Gwamna Lawal Ya Jaddada Aniyar Inganta Kiwon Lafiya A Jihar Zamfara
Published: 17th, May 2025 GMT
A lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa da hawansa mulki a watan Mayun 2023, ya ci karo da tsarin kiwon lafiya da ya tabarbare saboda rashin kulawa.
Ya ce, “Gwamnatinmu, ƙarƙashin ginshiƙan shirye-shiryen ceto, nan da nan ta fara tantance abubuwan da asibitoci ke buƙata, inda sakamakon ya zama abin tsoro kuma ya nuna akwai jan-aiki.
“Alal misali, a jihar da ke da mutane kusan miliyan 6 tare da tarin ƙalubale, na’urar duban ɗan tayi ɗaya ce kawai a cikin dukkan cibiyoyin da gwamnati ta mallaka, kuma shi ma duk faci ne a jikinsa da salataf ko’ina! Nan take na ayyana dokar ta-baci a bangaren kiwon lafiya don dawo da ababen more rayuwa, samar da kayan aiki a asibitocinmu tare da samar da kwarin gwiwa da horarwa ga ƙwararru a fannin kiwon lafiya.
“Don inganta ayyukan more rayuwa, mun kuma ba da kwangilar samar da kayayyaki, sakawa, gwadawa, da horar da ma’aikata kan yadda za su yi amfani da na’urorin na zamani.
“Kamar yadda aka saba a wannan gwamnati ta Jihar Zamfara, muna tabbatar da cewa duk kayan aikin da aka kawo da kuma sanya su sun kasance masu inganci kuma sun cika ƙa’idojin da ake da su.
“Bari in jaddada cewa wannan ƙaddamarwar wani bangare ne na sake fasalin jihar Zamfara bakiɗaya a fannin kiwon lafiya, za ku iya tuna cewa mun riga mun samar da manyan asibitocin da aka gyara a garuruwan Ƙaura, Maradun, Maru, da Nasarawa Burkullu.
“Har ila yau, ana shirin ƙaddamar da wasu muhimman asibitocin da suka haɗa da Asibitin Ƙwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura, Gusau, Babban Asibitin Talata Mafara, Shinkafi, da Babban Asibitin Tsafe, da dai sauransu.
“Bugu da ƙari, bayan amincewar majalisar zartarwa ta jiha, Ma’aikatar Lafiya ta fara aikin samar da cikakken kayan aiki ga manyan asibitocin da ke Anka, kuma wannan ya haɗa da samar da kayan aiki na zamani tare da horar da ma’aikatan kiwon lafiya.
“Ya ku ’yan uwa maza da mata, waɗannan ayyukan suna nuna hangen nesan mu na gina tsarin kiwon lafiya na zamani, mai aiki da kuma ɗorewa wanda zai rage yawan tura marasa lafiya zuwa wasu asibitoci a wajen jihar tare da tabbatar da cewa ’yan jihar mu sun sami ingantaccen kulawa kusa da gida.
“Yayin da muke murnar wannan nasarar, ina so in jawo hankalin mahukuntan asibitin kan buƙatar yin taka-tsan-tsan wajen amfani da kuma kula da wannan wuri.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kiwon lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
Jami’an tsaro a Jihar Kaduna, sun fara gudanar da babban samame domin kawar da ’yan ta’adda da ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gudanar da aikin tare haɗin gwiwar sojoji, DSS, NSCDC, KADVS, da kuma ƙungiyoyin sa-kai da mafarauta.
Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000Aikin ya shafi ƙananan hukumomin Makarfi, Hunkuyi da Ikara.
Rundunar ta ce manufar wannan samame shi ne “share dukkanin maɓoyar miyagu, rushe sansanonin da suka kafa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.”
Wannan mataki ya biyo bayan umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, wanda ya umarci dukkanin rundunonin ’yan sanda a faɗin ƙasar nan su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da aikata laifuka.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Rabiu Muhammad, ya tabbatar wa jama’a cewa jami’an tsaro za su ci gaba da matsa wa miyagu lamba.
Ya ce za su ci gaba da yin gwiwa da rundunonin tsaro domin tabbatar da tsaro a jihar.