin jiragen ruwa na kasar Yemen. Ya kara da cewa hare-haren da aka kai a tashar jiragen ruwa ta Hudaydah, Ras Issa da kuma Salif na kasar Yemen, ya zama babban...
Kasar Faransa ta mika iko na sansanin soja na Contre-Amiral Protet ga kasar Senegel, wanda shi ne sansanin soja na 3 da aka mikawa kasar a bana. An mika sauran sansanoni biyu da suka hada da Marechal da Sanit-Exupery ne a watan Maris din da ya gabata, Kuma dukkan sansanonin na da mazauni ne a Dakar, babban birnin Senegal. Wata sanarwa da ofishin jakadancin Faransa ya fitar, ta ce an tsara mika dukkan wasu sansanonin dake karkarshin ikon Faransa a Senegal a bana, biyo bayan yarjejeniyar da kasashen biyu suka yi. A ranar 31 ga watan Disamban 2024, shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya sanar a jawabinsa na sabuwar shekara cewa, za a bukaci dakarun Faransa su fara janyewa daga...
Wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yeman ya fada a yankuna Falasdinawa da aka mamaye. Yemen ta jima da take kai hare-hare kan Isra’ila a matsayin nuna goyan baya ga al’ummar Gaza dake fuskantar mamaya da ukuba da kisan kare dangi daga Isra’ila. A cikin bayanin da ya yi bayan harin, babban jami’in gwagwarmayar Ansarullah ta kasar Yemen Nasr al-Din Amer, ya yi ishara da yadda gwamnatin Isra’ila ta yi watsi da kiran da kasashen Larabawa suka yi na neman zaman lafiya, ya kuma jaddada cewa hare-haren da ke faruwa a yankunan da aka mamaye, shi ne yare daya tilo da gwamnatin Isra’ila ke fahimta. Hare-haren na Yemen sun yi matukar tasiri wajen durkusar da tattalin arzikin...
A farkon wannan sati ne wata takardar neman raba Masarautar Katsina ta bayyana, wadda take neman a ƙirƙiro ƙarin masarautu uku da suka haɗa da ƙarin sarki mai daraja ta ɗaya da mai daraja ta biyu da kuma mai daraja ta uku. Takardar wadda aka gani da tambarin da ke nuna alamar an miƙa ta ga Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta tayar da ƙura, inda ake ta musayar yawu kan abin da ta ƙunsa da kuma abin da zai iya biyo baya. Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma ISWAP ta kashe manoma sama da 50 a Borno Wakilinmu ya gano cewa takardar, wadda kafar yaɗa labarai ta Katsina Times ta fara wallafa wa a kafofin sada zumunta,...
Shugaban Hukumar Kula da Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya karɓi tawagar jami’an Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) tare da kamfanin Max Air domin duba kayayyakin aikin hukumar. A jawabinsa, mataimakin mai kula da ofishin hukumar da ke Kano, Mista Barnabas Anderson, ya ce manufar wannan ziyarar ita ce don yin binciken gaggawa da tabbatar da ingancin kayan aikin hukumar kula da alhazai ta jihar. Ya ƙara da cewa, tawagar ta tantance kayan aiki, shirin jigilar maniyyata na jihar, takardun tafiya, fasfo da kuma kayan aikin sansanin Alhazai. Ya bayyana cewa, za a yi jigilar rukuni na farko na maniyyata 550 daga jihar Jigawa zuwa kasa mai tsarki a ranar 20 ga watan...
Aƙalla manoma 50 ne suka rasu, sakamakon wani mummunan hari da ‘yan ta’addan ISWAP suka kai garin Malam Karanti da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa, a jihar Borno. Majiyoyi sun ce mayaƙan sun afka wa manoma yayin da suke noma da kamun kifi, duk da cewar suna biyan haraji kafin yin noma. Tinubu ya isa Rome don rantsar da sabon Fafaroma Tsafta a gidan aure: Abubuwan da kowace mace ya kamata ta sani “Sun mallaki takardun izini daga kwamandan ISWAP da ke kula da yankin Malam Karanti har zuwa Dawashi. Sun jima suna samun kariya daga Amir Akilu, wanda shi ne kwamandan yankin,” in ji wani mazaunin yankin. Sai dai harin ya faru ne a lokacin da kwamandan bai kasance a...
Hukumar kula da ayyukan sama jannati ta kasar Sin ta ce masu bincike sun tabbatar da wata sabuwar halitta da aka samu a cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, wanda aka yi wa lakabi da Niallia Tiangongensis A watan Mayun 2023 ne, tawagar ‘yan sama jannati ta kumbon Shenzhou-15 ta gano wani samfurin halitta a cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin yayin da take cikin da’irarta. An kuma adana ta cikin yanayi mai sanyi, sannan daga bisani aka kawo ta duniyar dan Adam domin gudanar da nazari. Kuma bayan binciken kimiyya da ya shafi nazarin sauyawar yanayinta da tsarin kwayar halittarta da sauransu, masana sun tabbatar da cewa sabuwar halitta ce da ba a taba...
Yanzu haka, ƙungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta za ta kammala kakar ba tare da lashe kofi ba. A wannan kakar kuwa, Liverpool ce ta lashe gasar Firimiya, yayin da Real Madrid ta fitar da Manchester City daga gasar Zakarun Turai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Farfesa Radda ya ce an cire ‘yan takara masu yawa da suka cencenta saboda rashin adalci, duba da cewa sun cika dukkan sharadan da ya dace wajen neman mukamin shugabancin makarantar. Haka kuma, Farfesa Bichi ya ce zargin da ake masa ba gaskiya ba ne, yana mai cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci kamar yadda doka ta tanada. Dukkan ‘yan takarar sun bayyana gamsuwarsu kan shigowar gwamnatin tarayya cikin lamarin, inda suke yi kira ga ministan ilimi ya sake duba dukkan matakan da da aka bi domin yin gaskiya kamar yadda dokar makarantar ta tanada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Amma mu tambayi kanmu, shin da gaske wannan ita ce hakikanin manufar? Amma bari mu yi la’akari da wannan hasashen mu gani, ko shi ne ya fusata Amurka ta maka harajin kashi 100 bisa 100 kan fina-finai da ake shigar da su daga kasashen waje ko kuma wadanda aka shirya a ketare? Akwai wani kirkirarren fim mai suna ‘Ne Zha 2’ da masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta shirya a baya-bayan nan. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, wannan fim ya zama na farko da ya samar da Dala biliyan 1 a kudin tikitin shiga a kasuwar cikin gida kadai. Bugu da kari, wannan adadi, ya haura sama da Dala biliyan 2 a kudaden shiga...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya isa birnin Rome na Ƙasar Italiya domin halartar bikin rantsar da sabon Fafaroma, Leo na XIV. Za a gudanar da bikin ne a wajen wani taron addu’a da ake kira “solemn mass” a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu. Crystal Palace ta lashe kofin FA na farko a tarihinta Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — Kwankwaso An tarbi Shugaba Tinubu a filin jirgin sojin Mario De Bernardo, inda jakadiyar Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da jami’an diflomasiyya daga Vatican da ofishin jakadancin Najeriya suka tarbe shi. Tinubu ya samu gayyata ta musamman daga Sakatare Janar na Vatican, Cardinal Pietro Parolin. A cikin wasiƙar gayyatar, Fafaroma Leo XIV ya bayyana cewa ya...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga shugaban Iraqi Abdul Latif Rashid, wanda kuma shi ne shugaban karba-karba na majalisar shugabannin kasashen kungiyar Larabawa, tare da taya murnar kaddamar da babban taron kungiyar na 34, a birnin Baghdad na Iraqi. Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru sama da 80 da kafata, kungiyar kasashen Larabawa ta kasance mai mayar da hankali kan inganta hadin kai da karfafa yankin Larabawa da furta matsalolin kasashen da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya. Ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take ta hada hannu da kasashen Larabawa wajen zurfafa aminci da ingiza hadin gwiwar moriyar juna da kara musayar...
Farfesa Radda ya ce an cire ‘yan takara masu yawa da suka cencenta saboda rashin adalci, duba da cewa sun cika dukkan sharadan da ya dace wajen neman mukamin shugabancin makarantar. Haka kuma, Farfesa Bichi ya ce zargin da ake masa ba gaskiya ba ne, yana mai cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci kamar yadda doka ta tanada. Dukkan ‘yan takarar sun bayyana gamsuwarsu kan shigowar gwamnatin tarayya cikin lamarin, inda suke yi kira ga ministan ilimi ya sake duba dukkan matakan da da aka bi domin yin gaskiya kamar yadda dokar makarantar ta tanada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Crystal Palace ta doke Manchester City da ci ɗaya mai ban haushi a filin wasa na Wembley a ranar Asabar, inda ta lashe Kofin FA karo na farko a tarihinta. Eberechi Eze ne, ya zura ƙwallo ɗaya tilo tun da aka fara wasan, yayin da mai tsaron ragar Crystal Palace, Dean Henderson ya taka rawar gani a wasan wajen hana Man City zura ƙwallo. Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — Kwankwaso Hajj: Ranar Lahadi za a fara jigilar maniyyatan Katsina zuwa Saudiyya Man City ta rasa damar yin kunnen doki a wasan bayan Omar Marmoush ya kasa cin bugun daga kai sai mai tsaron raga. Henderson, ya tsallake rijiya da baya, bayan duba VAR kan...

Jagora: Jawaban Trump A Ziyar Da Ya Kai Wasu Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Abin Kunya Ne Gare Shi Ga Kuma Amurkawa
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yi watsi da wasu kalaman shugaban kasar Amurka Donal Trump a ziyar da ya kammala a wasu kasashen larabawa na yankin Tekun farisa, ya kuma bayyana wasu kalamansa a matsayin kungiya ga kansa da kuma mutanen Amurka. Har’ila yau Jagoran ya kara da cewa da dama daga cikin maganganunsa basu cancanci maida martani ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a yau Asabar, a lokacinda yake ganawa da wasu malaman makaransu daga larduna daban daban na kasar, a Husainiyyar Imam Khonaini (q) a nan Tehran. Jagoran ya kara da cewa : Trump yace yana son amfani da karfin da Amurka...

Iran: Aiwatarda Yarjeniyar Zaman Lafiya Tsakanin Armenia Da Arzerbaijan Zai Tabbatar Da Zaman Lafiya A Tsakanin Kasashen Biyu
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa aiwatar da yarjeniyar zaman zaman lafiya wadanda aka cimma tsakanin kasashen Armenia da kuma Azerbaijan da gaggawa zai tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto Aragchi yana fadar haka a lokacin ganawarsa da sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Armenia, Armen Grigoryan wanda yake ziyarar aiki a nan Tehran a yau Asabar. Ministan ya kara da cewa JMI zata tabbatar da cewa an aiwatar da sulhu tsakanin kasashen biyu da gaggawa saboda tana dasawa da kasashen biyu makobta gareta. A cikin watan Maris da ya gabata ne kasashen Armenia da Arzerbaijan suka amince a rubuta yarjeniyar...
A taron kasashen larabawa karo na 34Th wanda ake gudanarwa a birnin Bagdaza na kasar Iraki, shuwagabannin kasashen larabawa sun bukaci tsagaita wuta a gaza sannan sun yi kira da aka kafa kasar Falasdinu mai zaman kanta. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, shuwagabannin sun bukaci a magance matsalolin da suke faruwa a Siriya Lebanon da kuma sudan. Ana taron shuwagabannin kasashen larabwa a Bagdaza ne a dai dai lokacinda gwamnatin HKI take kara fadada hare-hare a kan zirin Gaza da kuma kashe Falasdinawa maza da mata da yara mutkar abinda zata iya kashewa. Majiyar kiwon lafiya ta Gaza ta bayyana cewa, ya zuwa yanzu sojojin HKI sun kashe falasdinawa kimani 53,272 mafi yawansu mata da...

