Sojan Lebanon Daya Ya Jikkata Sanadiyyar Harin Sojan HKI Da Jirgin Sama Maras Matuki
Published: 18th, May 2025 GMT
Jiragen na sojojin HKI sun kai hari ne dai a yau Lahadi a kan hanyar da ta raba tsakanin garin Beit-Yahun da Bent-Jubail dake kudancin kasar.
A garin Kafar-kalla ma wani jirgin saman marar matuki ya jefa bama-bamai masu sauti a kusa da wani gida da dama an rushe shi.
Harin na sojojin HKI yana cikin ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon da take yi wanda ya wuce 2000 tun daga tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Nuwamba na 2024.
Bugu da kari HKI ta girke sojojinta a cikin wasu wurare 5 dake kan iyaka,wanda shi ma keta karjejeniya ce.
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hizbullah ta sha yin kira ga gwamnatin kasar da ta yi duk abinda za ta iya domin yin matsin lamba domin fitar da ‘yan sahayoniyar daga cikin kasar.
Kungiyar ta Hizbullah ta ja nanata cewa ba za ci gaba da zuba idanu tana Kallon HKI tana keta hurumin kasar ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Bayyana Adawa Da Keta Hurumin ‘Yanci Tsaro Da Ikon Mulkin Yankunan Iran
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp