2025-05-14@18:07:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4488

«da kasar Amurka»:

    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta cafke wasu maza biyu bisa zargin yi wa ƙananan yara mata fyaɗe a lokuta daban-daban a jihar. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce sun kama wani mutum mai shekara 47, da zargin yi wa ‘yar matarsa mai shekara biyu fyaɗe a Tudun Wada, Shamaki a ranar 5 ga watan Mayu. ’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara  Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Bayan samun rahoton daga matarsa, rundunar ’yan sandan ta garzaya gidansu inda ta kama wanda ake zargin, sannan suka kai yarinyar Asibitin Ƙwararru na Gombe domin duba lafiyarts. Ya ce...
    Oloyede, wanda ya bayyana tangardar a matsayin “zagon kasa” ga shirin jarabawar UTME ta 2025, ya ce, wadanda abin ya shafa za su fara samun sako a wayar salularsu daga Hukumar daga ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025.   Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME ta shekarar 2025, sama da miliyan 1.5 aka bayar da rahoton, sun samu maki kasa da 200 daga cikin mafi girman maki 400, lamarin da ya haifar da damuwa a bangaren ilimi na kasar.   UTME ta wannan shekara, ta gamu da koma baya sosai, wanda ya haifar da damuwa tsakanin ɗalibai, iyaye, da malamai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo Ya ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani ƙauye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, ’yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su. Ya kuma ruwaito yadda wani yaro mai fama da cutar farfaɗiya ya mutu bayan...
    Ɗan Majalisa mai wakiltar yankin Kaura Namoda da Birnin Magaji a jih6ar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bai wa karnuka wasu jairirai tagwaye da aka haifa a daji su ci. Jaji, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba. Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo Ya ce maharan sun sace wata mata mai ciki a wani ƙauye da ke Zamfara, kuma bayan ta haihu, ’yan bindigar suka jefa wa karnuka domin ci su. Ya kuma ruwaito yadda wani yaro mai fama da cutar farfaɗiya ya mutu bayan...
    Tsohon shugaban kasar Sin marigayi Mao Zedong ya taba bayyana cewa, ” Idan an dauki mataki mai karfi wajen neman zaman lafiya, to, za a samu. Amma idan an nuna sassauci a kokarin neman tabbatar da zaman lafiya, to, ba za a samu biyan bukata ba. ” Wannan tunani ya sa kasar Sin nuna ra’ayin kin amincewa da matakin kasar Amurka na karbar karin harajin fito ba tare da wasiwasi ba. Musamman ma ta la’akari da yadda kasar ba ta rasa “kati” a hannunta ba, inda karfin tattalin arzikinta, da manufar bude kofa da ta dauka, dukkansu suka kasance karfinta na tinkarar kalubale. Sai dai, idan babu “kati” a hannu, yaya za a yi? Ga shi, abu na biyu da...
      Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce zuba jarin Euro miliyan dari da goma sha ɗaya da tayi akan aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani zai rage cunkoson ababen hawa da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar.   Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka da Ababen More Rayuwa ta Jihar Kaduna, Ibrahim Hamza, ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki kan aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani wato BRT da aka gudanar a Kaduna.   Aikin samarda hanyoyi da motocin sufuri na zamani yana da nufin inganta zirga-zirgar ababen hawa a birane, rage cunkoso, da kuma inganta rayuwar jama’ar Jihar Kaduna. Kwamishina Ma’aikatar Aiyyuka da Ababen More Rayuwa, Ibrahim Hamza ya tabbatar da kudurin gwamnati na sauya...
    Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta bukaci Gwamnatin Jiha da kananan hukumomin jihar goma sha uku da su gaggauta bayar da kayayyakin tallafi ga wadanda guguwar iska ta shafa a fadin jihar. Majalisar ta bayyana cewa hakan na da muhimmanci domin inganta rayuwar wadanda abin ya shafa da rage musu radadin halin da suke ciki. Shugaban Majalisar, Dr. Danladi Jatau, ne ya bayyana hakan bayan Hon. Hudu A Hudu ya gabatar da batun a matsayin lamari mai muhimmanci ga jama’a, yayin zaman majalisar da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar. Shugaban majalisar ya ce abin jimami ne kwarai yadda guguwar iska ta lalata gidaje, makarantu, gine-gine da wasu muhimman kayayyaki da suka kai daruruwan miliyoyin Naira tare da jikkata mutane...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Karba-karba wani tsari ne da ya tanadi kewayarwar ludayi a tsakanin kudanci da arewacin Najeriya wajen rike shugabancin kasa. Manufar tsarin, wanda babu shi a Kundin Dokokin Najeriya, ita ce tabbatar da daidaito da haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa. Sai dai yunkurin samar wa tsarin mazauni ta yadda shugabanci zai riƙa kewaya a tsakanin shiyyoyi shida na kasar nan bai samu shiga ba a Majalisar Wakilai. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A Najeriya Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan wannan tsari na karba-karba da tasirinsa. Domin sauke shirin, latsa nan
    A jiya ne uwar gidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan da matar shugaban kasar Brazil Rosângela da Silvaa wadda ta rako mai gidanta a ziyarar da yake yi a kasar Sin, suka ziyarci babban zauren nuna fasahohin nishadantarwa ta kasar Sin, inda suka kalli abubuwan dake ciki, tare da kallon wasan opera da wasu wake-waken Sin da Brazil. Peng Liyuan ta bayyana cewa, Sin da Brazil suna mu’amala da juna a fannin al’adu, kuma jama’ar kasashen biyu suna ta kara fahimtar juna, da sada zumunta mai zurfi. A nata bangare kuwa, Madam Rosângela ta jinjinawa nasarorin ci gaba da kasar Sin ta samu da kuma yadda ake raya al’adun kasar. Tana fatan kara sa kaimi ga yin mu’amala a tsakanin...
    Masana sun ce wannan mataki zai iya sauya tsarin kasuwanci da ci gaban fasaha a duniya, musamman a yankin Larabawa. Bayan kammala taron a Saudiyya, ana sa ran zai wuce Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) domin ci gaba da tattaunawa da shugabannin yankin kan batutuwan tsaro da haɗin gwiwar tattalin arziƙi. Yarjejeniyar ta samu karɓuwa daga ɓangarorin da dama, inda wasu ke ganin hakan zai ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu, musamman wajen yaƙi da ta’addanci da bunƙasa fasahar zamani. Sai dai wasu na nuna damuwa kan yawan makaman da Saudiyya ke saye daga Amurka, suna mai cewa hakan na iya ƙara tsananta rikice-rikice a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    A jiya Talata sojojin HKI su ka kai wani mummunan hari akan asibitin Gaza na “Turai” da kuma zagayensa da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da kuma jikkata wasu da dama. Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama wajen kai wadannan munanan hare-haren akan Asibitin da ake kir ana turai, da kuma gefensa a kudu maso gabashin birnin  Khan-Yunus. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; jiragen saman na HKI sun kai hare-haren ne ta hanyar harba makamai masu linzami akan bangare da kuma kula da matsalolin gaggawa na asibitin da kuma bangaren dake kula da asibitin da gyara abubuwan da su ka baci. Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wasu hare-haren a...
    Rahoton MDD ya sanar da cewa, fiye da mutane 48,000 ne, ambaliyar ruwan saman da aka yi a Somaliya ya yi wa illa, yayin da wasu da adadinsu ya kai 17 su ka rasa rayukansu. Hukumar MDD mai kula da ayyukan jin kai da cewa ( OCHA) ce ta sanar da hakan,tana mai kara da cewa da akwai yiyuwar a kara samun saukar mamakon ruwa sama a tsakiyar kasar, nan da wasu kwanaki masu zuwa. Wannan ambaliyar dai wacce ta shammaci mutanen kasar, a lokacin da kungiyar agajin kasar ta sanar da cewa, tana da karancin kayan da ake da bukatuwa da su domin kai daukin gaggawa idan hakan ta faru. Kasar Somaliya ta fuskanci ambaliyar ruwa mai tsanani a...