Gidan Adana Kayayyakin Tarihi Na Amurka Ya Mayarwa Kasar Sin Rubuce-rubucen Hannu Masu Daraja Na Lokacin Yake-yake A Kasar
Cikin jawabin da ya gabatar ta bidiyo, mataimakin ministan kula da al’adu da yawon bude ido na kasar Sin Rao Quan, ya ce dawowar rubuce-rubucen na Wuxing Ling da Gongshou Zhan, na tabbatar da cewa za a iya nazarta da kare wadannan kayayyakin gargajiya masu daraja yadda ya kamata a mahaifarsu. (Fa’iza) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani babban jami’in kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza ya bada sanarwan cewa an fara tattaunawa da HKI ta kawo karshen wannan yakin a birnin doha ba tare da shimfida wasu sharudda ba. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto Taher Annunu daga daga cikin manya-manyan jami’an kungiyar ta Hamas yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa tattaunawar zata hada dukkan matsalolin da ke tsakanin bangarorin biyu. Annunu ya ce kungiyarsa zata gabatar da dukkan abubuwan da yakamata a tattaunawa a kansu kama daga tsagaita wuta, musayar fursinoni da kuma ficewar sojojin HKI daga Gaza. Majiyar HKI ta nakalto firai ministan HKI Benyamin Natanyahu yana cewa ya aika tawagar tattaunawarsa zuwa birnin Doha na kasar Qatar.
Kwanan nan ne Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoton dake sabunta hasashen yanayin tattalin arzikin duniya gami da makomarsa na shekara ta 2025 a tsakiyar shekarar da muke ciki, inda rahoton ke ganin kara harajin kwastam da rashin sanin tabbas game da manufofin cinikayya sun janyo tabarbarewar makomar tattalin arzikin duk duniya, tare da haifar da tarin kalubaloli ga kasa da kasa, musamman kasashe masu tasowa, ciki har da kasar Sin. Rahoton na hasashen cewa, saurin karuwar tattalin arzikin duniya na bana, zai ragu zuwa kaso 2.4 bisa dari, yayin da saurin karuwar cinikayya zai ragu zuwa kaso 1.6 bisa dari. Kana, rahoton na ganin cewa, daidaita manufofi gami da hadin-gwiwar kasa da kasa, na da muhimmanci gaya ga...
A makon da ya gabata, wasu ma’aikatan hukumar ilimi ta ƙaramar hukumar Damboa guda biyu sun mutu a irin wannan hari a hanyar Damboa zuwa Maiduguri. ’Yan ta’addan Boko Haram sun dawo da amfani da bama-bamai da suke birnewa a hanya domin kai hari kan matafiya da motocin da ke amfani da manyan hanyoyin Jihar Borno, abin da ya janyo asarar rayuka da dama a baya-bayan nan. A halin yanzu kuma, dakarun sojin Nijeriya na ci gaba da kai farmaki a dazukan Sambisa da sauran maɓoyar ’yan ta’adda a faɗin jihar domin murƙushe su da kawar da su gaba ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Kwamitin Haɗin Gwiwa na Jihar Kano kan Tsaro da Gyaran Matasa, ya kama ’yan daba 31 a wani samame da ya gudana a unguwanni bakwai a jihar. An kai samamen ne daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Mayu, 2025 ƙarƙashin jagorancin Dokta Yusuf Ibrahim Kofar Mata. Tsafta a gidan aure: Abubuwan da kowace mace ya kamata ta sani Jami’an tsaro sun daƙile harin Boko Haram sun kashe mayaƙa 5 a Borno Unguwannin da aka kai samamen sun haɗa da Ɗorayi, Ja’in, Sharada, Unguwar Dabai, Dukawa, Kabuga, Kofar Mata da sauransu, wuraren da suka yi ƙaurin suna wajen aikata laifuka. Daga cikin waɗanda aka kama, mutum 25 ana zargin ’yan daba ne, yayin da shida ake zarginsu dallacin miyagun ƙwayoyi....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsafta tana kasancewa wani muhimmin ɓangare na rayuwar mace. Duk da cewa galibi ana alaƙanta tsafta da kyawun gani ko ƙamshi, sai dai a zahirin gaskiya tsafta ta wuce gaban haka ce. Ita ce turbar zaman lafiya a gidan aure, makamin janyo soyayya, da ginshiƙin lafiyar jiki da tunani. Hajj: Ranar Lahadi za a fara jigilar maniyyatan Katsina zuwa Saudiyya Gwamnatin Kano ta haramta ‘Ƙauyawa Day’ a lokacin bikin aure Wasu matan na iya cika ido da kwalliya a wajen biki ko taro, amma su kan bar gidansu cikin ƙazanta da rashin tsafta. A wasu lokuta kuma, akwai matan da rashin tsaftarsu ke janyo mutuwar aurensu, rashin kulawa da miji, ko kuma sa mijin ya ɗauki matakin ƙaro aure. Tsafta...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina ta sanar cewa, za a fara jigilar maniyyatan jihar a ranar Lahadi 18 ga wannan wata na Mayu, 2025, zuwa Ƙasa Mai Tsarki. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Alhaji Badaru Bello Karofi, ya shaida wa wakilinmu, cewa maniyyatan da suka fito daga Malunfashi da Bakori, Ƙanƙara, Dandume, Ƙafur da Ɗanja sune rukunin farko da ake sa ran za su tashi daga filin sauka da tashin jiragen sama na Umaru Musa da ke cikin babban birnin jihar. Tun farko sai da jagoran mahajjatan jahar, wanda kuma shi ne mataimakin gwamnan jihar, Malam Faruk Joɓe ya bayyana cewar, gwamnatin jihar ta ɗauki duk wasu matakan da suka wajaba tun daga gida har zuwa Ƙasa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano, ta dakatar da dukkanin cibiyoyin gudanar da taro da ke faɗin jihar, tare da haramta gudanar da bikin ‘Kauyawa Day’ gaba ɗaya. Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne, ya bayyana hakan a ranar Asabar, bayan wata ganawa da masu ruwa da tsaki a jihar. ISWAP ta yi wa manoma 15 yankan rago a Borno Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo a Ribas Ya ce wannan mataki na cikin sabuwar doka da majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da ita, kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya sanya wa hannu. “Daga yanzu, duk wanda ya shirya wani taro da sunan Kauyawa ko Villagers Day, ya karya doka,” in ji El-Mustapha. Sabuwar dokar ta bai wa hukumar...
