Aminiya:
2025-06-14@13:50:48 GMT

Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa

Published: 18th, May 2025 GMT

Wani jami’in Hukumar Sibil Difens, Abubakar Abdulkadir Mayos, ya mayar da kuɗin wata maniyyaciya Naira 822,038 da suka ɓata a sansanin alhazai na Yola da ke Jihar Adamawa.

Kuɗin da aka samu sun haɗa da dala $505 da Riyal 30 na ƙasar Saudiyya, wanda ya kai kimanin Naira 822,038.

An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin tantance alhazai a Abuja Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso

Kuɗin mallakin Maimuna Salihu, wata maniyyaciya daga Jihar Taraba da ke shirin zuwa aikin Hajjin bana.

Jami’in ya mayar mata da kuɗin a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu, 2025.

An gudanar da bikin miƙa kuɗin a gaban jami’an Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ciki har da jami’in Taraba, Daraktan Tsare-tsare, da wasu manyan jami’ai.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Adamawa Hajiya maniyyaciya Taraba

এছাড়াও পড়ুন:

Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai

Aƙalla jihohi 11 na Najeriya sun kashe sama da Naira biliyan 6.2 wajen tallafa wa Alhazansu domin sauƙaƙa musu wajen zama a ƙasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin 2025.

Wannan tallafi ya haɗa da kuɗi, jakunkunan tafiya, da kuma sayen raguna na hadaya domin sallar Layya.

Tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka cikin shekaru uku masu zuwa — Bankin Duniya Dalilin da babu abin da gwamnatin NNPP ta taɓuka a Kano — APC

Gwamnatin Jihar Sakkwato ce ta fi kowa bayar da tallafi mafi yawa, inda Gwamna Ahmed Aliyu, ya bai wa kowane daga cikin alhazai 3,200 na jihar Riyal 1,000 (kimanin Naira 450,000).

A Kano kuwa, kowane alhaji daga cikin alhazai 3,345 sun samu kyautar Riyal 50.

Gwamnatin Jihar Legas ta bai wa kowane daga cikin alhazai 1,315 Riyal 180 (kimanin N74,870), yayin da Jihohin Jigawa da Kebbi suka bayar da mafi ƙarancin adadi.

Wani jami’in Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana cewa: “Kowane Alhaji ya samu Riyal 180 a matsayin kyauta don sauƙaƙa rayuwarsu a lokacin aikin hajji.”

Jihar Borno ba ta bayar da kuɗi ba, amma ta biya kuɗin ragunan layya (hadaya) na Alhazan jihar guda 2,174.

Haka kuma, hukumomin Kano sun sanar da cewa kowane Alhaji zai samu babbar jakar tafiya domin dawowarsa gida cikin sauƙi.

Sai dai masana da malamai sun soki irin wannan kashe-kashen kuɗi da gwamnati ke yi, inda suka bayyana hakan a matsayin almubazzaranci da rashin fifita abin da ya fi muhimmanci.

Farfesa Yahaya Tanko, masani a harkokin siyasa, ya ce: “Wannan ba fifiko ba ne. Ya kamata gwamnoni su mayar da hankali kan matsalolin tsaro da talauci, ba tare da kashe kuɗi kan aikin hajji ba.”

Ya ƙara da cewa: “Al’umma na fama da sace-sace, manoma ba sa iya zuwa gonakinsu, amma gwamnoni na kashe miliyoyi kan aikin Hajji. Wannan ba daidai ba ne.”

Hakazalika, babban malamin addini, Sheikh Fuad Adeyemi, ya ce: “Kuɗaɗen da aka kashe a kan Hajji za a iya amfani da su wajen taimaka wa ‘ya’yan Alhazai su yi karatu. Wannan zai amfanar da iyalai da kuma al’umma gaba ɗaya.”

Mutane da dama a kafafen sada zumunta sun bayyana irin wannan kashe kuɗi a matsayin rashin adalci ga talakawa.

Wasu sun ce aikin Hajji ibada ce da ya kamata mutum ko al’umma su ɗauki nauyinta da kansu, ba gwamnati ba.

Yanzu haka ana ta kira ga gwamnoni da su dawo da hankali kan tsaro, kiwon lafiya, da ilimi domin hakan ne zai amfani mafi yawan jama’a, ba wasu ƙalilan da suka samu damar zuwa aikin Hajji kawai ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jami’in Hamas Ya Jinjinawa Iran Kan Kakkausan Martanin Da Ta Mayar Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasu
  • Ƴansanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane 2, Sun Ceto Mutane 11 A Delta Da Katsina
  • Gwamnan Gombe Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Da ‘Yan Daba Suka Yi Wa Amadi Kasiran
  • Iran tana da hakkin mayar da martani ga Isra’ila : Sanarwar Ma’aikatar harkokin waje
  •  Iran Za Ta Kara Yawan Sanadarin Urani’um Da Take Tacewa A Wuri Na Sirri
  • An kashe jaririn wata 9 da wasu 3 a Filato
  • Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Sake Tunzura Iran Shirin Makamashin Nukiliyarta Zai Fuskanci Martani
  • Birnin Los Angeles Na Amurka Ya Rikice Yadda Ake Dauki Ba Dadi Tsakanin Al’ummar Jihar Da Jami’an Tsaro