    A yau Laraba ne dai shugaban majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf ya birnin Jakarta na kasar Indonesia, da zummar halartar taron wakilan majalisun kasashen da suke mambobi a kungiyar kasashen musulmi. Taron na wannan karon a kasar Indonesia shi ne karo na 19 da kungiyar ta kasashen musulmi take yi a matakin wakilan majalisun, kasashe mambobi. An bude taron ne dai daga jiya Talata 13 ga watan Mayu, zai kuma ci gaba har zuwa ranar 15 gare shi. Tun a jiya ne dai wakilan Iran su 4 daga majalisar shawarar musulunci ta kasar su ka isa birnin na Jakarta domin halartar taron.
    Rundunar “Sarayal-Kudus” ta kungiyar jihadul-Islami ta harba makamai masu linzami akan sansanonin ‘yan share wuri zauna na “Asqalan” da “Ushdud”. A jiya Talata ne dai rundunar ta Sarayal-Qudus’ ta sanar da harba makamai masu linzamin kaan sansanonin ‘yan share wuri zauna, a matsayin ci gaba da mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin na HKI akan al’ummar Falasdinu. Sanarwar da rundunar ta fitar ta kunshi cewa: Harin nata yana a matsayin mayar da martani ne akan kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu a Gaza. A wani labarin na daban, rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas ta sanar da cewa ta yi taho-mu-gama da sojojin mamaya a unguwar “Shuja’iyya” dake gabashin birnin Gaza. Sojojin HKI suna ci...
    Makaman sun haɗa da bindiga ƙirar AK-47 guda biyar, AK-49 guda biyu, harsasai sama da 400 da sauransu. CP Dantawaye, ya ce rundunar ta fara horar da jami’anta domin ƙara musu ƙwarewa da ƙaimi wajen yaƙi da laifuka kamar garkuwa da mutane da fashi da makami. Ya ce wasu jami’an da suka halarci wani horo na musamman sun kammala a makon jiya, sannan kuma rundunar ta ƙaddamar da sabbin dabarun yaƙi da laifuka kamar sintiri a manyan hanyoyi, kai samame maɓoyar ‘yan daba, da kuma binciken motocin jama’a a wurare daban-daban. Ya ƙara da cewa rundunar tana aiki da al’umma ta hanyar amfani da tsare-tsaren ‘yansanda. Kwamishinan ya buƙaci al’ummar Jihar Kogi, musamman sarakunan gargajiya, shugabannin addini, ƙungiyoyin matasa da...
    Gwamnatin jihar Kwara ta shirya wani gagarumin horo ga likitocin kiwon lafiya a fadin cibiyoyin kiwon lafiya na jihar kan yadda za a shawo kan cutar zazzabin cizon sauro.   Da yake sanar da bude horon a Ilorin, daraktan kula da lafiyar jama’a na jihar, Dokta Oluwatosin Fakayode, ya jadadda bukatar gaggawar gano cutar da wuri da kuma gaggauta magance cutar zazzabin cizon sauro, musamman a cikin mutane masu rauni kamar yara ‘yan kasa da shekaru biyar da mata masu juna biyu.   A cewarsa shirin ya kasance wani bangare na faffadan kokarin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a jihar, gami da shirye-shiryen yakin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro na 2025 (SMC).   Dokta Fakayode ya bayyana cewa horon...
    Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta amince da dokar kafa doka da za ta samar da tsari da kula da bada izinin filaye da yarjejeniyoyin al’umma ga masu hakar ma’adanai da sauran batutuwan da suka shafi hakan.   Shugaban Majalisar Dokta Danladi Jatau, ya sanar da amincewa da kudirin a zaman majalisar a Lafiya.   Shugaban majalisar ya ce kudirin dokar idan Gwamna Abdullahi Sule ya amince da shi zai magance kalubalen hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar.   Shugaban majalisar ya ce sashe na uku na kudirin ya ba da umarnin kafa Asusun Raya Al’umma na CDF don inganta walwalar al’ummomin da ke hakar ma’adanai ta hanyar samar da ayyukan more rayuwa da ayyukan jin kai.   “Kamfanonin...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umurci shugabannin kananan hukumomin jihar 44 da su tabbatar da cewa Kansilolinsu sun shiga dukkan ayyukan da aka gudanar a kananan hukumominsu .   Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da kansilolin kananan hukumomi 484 daga kananan hukumomi 44 na jihar.   Taron wanda ya gudana a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati, da nufin karfafa alaka tsakanin gwamnatin jihar da majalisun kananan hukumomi.   Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa gwamnatin sa tana da hankali kuma ba ta da almundahana, kuma ba za a amince da duk wani nau’i na almundahana ba.   Ya kuma bukaci kansilolin da su yi aiki tukuru don ganin sun rike amanar...
    Majalisar Dattawa ta buƙaci rundunar sojin Nijeriya ta tura ƙarin sojoji da manyan makaman yaƙi zuwa jihohin Borno da Yobe, bayan farfaɗowar hare-haren ‘yan ta’adda na Boko Haram a jihohin. Ƙudurin ya biyo bayan ƙarin hare-haren ‘yan ta’addan ne a arewa maso gabashin ƙasar, ciki har da kashe kimanin sojoji goma a garin Marte da ke ƙaramar hukumar Monguno ranar Litinin, 12 ga watan Mayu, da kuma wani harin da suka kai Gajiram na Ƙaramar Hukumar Nganzai, da sanyin safiyar ranar Talata. Zaɓen 1993: IBB ya wallafa ba daidai ba a littafinsa — Sule Lamiɗo Trump ya janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria A wani ƙuduri da mai tsawatarwa majalisar, Sanata Tahir Munguno, ya gabatar a ranar Talata,...
    A yanzu haka ana zargin wasu dakarun sojin sun ɓace tun bayan kai harin na ranar Litinin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Gwamnan Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo, ya musanta dalilin da tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar a littafinsa dangane da soke zaɓen 1993. Tsohon Ministan Harkokin Wajen Nijeriyar ya ce dalilin da IBB ya bayar cewa shi ne abin da ya sa ya rushe zaɓen 1993, “ba gaskiya” ba ne. Janar Babangida a littafinsa mai suna “A Journey in Service” ya yi zargin cewa marigayi Janar Sani Abacha ne ke da alhakin rushe Zaɓen 12 ga watan Yunin 1993. Trump ya janye takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba wa Syria ‘Duk da hauhawar farashi tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka’ Alhaji Sule Lamido ya faɗi hakan ne a littafin tarihinsa da ya rubuta mai suna “Being True to...
    Wata majiyar kuma ta buƙaci dakarun Nijeriya da su ɗauki matakin gaggawa. “Har yanzu ‘yan ta’addan na riƙe da sansanin. Ya kamata a gaggauta dawo da zaman lafiya a yankin,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban kwamadn dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ko (IRGC) Manjo Janar Hussain Salami ya bayyana cewa dakarun kare juyin jya halin musulunci a nan Iran a shirye suke don fuskantar duk wani kuskureb da makiya zasu yin a kawowa kasar Hare-hare. Janar Salami ya bayyana haka ne a jiya Talata a lokacinda yake wani Jawabi a birnin Mashad na arewa maso gabacin kasar Iran. Janar Salami yana wannan maganane bayan da shugaban kasar Amurka Dunal Trump wanda yake ziyarar wasu kasashen larabawa a yankin yammacin Asiya, na cewa idan an kasa cimma dai-daito tsakanin Iran da Amurka a tattaunawa kan shirinta na makashin nukliya to Iran ta shiryawa yaki. Salami ya kara da cewa sun san...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai dagewa kasar Siriya dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata, kuma zai gana da shugaban gwamnatin riko na kasar Ahmad Sharaa wanda aka fi sani da Julani. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a wata tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar Saudiya a birnin Riyad na kasar Saudiya, inda ya fara ziyarar aiki a can tun jiya Talata. Shugaban ya kara da cewa: A yanzu lokaci yayi da mutanen kasar Siriya zasu huta, don zamu dauke dukkan takunkuman da muka dorawa kasar Siriya. Saboda zata samar da huldar Jakadanci da HKI kuma babu wata cuta da zata sami kasar daga Siriya. Wannan yana zuwa...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya tattauna da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan na farko Hiroyuki Namazu a nan birnin Tehran a jiya Talata inda bangarorin biyu suka tattauna al-amuran da suka shafi kasashen biyu na harkokin kasuwanci da kuma wasu bangarori, sannan tare da tattauna irin sauye-sauyen da ake samu a yankin da kuma abinda ya zama lazimi ga kasashen biyu su yi a wannan halin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasashen biyu sun kara jaddada bukatar kasashen su karfafa dangantaka da ke tsakaninsu. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Japan ya fada a taron kwamitin hadin guiwa na kasashen biyu kan cewa kasar Japan ta zabi zurfafa dangantaka da kasar Iran...
    Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa karfin bangaren sojojin tabbatar da zaman lafiya na majalisar a duniya, yana dai dai da karfin dukkan kasashen da suke bawa kudaden da ake tafiyar da ayyukansu ne. Don haka ya bukaci kasashen da basu biya rabonsu na kudade karo-karon da ake yi don tafiyar da ayyulan zaman lafiya a duniya bas u yi hakan da gaggawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto babban sakataren yana fadar haka a jiya talata ya kuma kara da cewa a halin yanzu majalisar tana tafiyar da ayyukan zaman lafiya har 11 a kasashen duniya  wadanda suka hana da  nahiyar Afirka Asia da kuma turai. Guterres ya kara da cewa majalisar tana da...
    A cikin binciken jin ra’ayoyin, kashi 91 cikin 100 na masu bayyana ra’ayoyi, sun yi imanin cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke barazana ga rayuwar Amurkawa. An wallafa sakamakon binciken a dandalolin CGTN a cikin harsuna biyar da suka hada da Ingilishi, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci. A tsakanin sa’o’i 24 da kaddamar da binciken, masu amfani da intanet fiye da 12,000 ne suka shiga cikin binciken tare da bayyana ra’ayoyinsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Ya ce, “Samar da motocin aiki ga jami’an tsaron zai bayar da ci gaba wajen sawwaƙa masu zirga-zirga, kai ɗauki a kan lokaci da ƙara ƙarfafa masu gwiwa wajen samar da tsaro da bin doka da oda. “Wannan taro na yau, wani ci gaba ne na ƙoƙarin gwamnatina wajen ƙarfagawa, tare da inganta ayyukan jami’an tsaron da ke aiki a duk faɗin jihar. “Wannan kuma yana ɗamfare ne da alƙawuran da muka yi, tare da jajircewar mu wajen samar da duk abin da za mu iya don tunkarar dukkan nau’o’in rashin tsaro, samar da zaman lafiya, kare rayuka da dukiyar jama’ar jihar mu. “Wannan ƙoƙari namu yana ƙara nuna hobbasan gwamnatin mu wajen ƙarfafa wa jami’an tsaron mu don...
    Babu wata ’yantacciyar kasa da za ta hakura da muradunta domin wata ta biya bukatunta na son rai. Yayin da Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kasashe haraje-harajen kwastam na babu gaira ba dalili, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kin amincewa da salon cin zali, inda ta sha nanata cewa, sai ta ga abun da ya ture wa buzu nadi, a yakin cinikayya da Amurkar ta tayar. Lallai tsayuwar kasar Sin ya ba kasashe masu tasowa kwarin gwiwa, kuma ya nuna cewa, lokaci ya wuce da za a rika yi wa ’yantattun kasashe danniya da cin zali domin biyan bukatu na kashin kai. Hakika kasar Sin ta gina tubali mai karfi da ta dora tattalin arzikinta a...