A Premier League, kungiyoyi sun gama sanin Man United ciki da waje. “Dalili shi ne su kan hadu sau biyu duk shekara. Sun san abin da za su tarar game da ‘yanwasan United din da kuma filin wasanta, a gasar zakarun Turai kuma, akasari wannan ne karon farko da suke zuwa filin wasa na Old Trafford da kuma karawa da United. Ba su san yadda ya kamata su tunkare su ba” in ji shi. Sai dai ya ce Manchester United dole sai ta yi da gaske a kan kungiyarTottenham saboda duka daga Ingila suka fito kuma sun hadu da su sau uku a wannan kakar duka Tottenham tana samun nasara kuma Tottenham din ta san lagon Manchester United sosai saboda...
Sojoji da mafarauta don halaka mayaƙan Boko Haram biyar tare da daƙile wani hari da ’yan ta’addan suka kai a ƙauyen Warambe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. Warambe na daga cikin yankunan da mazanaunansu suka dawo da zama a baya-bayan nan, kuma mayaƙan Boko Haram sun sha yin yunƙurin kurɗawa cikinsa. Shugaban mafarautan wanda ɗan asalin garin ne ya ce a safiyar Juma’a ne maharan suka nemi shiga ƙauyen, “amma muka gana su, muka kashe mutum biyar daga cikinsu. An miƙa makaman da muka ƙwato daga hannunsu ga sojoji.” Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Kudancin Borno, ya jinjina wa ƙoƙarin jami’an tsaron, musamman wajen ɗaukar mataki cikin gaggawa yana mai ba su ƙwarin gwiwar su ƙara...
Shugaban kasar Iran ya jaddadacewa: Sun yi Imani da tattaunawa, amma ba su jin tsoron duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Tabbas Iran tana gudanar da zaman tattaunawa da Amurka amma ba ta tsoron duk wata barazanarta, yana mai nuni da kalaman Trump da ke cin karo da juna, wani lokaci yana magana kan zaman lafiya sannan a wasu lokutan yana barazana da yaki. A jawabin da ya gabatar a wajen bikin cika shekaru biyu da samun nasarar tawagar “Rukunin Jirgin Ruwa na 86” na sojojin ruwan Iran, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yaba da sadaukarwar da jaruman da suka yi wannan hidimar, yana mai cewa: “Suna alfahari da kasancewar dakarunsu, yana mai...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Kiyaye ci gaba da sarrafa sinadarin yuraniyon da tushen kayan aikin makamashin nukiliya ba abubuwa ba ne da za a tattauna a kansu Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta samar da kwarin gwiwa dangane da ci gaba da zaman lafiya a shirinta na makamashin nukiliya, amma ba za ta iya tauye hakkin jama’ar Iran na halal da kuma hakkinsu na samar da makamashin nukiliya cikin lumana ba, ciki har da inganta sinadarin yuraniyom domin zaman lafiya ba. A wata ganawa ta hadin gwiwa da tare da tawagar babban taron kasa da kasa na Pugwash da hukumar makamashin nukiliya ta Iran ta shirya a yammacin...
Sai ya ce “Na riga na amsa wannan tambayar amma har yanzu kana sake maimaita ta. Idan dai za a iya tunawa, ‘yan jarida 43 mazauna Kaduna ne suka halarci taron, ciki har da wasu ‘yan jarida daga wasu jihohin da suka raka gwamnonin nasu. Don haka, ba daidai ba ne a ce na hana ‘yan jarida shiga taron gwamnonin Arewa. Duk jaridun kasar nan sun je a wurin. Duk gidajen rediyo da talbijin na Kaduna suna wurin. Duk wakilan manyan gidajen Talabijin da Rediyo da ke wajen Kaduna su ma suna nan. Kada ka dauki maganata a wani bangare daban, je ka bincika. Duk wadannan labarai ne irin na teburin mai shayi. Ni kuma ban sani ba. Abin da...
“Dangote ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba wanda ya cancanci yabo. Muna kan tattauna yadda za a kawo karshen rigimar. Nan gaba, za mu yi aikin hadin gwiwa domin tabbatar da samar da wadataccen mai ga al’ummar Nijeriya,” in ji shi. Ya nuna cewa ta hanyar zaman sulhu za su kawo karshen matsalar, “Nan gaba kadan ba za ku ji wata rigima tsakanin NNPCL da matatar mai ta Dangote ba. Za mu yi aikin hadin guiwa domin amfanuwar ‘yan kasa.” Ojulari ya kuma yi tsokaci kan faduwar farashin danyen mai a duniya a baya-bayan nan, wanda ya rage kudaden shiga da ake sa ran Nijeriya za ta samu. “Wannan raguwar ta shafi kasafin kudin Nijeriya tun da babban...
An tabbatar da mutuwar mutum uku tare da jikkatar wasu da dama sakamakon turmutsutsu a yayin wani taron rabon kuɗaɗen tallafi a garin Bama da ke jihar Borno. Wasu bayanai sun bayyana cewa ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya da UNICEF suka shirya rabon tallafin. Shaidun gani da ido sun ce, turmutsitsin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 8:00 na safe a makarantar firamare ta Kasugula, daya daga cikin cibiyoyin bayar da tallafi da aka kebe a garin Bama. Rahoton na nuni da cewar waɗanda suka ci gajiyar shirin sun taru ne domin karɓar tallafin kuɗi na naira 28,500 kowannensu. Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo a Ribas Budurwa ta guntule mazakutar saurayinta da cizo...
