Aminiya:
2025-06-14@01:42:20 GMT

Ban sauya sheƙa ba, makircin siyasa da ƙarya ake min — Kwankwaso 

Published: 17th, May 2025 GMT

Jagoran jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ƙaryata wani rahoto da ke yawo cewa yana shirin shiga sabuwar haɗakar siyasa.

A wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, Kwankwaso ya bayyana rahoton a matsayin “karya, ba shi da tushe kuma makircin wasu ‘yan siyasa ne.”

Riƙaƙƙun ’yan daba da dilolin ƙwaya 31 sun shiga hannu a Kano Tsafta a gidan aure: Abubuwan da kowace mace ya kamata ta sani

Ya gargaɗi jama’a da ka da su yarda da irin waɗannan labarai marasa tushe.

“An jawo hankalina kan wani rahoto wanda ke bayyana matsayina a haɗin gwiwar siyasa a Najeriya.

“Ina so na fayyace cewa irin waɗannan rahotannin ƙarya ne, ba su da tushe kuma makircin siyasa ne kawai,” in ji Kwankwaso.

Tsohon ministan tsaron, ya bayyana cewa ya zaɓi ka da ya riƙa yin magana a fili kan wasu abubuwan da ke faruwa a siyasar ƙasar nan, amma zai yi magana a lokacin da ya dace.

“Na daɗe da daina yin sharhi kan abubuwan da ke faruwa a siyasa, kuma zan ci gaba da kaucewa yin haka a halin yanzu,” ya ƙara da cewa.

Kwankwaso ya buƙaci ’yan Najeriya da su dinga dogaro da hanyoyin sadarwarsa a hukumance idan suna son sanin matsayinsa ko ra’ayinsa game da wani abu.

“Dangane da hakan, ina roƙon jama’a da su riƙa duba ko sauraron saƙonni da ke fitowa daga shafukana da sauran hanyoyin sadarwarta kawai,” in ji shi.

Aminiya ta ruwaito cewa Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, har yanzu yana ɗaya daga cikin manyan ’yan siyasar da ake sa ido a kansu kan yiwuwar yin haɗaka da wata tafiya ta siyasa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kwankwaso Siyasa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Bayyana Adawa Da Keta Hurumin ‘Yanci Tsaro Da Ikon Mulkin Yankunan Iran

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Bayyana Adawa Da Keta Hurumin ‘Yanci Tsaro Da Ikon Mulkin Yankunan Iran
  • Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Karɓo Bashin Dala Miliyan 6.6
  • Iran ta caccaki kudurin IAEA wanda ta ce yana cike da siyasa
  •  Iran Za Ta Kara Yawan Sanadarin Urani’um Da Take Tacewa A Wuri Na Sirri
  • An kashe jaririn wata 9 da wasu 3 a Filato
  • Iran ta Yi Gargadin Cewa Zata Fice Daga Yarjeniyar NPT Idan Hukumar IAEA Ta Tir Da Ita
  • Ministan Tsaro Na Kasar Iran ya bada Labarin Gwajin Wani Sabom Makami Mai Limzami Mai Daukar abubuwan Fashewa Har Ton Biyu
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Sake Tunzura Iran Shirin Makamashin Nukiliyarta Zai Fuskanci Martani
  • A Bai Wa Kudu Tikitin Takara A 2027 Ko PDP Ta Ruguje – Wani Jigo A PDP
  • Nan Ba Da Jimawa Ba Harkar Man Fetur Za Ta Sauya A Nijeriya – Dangote