    Ya ce, aikin wannan cibiya ta “Saudi Noor” yana gudana ne a karkashin jagorancin Hadimin wurare biyu masu tsarki; Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima Mohammed bin Salman.   Hakan ya nuna manufar Saudiyya wajen gudanar da ayyukan jinkai a fadin duniya—wanda KSrelief ke tallafawa al’umma—domin inganta kiwon lafiya tare da magance cututtukan dake addabar al’umma masu karamin karfi.   Ya ce, “tun lokacin da cibiyar ta fara ayyukan jinkai don yaki da cutar makanta a Nijeriya, cikin watan Oktobar 2019, KSrelief ta gudanar da gwaje-gwajen idanu sama da 218,000, da gudanar da tiyatar idanu sama da 21,000, kuma da bayar da tallafin tabarau sama da 45,000 ga al’umma.   “KSrelief ta samu karbuwa a matsayin daya daga...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar dattawa a ranar Talata ta yi kira ga rundunar sojin Nijeriya da ta gaggauta tura jami’anta da sabbin kayan yaki na zamani zuwa jihohin Borno da Yobe sakamakon sabon hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a yankin. An yi wannan kiran ne biyo bayan sabbin hare-haren ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, ciki har da kashe sojoji sama da 10 a garin Marte da ke karamar hukumar Monguno ta jihar Borno, a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu. Majalisa Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Dokar Karɓa-karɓa A Kujerar Shugaban Ƙasa A Tsakanin Shiyyoyin Nijeriya An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya ‘Yan ta’addan sun kuma sake kai wani hari da sanyin safiyar Talata a Gajiram...
    Kazalika, shugabannin kasashen biyu sun kuma gana da manema labarai a tare. Bangarorin biyu dai sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan karfafa gina al’ummar Sin da Brazil mai makoma guda domin kara tabbatar da samuwar duniya mai cike da adalci, wacce za ta kasance mai dorewa cikin nagarta, da kara hada karfi da karfe wajen karfafa damawa da sassa daban-daban a sha’anin duniya, tare da ba da sanarwar hadin gwiwa game da rikicin Ukraine. Kafin ganawar dai, shugaba Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, sun shirya bikin maraba ga Lula da uwargidansa ​​a dandalin da ke wajen kofar gabas na babban zauren taron al’umma. (Bilkisu Xin/Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Amurka ta sanar da cimma wata yarjejeniya makamai mai tsoka ta Dala biliyan 142 da Saudiyya. Wanan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Amurka Donald Trump, ke gudanar da ziyara a kasar Saudiyya irinta ta farko a ketare tun bayan sake hawansa karagar mulki. Amurka ta bayyana yarjejeniyar a matsayin “mafi girma a tarihi. ” Wannan yarjejeniya, wacce wani bangare ne na babban kunshin alkawurran saka hannun jari – da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 600, a cewar gwamnatin Amurka – za ta ba wa masarautar Saudiyya damar sayen “kayan aikin soja daga kamfanonin tsaron Amurka goma sha biyu,” musamman a fannin tsaron sararrin samaniya, makamai masu linzami, tsaron teku da tsarin sadarwa. A wani...
    A kasar Mali a rushe dukkan jam’iyyun siyasa na kasar a hukumance. bisa ga bukatar shugaban kasa da aka amince da shi a wannan Talata, yayin wani taron majalisar ministocin kasar, an rusa jam’iyyun siyasa a duk fadin kasar. An kuma haramta tarurruka da sauran ayyukan jam’iyyun siyasar da kungiyoyin dake da alaka da siyasa ko kuma su fuskanci takunkumi. Gwamnatin rikon kwarya ta ayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan soke kundin tsarin mulkin jam’iyyun siyasa. Dole ne a samar da sabuwar doka musamman don tafiyar da harkokin siyasar Mali, inji karamin minsitan kula da sauye-sauyen al’amuran siyasa a gidan talabijin na kasar.
    Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar a Jabalia da Khan Younis na Falasdinu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren na Isra’ila, yana mai cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa. A yayin da yake bayyana goyon bayansa ga al’ummar Falastinu da ake zalunta, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kakkausar suka kan mummunan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai kan matsugunan ‘yan gudun hijira da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira a Jabalia da Khan Younis, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da kananan...