Habakar matsayi na kasafin kudi ya inganta a cikin 2024, ta hanyar habaka kudaden shiga. Gibin kasafin kudi ya ragu daga kashi 5.4 na kudin shiga a shekarar 2023 zuwa kashi 3.0 na kudin shiga a shekarar 2024, babban ci gaban da aka samu sakamakon karuwar kudaden shiga na daukacin tarayyar kasar, wanda ya karu daga naira tiriliyan 16.8 a shekarar 2023 (7.2 na kudaden shiga) zuwa kimanin naira tiriliyan 31.200. Rahoton ya kara da cewa hauhawar farashin kayayyaki ya tsaya tsayin daka amma ana sa ran zai fadi zuwa matsakaicin shekara da kashi 22.1 cikin 100 a shekarar 2025, yayin da tsayin daka mai tsayi ya tabbatar da amincin manufofin kudi tare da rage tsammanin hauhawar farashin kayayyaki. Ko...
Sai dai dan majalisar wakilai Ali Isah na (PDP, Gombe), bai amince da matsayin Madaki ba. Ya ce sanya shugaban kasa na a tsarin karba-karba a cikin kundin tsarin mulkin kasar zai samar da adalci da sanin ya kamata ga dukkan shiyyoyin siyasar kasar nan. Dan majalisa Sada Soli na (APC, Katsina), yayin da yake adawa da kudurin, ya ce dokar da aka gabatar “Na da illa sosai ga hadin kan kasa.” Ya ce sanya ka’idar shugabancin karba-karba a cikin kundin tsarin mulkin kasar zai kai ga samar da abubuwa bisa cancanta. “Hakan zai iya sanya muradun yanki da na kabilanci a gaba su zamo mafi cancanta. Zai karfafin zabin mutanen da za su iya tsayawa takara kuma zai kara...
Wata mata da age zargin ta cije mazakutar saurayinta ta shiga hannun ’yan sanda. Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta kama matar mai shekara 43 ne bayan ta yi wa masoyin nata wannan aika-aika ne a lokacin da suke rikici a cikin gida a unguwar Mile 3 da ke yankin Diobu a garin Fatakwal babban birnin jihar. Lamarin wanda ya afku a ranar Alhamis, ya girgiza mazauna titin Bishop Okoye mai yawan jama’a lokacin da aka samu labarin lamarin. A cewar majiyoyi, rikicin ya fara ne lokacin da masoyin matar ya nemi kwanciya da ita. An bayar da rahoton cewa matar ta ƙi amincewa da buƙatar saurayin nata, inda ta zarge shi da yin amfani da ƙwayoyin masu ƙara kuzarin...
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza ya kai 53,119 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023. Adadin ya karu ne sakamakon wasu hare-haren Isra’ila na baya baya nan wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 93 wayewar safiyar Juma’a. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, ma’aikatar ta ce an kuma mika wasu mutane fiye da 200 da suka jikkata zuwa asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a zirin Gaza, biyo bayan hare-haren wuce gona da iri da sojojin Isra’ila suka kai a yankuna da dama. A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an sami rahoton mutuwar mutane 109 da...
“Amma sai ku ga cewa daya bayan daya, mun magance yawancin wadannan matsalolin. Har yanzu akwai sauran aiki a gabanmu, amma muna kan samun nasarori.” Da yake jawabi a wajen taron, wakilin AON, Obiora Okonkwo ya yi maraba da wannan sabon ci gaban, inda ya bayyana cewa zai inganta ayyukansu. A cewarsa, “Abin da muke gani a nan a yau wani babban ci gaba ne daga jerin abubuwa da dama.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Iran da kasashen turan nan guda uku sun da ake wa lakabi da E3 sun kudiri anniyar bin hanyoyin diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar kasar ta Iran. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa, Iran da kasashen Turan uku Birtaniya da Faransa da Jamus (EU-3) sun kuduri aniyar yin amfani da diflomasiyya dangane da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Gharibabadi ya bayyana hakan ne a shafinsa na X bayan ganawarsa da wakilan kasashen Turan uku na yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015 a birnin Istanbul na kasar Turkiyya. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-Ravanchi shi ma ya halarci taron. Ya ce, wakilan...
Gwamnatin Isra’ila ta yi barazanar kashe jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Abdul-Malik al-Houthi, idan har Sana’a ta ci gaba da kai hare-hare da makami mai linzami kan Isra’ilar don goyon bayan Falasdinu. Ministan harkokin soji na gwamnatin, Isra’ila Katz ya ce idan har Yemen ta ci gaba da ayyukanta “za su sha azaba mai radadi.” Katz ya ce kisan da gwamnatin za ta wa al-Houthi zai yi kama da kisan gilla kan “Deif da Sinwars a Gaza.” Ministan na Isra’ila yana magana ne a kan tsohon kwamandan kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da ke Zirin Gaza, Mohammed Deif, wanda gwamnatin kasar ta sanar da kashe shi a watan Janairu. Katz ya kuma ce yuwuwar nasarar kisan gillar da gwamnati...
Adadin kudaden harkar soji a nahiyar Afirka a bara, musamman a Aljeriya da kasashen kawancen Sahel, ya karu. A cewar wani bincike da Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya ta Duniya ta Stockholm (SIPRI) ta gudanar, kashe kudaden soji a Afirka ya karu zuwa dala biliyan 52.1 a shekarar 2024 a fadin Nahiyar, wanda ya karu da kashi 3 bisa 100 a shekarar 2023 da kuma karuwar kashi 22 cikin 100 a shekarar 2015. A cewar rahoton na SIPRI, kudaden da ake kashe wa sojojin na Arewacin Afirka ya kai dala biliyan 30.2 a shekarar 2024, ya kuma karu da kashi 4 cikin 100 a shekarar 2024. Kudaden da Aljeriya da Maroko kadai suka kashe ya kai kashi 90% na adadin kudaden...
A lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa da hawansa mulki a watan Mayun 2023, ya ci karo da tsarin kiwon lafiya da ya tabarbare saboda rashin kulawa. Ya ce, “Gwamnatinmu, ƙarƙashin ginshiƙan shirye-shiryen ceto, nan da nan ta fara tantance abubuwan da asibitoci ke buƙata, inda sakamakon ya zama abin tsoro kuma ya nuna akwai jan-aiki. “Alal misali, a jihar da ke da mutane kusan miliyan 6 tare da tarin ƙalubale, na’urar duban ɗan tayi ɗaya ce kawai a cikin dukkan cibiyoyin da gwamnati ta mallaka, kuma shi ma duk faci ne a jikinsa da salataf ko’ina! Nan take na ayyana dokar ta-baci a bangaren kiwon lafiya don dawo da ababen more rayuwa, samar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum biyar ne sun jikkata bayan da gobara ta tashi a gidan man Nobpet da ke kusa da mahaɗar Sojojin Sama a garin Fatakwal, Jihar Ribas. Gobarar ta kuma ƙone sama da motoci takwas da aka ajiye kusa da ofishin Hukumar Sufuri ta Jihar Ebonyi. Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba Tinubu ya ƙaddamar da jirage 2, ya buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Ma’aikatan kashe gobara na Jihar Ribas tare da haɗin gwiwar na Sojojin Sama ne suka yi aiki tare har suka iya kashe gobarar. Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Emmanuel Ninyaegwu, wanda direba motar haya ne, ya ce motarsa mai ɗaukar fasinja 18 ta ƙone gaba ɗaya. Ya...
A kokarin da yake yi na jigilar maniyyatan aikin hajjin bana, Kamfanin jiragen sama na Max Air yace zai kwashe daukacin Alhazan Jihar Jigawa cikin kwanaki biyu. Mataimakin mai kula da ofishin kamfanin dake jihar kano, Mr Barnabas Anderson ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shelkwatar hukumar Jin dadin alhazan jihar Jigawa dake Dutse babban birnin jihar. A cewarsa, ana sa fara jigilar maniyatan jihar zuwa kasar Saudi Arabia a ranar 20 da kuma 21 ga watan Mayun 2025. Ya ce jirgin Max air zai yi sawun farko da maniyata su 550 zuwa kasa mai tsarki a ranar 20 ga watan Mayu. Mr Anderson yace a ranar 21...
A cewarsa, ba ga wannan akwai shirin kawo sauyi kan manyan kalubale da suka hada da lalata na’urorin wutar lantarki, gudanarwa, matsalolin yankuna da suke janyo cikas ga gudanar da ayyuka. Ya umarci hukumar kula da wutar lantarki a Nijeriya (NERC) da ta tabbatar kamfanonin rabar da wutar lantarki sun bayar da hadin kan da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban hukumar Spain Pedro Sanchez ya bayyana ” Isra’ila” da cewa; “Mai Kisan Kiyashi Ce,” wacce kasarsa ba za yi mu’amala da ita ba. Fira ministan na kasar Spain ya bayyana hakan ne a matsayin mayar da martnni ga wani dan majalisar kasar daga yankin Catalonia, Gabrel Rovian yana wanda ya tuhume shi da cewa, yana huldar kasuwanci da Isra’ila,alhali tana yi wa mutanen Gaza kisan kiyashi. Kafafen watsa labarun Spain sun ce wannan shi ne karon farko da firma ministan kasar ya bayyana abinda Isra’ila take yi da cewa kisan kiyasn kare dangi ne. HKI ta fusata akan furucin da Fira ministan Spain tare da kiran jakadan kasar domin nuna masa rashin amincewa.
Majiyar tsaron kasar Yemen ta ce; Jragen HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan tasoshin jiragen ruwa na Hudaidah, da Salif a gudunar Hudaidah dake yammacin kasar. Majiyar tsaron ta Yemen ta ci gaba da cewa; An yi amfani da bama-bamai masu yawa da aka jefa akan wadannan tasoshin jiragen ruwan,kuma fiye da jiragen sama na yaki 10 ne su ka kai harin. Wata majiyar HKI ta fada wa tashar talabijin din “Kan” cewa; manufar kai wadannan hare-haren su ne kakaba wa Yemen takunkumi ta ruwa.” A ranar 6 ga watan nan na Mayu da ake ciki, ma HKI ta kai wani harin akan filin saukar jiragen saman a Sana’a tare da kona jirgen saman kasar da dama. Ita dai...
Da safiyar yau Juma’a ne dai jami’an tsaron kasar Chadi su ka kai wani farmaki na kama tsohon fira minista kuma jagoran ‘yan hamayyar siyasar kasar Succès Masra. Jam’iyyar hamayya da Masra yake jagoranta, ta bayyana abinda jami’an tsaron su ka yi wa jagoran nata da cewa, garkuwa ce. Ita kuwa hukumar kasar ba ta fitar da wani bayani akan kamun Masra ba,wanda shi ne ya zo na uku a zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar da ta gabata. A yayin wancan zaben dai shugaban ‘yan hamayyar siyasar ya riya cewa shi ne wanda ya lashe zaben,amma kuma daga baya ya amince da sakamakon da hukumar zabe ta sanar duk da cewa yana cike da kura-kurai kamar yadda...
A yau Jumma’a, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya yi hadin gwiwa da kawancen gidajen rediyon Turai na EBU wajen gabatar da rahoton Report ITU-R BT.2550, wato fasahar tsara shirye-shiryen bidiyo da rediyo ta hanyar amfani da fasahar sadarwa ta 5G, a shafin intanet na kwancen harkokin sadarwa na duniya wato ITU. Lamarin da ya nuna cewa, CMG ya taka muhimmiyar rawa a fannin tsara shirye-shirye masu inganci, ya kuma kai matsayi na gaba a fannin fitar da fasahohin tsara shirye-shiryen zamani masu inganci. (Mai Fassara: Maryam Yang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Sojojin da suke aiki a ƙarƙashin rundunar birget ta 6 da ke garin Jalingo a Jihar Taraba sun kashe ’yan bindiga biyu tare da ƙwato shanu guda dubu ɗaya daga hannun ɓarayin shanu. Muƙaddashin Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojoji ta birget ta 6 da ke garin Jalingo, Kyaftin Oni Olubodunde ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a garin Jalingo a ranar Juma’a. Tinubu zai halarci rantsar da sabon Fafaroma Leo An kama wasu da haramtattun buhunan takin zamani 20 a Borno Ya ce, nasarar ƙwato shanu tare da kashe ’yan bindigar ya kasance ne biyo bayan wani bayanan sirri da rundunar ta samu dangane da shuguban wasu guggun ’yan bindigar akan bubura talatin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kididdigar da ma’aikatar kula da harkokin masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta yi, ta nuna cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun bana, adadin yarjejeniyoyin da suka shafi fasaha da aka kulla ya kai dubu 228 a kasar Sin, wadanda suka shafi Yuan triliyan 1 da biliyan 600, adadin da ya karu da kaso 13.3 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Lamarin da ya nuna cewa, kasuwar fasaha ta kasar Sin tana bunkasuwa yadda ya kamata. A matsayin daya daga cikin muhimman kasuwanni 5 na kasar Sin, bunkasuwar kasuwar fasaha tana da muhimmanci ga aikin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da sana’o’i. Kididdigar ta nuna cewa, a shekarar 2024, jimillar kudaden da aka samu daga...
