Sin Ta Cimma Nasarar Gwajin Jirgin Sama Samfurin AG600
Published: 19th, May 2025 GMT
Kamfanin kirar jiragen sama na kasar Sin wato AVIC ya ce ya cimma nasarar samar da jirgin sama dake iya tashi a kasa da ruwa irinsa na farko samfuri AG600 da aka yiwa lakabi da “Kun Long”. An kuma cimma nasarar gwajinsa a jiya Lahadi a birnin Zhuhai na lardin Guangdong.
Hakan ya nuna cewa, ingancin jirgin ya dace da ma’aunin da aka tanada, kuma ya alamta cewa jirgin samfuri AG600 ya samu iznin kira wato PC.
Rahotanni na cewa a ranar 20 ga watan Afrilun bana, jirgin samfurin AG600 ya samu takardar shaidar inganci ta samfurinsa, matakin da ya nuna cewa, nazarin da aka yi a wannan bangare ya cimma cikakkiyar nasara, kuma jirgin ya samu izinin shiga kasuwa. Kazalika, kamfanin AVIC zai gaggauta tabbatar da cewa “Kun Long”, ya taka rawa a fannin ba da agajin gaggawa, da tinkarar da kuma kandagarkin bala’u daga indallahi. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Rasha ta amince da gwamnatin Taliban a Afghanistan
Rasha ta zama ƙasa ta farko da a hukumance ta amince da gwamnatin ƙungiyar Taliban da ke mulkin ƙasar Afghanistan.
Wannan na zuwa ne bayan Rashar ta karɓi takardun shaidar kama aiki na sabon jakadan Afghanistan, wanda hakan ya sa ta zama ƙasa ta farko da ta amince da gwamnatin Taliban a ƙasar.
Ambaliya da iska sun rushe gidaje 171 a watanni biyu a Gombe – SEMA Majalisar Mali ta ƙara wa Goita wa’adin mulkin shekara biyar“Mun yi imani cewa wannan matakin na amincewa a hukumance da gwamnatin Daular Musulunci ta Afghanistan zai ba da damar haɓaka haɗin gwiwa mai amfani tsakanin ƙasashenmu a fannoni daban-daban,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Afghanistan ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa jakadan Rasha Dmitry Zhirnov ya gana da Ministan Harkokin Wajen Taliban Amir Khan Muttaqi, inda ya isar da wannan matakin na gwamnatin Rasha da ke nuna “muhimmancin wannan mataki”.
Zhirnov ya bayyana wannan a matsayin “mataki mai tarihi wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.”
Ma’aikatar Harkokin Wajen Afghanistan ta ce: “Da wannan mataki, dangantakar ƙasashen biyu za ta ƙara faɗaɗa.”
Muttaqi ya nuna fatan cewa wannan zai haifar da ƙarin haɗin gwiwa da kuma ƙarfafa dangantaka tsakanin Afghanistan da Rasha.
Zhirnov ya shaida wa tashar talabijin ta gwamnati Rossiya-1 Shugaba Vladimir Putin ne ya ɗauki wannan matakin bisa shawarar Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov. “Wannan yana nuna burin gaskiya na Rasha na kafa haɗin gwiwa mai ƙarfi da Afghanistan,” in ji shi.
Zuwa yanzu dai babu wata ƙasa mamba a Majalisar Ɗinkin Duniya da ta amince da gwamnatin riƙon ƙwarya ta Taliban tun dawowarta kan mulki a watan Agustan 2021.