    Bankin Duniya ya sanar da cewa duk da ƙalubalen hauhawar farashin da Nijeriya take fuskanta, tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru a shekarar da ta gabata. Babban bankin ya ce tattalin arzikin Nijeriyar ya samu haɓaka a kusan shekaru goma a 2024, inda a watanni uku na karshen 2024 aka samu haɓaka sosai. HOTUNA: Trump na ziyara a Saudiyya Majalisa ta yi watsi da kudurin dokar mulkin karba-karba Hakan na ƙunshe cikin wani rahoto da babban jami’in tattalin arzaki na Bankin Duniya a Nijeriya, Alex Sienaert, ya fitar ranar Litinin a Abuja. Sienaert ya bayyana cewa tattalin arzikin ya ƙaru da kashi 4.6 a watanni uku na ƙarshen 2024, inda ya kuma yi nuni da cewa zai ci gaba da haɓaka...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya sake jaddada cewa bikin ya nuna wani muhimmin mataki a ƙoƙarinsa na ƙarfafa wa al’ummar Zamfara masu ƙaramin ƙarfi.   “Saboda haka, cikin farin ciki na tsaya a gabanku domin ƙaddamar da wannan muhimmin shiri.   “Ya ku jama’a, da baƙi, an tsara wannan shiri ne domin bayar da tallafin kuɗi na Naira 75,000.00 kowanne ga masu cin gajiyar shirin su 448,141.   “Kamar yadda Kwamishina Kainuwa ya bayyana a baya, daga cikin adadin da ake sa ran, mutane 279,534 sun cika mafi ƙarancin abin da ake buƙata don karbar Naira 75,000 kowannen su, sauran waɗanda suka ci gajiyar shirin za a tantance su kuma za a ba su nasu da zarar an kammala,...
    Na hudu, zaman lafiya, Sin na fatan tabbatar da shawarar tsaro ta duniya tare da bangaren Latin Amurka, kuma za ta samar musu horo a bangaren aiwatar doka da shari’a bisa bukatunsu. Na karshe, muradun jama’a, inda karkashin haka Sin za ta samarwa dalibai 3500 na mambobin kawancen kasashen Latin Amurka wato CELAC tallafin kudin karatu cikin shekaru 3 masu zuwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An zabi Comrade Isma’il Ibrahim Dutse na ma’aikatar yada labarai a matsayin sabon shugaban kungiyar ‘yan jaridu NUJ ta kasa reshen jihar Jigawa ba tare da hamayya ba. A lokacin da yake sanar da sakamakon zaben, mataimakin shugaban kungiyar na kasa mai kula da shiyya ta daya wato Zone A, Comrade Tukur Umar Muhammad ya ce an kuma zabi Nura Sani Bello da Najib Umar da Aminu Umar Shuwajo ba tare da hamayya ba. Tukur ya ce Aisha Abba Ahmed ta kamfanin dillancin labarai na kasa NAN dake Dutse ta samu nasara da yawan kuri’u 46, shi kuma Abdullahi Mukhtar ya sami kuri’u 34, yayin da Larai Musa na NTA ta sami kuri’u 14. Tukur Umar, ya bayyana...
    Majalisar Wakilai ta yi watsi da kudurin dokar da ke neman sanya tsarin mulkin karba-karba a tsarin shugabancin Najeriya. Kudurin dokar na neman wajabta yin karba-karbar kujerar shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a tsakanin yankunan siyasan Najeriya guda 10.