Firaminista Li ya nanata cewa, ya kamata dukkan sassan gwamnati da larduna su karfafa tsara manufofi da aiwatar da su, da inganta hadin gwiwa, domin kyautata kuzarin kasuwa da warware matsalolin al’umma yadda ya kamata. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar Asabar ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Rome na ƙasar Italiya bisa gayyatar da sabon Fafaroma Leo XIV ya aike masa. A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya sanar da cewa, shugaba Tinubu zai yi bulaguron ne tare da manyan jagororin ɗariƙar Katolika na Najeriya domin halartar bikin rantsar da sabon fafaroman wanda shi ne na 267. Tinubu ya ƙaddamar da jirage 2, ya buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro An kama wasu da haramtattun buhunan takin zamani 20 a Borno A cewar Onanuga, Cardinal Pietro Parolin ya aike da goron gayyata daga Fafaroma Leo XIV, wanda...
Dangane da sake fasalin dokar zabe, shugaban hukumar INEC, ya ce hukumar na yin cudanya da majalisar dokokin kasar, inda ya ce makwanni biyu da suka gabata, ta yi wani taro a Legas tare da kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa da na wakilai kan sake fasalin zabe. “Majalisar dokoki ta kasa za ta shirya taron jin bahasin jama’a, bayan nan za a samar da kudirin doka, a karshen zancen za a mika wa shugaban kasa domin sanya hannu,” ya shaida. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci sojojin Najeriya su ƙara jajircewa wajen yaƙar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan. Ya ce zaman lafiya, dimokuraɗiyya, da ci gaban tattalin arziƙi duk suna dogara ne da tsaron ƙasa. An kama wasu da haramtattun buhunan takin zamani 20 a Borno Mutum ɗaya ya rasu a rikicin manoma da makiyaya a Yobe Tinubu, ya bayyana hakan ne yayin wani bikin ƙaddamar da sabbin jiragen sama guda biyu ƙirar Agusta 109 Trekker a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. Bikin ya kasance wani ɓangare na bukukuwan cika shekaru 61 da kafuwar Rundunar Sojin Saman Najeriya. Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne, ya wakilci Tinubu a wajen bikin. Ya ce Najeriya na...
“Don haka, idan kuna tunanin cewa taron bayanin ministoci, kamar yadda wasu ke yaɗa cewa za a mayar da shi zuwa wajen ƙasar, ba gaskiya ba ne. “Wannan dandamali da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take samarwa, nan ne inda abin ke faruwa, a nan ƙasar.” Taron ya samu halartar Ministar Harkokin Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musawa; da Ministan Ruwa da Tsaftace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, da kuma Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi. Sanata Umahi, wanda aka ruwaito ba daidai ba cewa yana daga cikin ministocin da za su gabatar da nasarorin Gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu a wani taro a London, ya goyi bayan furucin Idris, yana mai cewa rahoton ba gaskiya ba...
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta kama wasu mutane uku da ake zargi ɗauke da buhuna 20 na haramtattun takin zamani samfurin “Urea”. An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Borno DSP, Nahum Kenneth Daso ya fitar a ranar 15 ga Mayu, 2025. Cikin makonni kaɗan Obasanjo ya murƙushe Boko Haram — Atiku Gwamnatin Katsina za ta gina birnin dawakai na farko a Afirka Rundunar kai ɗaukin gaggawar (RRS), ƙarƙashin jagorancin Kwamishin ‘Yan sandan jihar CP Yusufu Mohammed Lawal ne ta kama waɗanda ake zargin a ranar 13 ga Mayu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na safe a unguwar Tashan Journey, Maiduguri. Waɗanda ake zargin sun haɗa da, Shamsuddeen Rabiu mai kimanin shekara 35,...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ne ya murƙushe ƙungiyar Boko Haram lokacin da ta fara bayyana a shekarar 2002. Atiku, wanda ya yi mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da masu ruwa da tsaki daga Jihar Kogi a birnin Abuja. Gwamnatin Katsina za ta gina birnin dawakai na farko a Afirka Ƙungiya mai alaƙa da Alƙa’ida ta yi iƙirarin kashe sojoji 200 a Buarkina Faso Ya bayyana cewa lokacin da Boko Haram ta fara tayar da hankali a Jihar Yobe, Obasanjo ya kira shi domin neman shawararsa. Atiku, ya bayar da shawarar a kira shugabannin tsaro a ba su wa’adin daƙile lamarin, ko su...
Gwamnatin Jihar Katsina ta samu sahalewar Hukumar Wasanni ta Kasa domin gina Birnin Dawakai na farko a nahiyar Afirka. Wannan amincewa ta biyo bayan wata ganawa ta musammam tsakanin Gwamna Dikko Umaru Radda — wanda Daraktan Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Katsina Dokta Kabir Ali Masanawa ya wakilta — da Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa, Malam Shehu Dikko da Ministar Al’adu, Yawon Bude da kuma Tattalin Arziqin Kirkire-kirkire Barista Hannatu Musa Musawa. Gwamna Radda wanda ya bayyana cewa, gagarumin aikin Birnin Dawakan zai lakume biliyoyin Naira kuma zai kara inganta qokarin gwamnatin jihar na raya al’adun jihar tare da samar da hanyoyin tattalin arziki mai dorewa ga al’ummar jihar da arewacin Najeriya gaba daya. Sabon birnin Dawakan na...

Nijeriya Na Bukatar Dala Biliyan 10 Kowace Shekara Domin Samun Ingantacciyar Wutar Lantarki — Minista
“Wannan ya ba wasu jihohi fiye da goma sha daya ‘yancin kai, tare da karin wadanda ake sa ran za su biyo baya. Wadannan jihohin yanzu suna iya shiga cikin masana’antar wutar lantarki, daga samarwa har zuwa isarwa, rarraba, har ma da samar da mitoci.” “Na biyu, dole ne mu magance rashin ingancin ababen more rayuwa, wanda ya taru a cikin shekaru 60 da suka wuce saboda rashin kula da rashin isasshen zuba jari don farfado da tsarin zamanantar da wutar lantarki.” Ministan ya kuma jaddada bukatar cike gibin mita na sama da kashi 50 bisa dari, yana mai cewa shirin shugaban kasa yana nufin cimma wannan ta hanyar girka mita miliyan 18 a cikin shekaru biyar masu zuwa. Ya...
Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ta shiga rudani a ranar Alhamis bayan da aka samu rahotanni masu karo da juna game da matsayin yajin aikin da reshenta na Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ke yi. Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa, ya gudanar da taron manema labarai inda ya sanar da cewa ASUU-KASU ta dakatar da yajin aikin nata, kuma za a ci gaba da karatun nan take. Ya danganta matakin janye yajin aikin da shiga tsakani da Gwamna Uba Sani ya yi, wanda ya amince da biyan Naira miliyan 50 miliyan don walwalar ma’aikata, tare da fitar da N146 miliyan don biyan wasu albashin da aka rike da kuma alawus-alawus na shirin koyon makamar aiki na dalibai (SIWES). Farfesa Musa ya...
Adepoyigi an sace shi ne da ƙarfe 10:00 na dare yayin da yake ƙoƙarin ajiye motarsa a gidansa da ke Ifon. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yayin da Babbar Sallah ke ƙara ƙaratowa, ’yan kasuwar dabbobi sun bayyana fargaba game da yiwuwar farashin raguna da sauran dabbobin lauya zai yi tashi gwauro a Najeriya. Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin sojin ƙasar Jamhuriyar Nijar ta sanya takunkumin wucin gadi kan fitar da dabbobi zuwa ƙetare, gami da yawaitar sace-sacen dabbobi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya. A farkon watan nan na Mayu ne Gwamnatin Nijar ta sanar cewa matakin na da nufin daidaita farashi dabbobin layya a cikin gida da kuma tabbatar da wadatarsu ga al’ummarta —waɗanda mafi rinjaye Musulmi ne — kafin zuwan Babbar Sallah a farkon watan Yuni. Haramcin ya shafi fitar da shanu da tumaki da awaki da raƙuma, tare da...
Harajin ya kuma kai kasa da kimanin kaso 11 a cikin dari, wanda ya kai kasa da wanda ake karba, idan aka kwatanta da duniya. “Abinda muka yi shi ne, mun cire daukacin ma’aikatan da karbar kasa kaso uku a cikin darei a cikin tsarin na karabar harajin,” Inji tsohon Shugaban LLP. Ya shedawa manyan Malaman Makaranta da Jami’an da ke katbar haraji hakan ne, a wani taro da aka gudanar a jihar Legas Nijeriya dai, ta kasance kasar da sama da alumominta miliyan 8o, ke fama da kangin talauci. Hakan ya kuma kara haifar da hauhawan farashin kayan masarufi, musamman yadda kayan suka tashi a 2024, kafin su sauka zuwa kaso 24.2 a cikin dari. Kazalika, hauhauwan farashi da...
Dubban falasdinawa ma zauna Amurka ne suka fito gagarumar zanga-zanga don tunawa da zagayowar Ranar musiba a jiya Al-Hamis a birnin NewYork. Inda suka bukaci a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza da gaggawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne musiba na shekaru 77 da suka gabata. Wato ranar da HKI to kore falasdinawa daga kasarsu bayan sun shelanta kafiwar HKI a kan kasarsu. Falasdinawa da kawayensu daga kasashen duniya da dama su kan fito zanga-zangar tunawa da wannan ranar shekaru 77 da suka gabata a ranar 15 ga watan Mayun shekara 1948., sannan ranar Nakba ta bana tazo a dai-dai lokacinda HKI take kara kissan Falasdinawa a Gaza. Yansanda a birnin NewYork...
Majiyar kiwon lafiya a zirin Gaza ta bayyana cewa daga safiyar jiya Alhamis zuwa karfe 12 dare HKI ta kashe falasdinawa 143 tare da amfani da jiragen saman yaki tankunan yaki ta kasa da kuma jiragen ruwa yaki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa bayan tsakiyar dare ma sojojin yahudawan sun kashe wasu karin mutane 21 wato a safiyar yau Jumma’a, a sansanin yan gudun hijira na Jabaliya. wato sa’o’ii 5 bayan tsakiyar dare a kuma lokacin bada wannan labarin. Labarin ya kara da cewa a wasu hare haren guda biyu a Khan Yunus sojojin yahudawan sun kashe falasdinawa 5 wasu daga cikinsu yara. Gwamnatin Hamas a Gaza, ta bayyana cewa, tun lokacinda sojojin yahudawan suka...
Ma’aikatar kiwon lafiya a kasar Saudia ta kaddamarda wata manhaja don kula da lafiyan mahajjata a hajjin bana, wanda aka tarjamata zuwa harsuna 8 a duniya. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto kamfanin dillancin labaran Saudi Press Agency (SPA) na fadar haka a yau Jumma’a. Ya kuma kara da cewa harsunan da ake samun manhajar a ciki suna hada da Arabiyya, Inglishi, Faransaci, Urdu, Farisanci, Indonesia, Malay da kuma Turkanci. Manufar wannan manhajar ita ce bada shawara ga mahajjata kan yadda zasu kula da lafiyarsu a cikin wannan lokacinda Hajji na bana, wanda yake zuwa tare da zafi sosai. Da farko manhajan ya bukaci mahajjata su yi amfani da laima don rage zafin da ke fadawa a kansu....