    Kwamandan rundunar Amotekun a Jihar Ondo, Adetunji Adeleye, ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce ana ƙoƙarin ceto Adepoyigi. Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Ondo, Olushola Ayanlade, shi ma ya tabbatar da sace shugaban na APC, inda ya ce an sace shi a gonarsa da ke hanyar Ifon-Owo. Ya ƙara da cewa DPO na Ifon tare da mafarauta, ‘yan sa-kai da sojoji sun fara bincike domin gano inda aka kai shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A daidai lokacin da  sake bude yaki a Gaza ya cika kwanaki 57,sojojin HKI suna ci gaba da kai hare-hare akan al’ummar Gaza da hakan ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa da dama. Cibiyar watsa labaru ta Falasdinu ta sanar da cewa; Sojojin na HKI sun kai hare-hare masu yawa a sassa mabanbanta na gaza wanda ya fara tun daga watan Maris, da hakan ya kara jefa Falasdinawa cikin wahala, bayan yunwar da suke fama da ita. Da safiyar yau Talata sojojin na HKI sun kai hare-hare  sau 3 a garin Abasan a gabashin Khan-Yunus. A cikin birnin Gaza kuwa sojojin na HKI sun baje wasu gidaje da kasa a karo na uku. A garin Khan-Yunsu wani matashi mai suna Amid...
    A yau Talata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki a karon farko tun da ya zama shugaban kasa. Baya ga kasar Saudiyya shugaban kasar ta Amurka zai kuma kai Ziyara zuwa kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da zummar bunkasa alaka  da larabawan yankin tekun Pasha kamar yadda majiyar bangarorin biyu take ambatawa. Bugu da kari, kafafen watsa labarun Amurka sun ce, a yayin wannan ziyarar tashi, shugaban kasar Amurkan, zai yi kokarin samarwa kasarsa hannun jari da kasashen larabawa masu arziki za su zuba. Tun a baya dai Donald Trump ya bukacin ganin Saudiyya kadai ta kara yawan hannun jarinta a cikin Amurka da zai kai dala tiriliyan 1. Kafar watsa...
    A yau Talata ne dai aka bude taron karawa juna sani karo na 31 a birnin Mashhad wanda shi ne karo na 31 da zai mayar da hankali akan yadda za a ci moriyar wannan fasaha ta fuskokin zaman lafiya. Hukumar makamashin Nukiliya ta Iran ce dai ta tsara wannan taron kara wa juna sanin wanda ya sami halartar masana wannan fage. Wasu batutuwa da za a tattauna a wurin taron sun kunshi; Bututun tace sanadarin Uranium, shi kanshi makamashin da kuma hanyoyin tafiyar da da kula cibiyoyin dake aikin tace da sarrafa makamashin na Nukiliya.
    Sakamakon rikicin siyasa a jihar, ne ya sanya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakinsa, da dukkanin ‘yan majalisar dokar Jihar Ribas na tsawon watanni shida. Haka kuma, Shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas tare da naɗa mai riƙon kwarya da zai shugabanci jihar na tsawon wannan lokaci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ƙara da cewa dole ne ɗaliban da abin ya shafa su fice daga ɗakunan nan da zarar sun kammala jarrabawar zangon da ake ciki. Jami’ar ta ja hankalin iyaye da ɗalibai da su nemi ɗakunan kwana ne kawai daga cikin jerin waɗanda jami’ar ta amince da su, kamar yadda ofishin Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da Rayuwar Ɗalibai ya wallafa. Ta gargaɗe su cewa ba za ta ɗauki alhakin duk wani abin da zai faru a wajen da ba ta amince da shi ba ba. Haka kuma, jami’ar ta bayyana cewa tana aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an rufe ɗakunan bisa doka da oda. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Jami’an tsaro sun killace wajen da lamarin ya faru, kuma suna ci gaba da bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici wajen tantance daga inda ɗan takarar PDP zai fito ya janyo rabuwar kai a cikin jam’iyyar, lamarin da ya taimaka wajen rage ƙarfinta a zaɓen 2023. Masana siyasa na ganin wannan gargaɗi na Wike na iya sake haifar da muhawara a jam’iyyar, musamman yayin da ta ke shirin fuskantar babban zaɓen 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Masarautar Zazzau ta tabbatar da rasuwar Alhaji Ramalan Yero, mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Muktar Ramalan Yero. Sanarwar da ta fito daga bakin Sarkin Fadan Zazzau, Alhaji Abbas Ahmed Fatika, inda ya ce marigayin ya rasu da yammacin ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya. NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar s unguwar Kaura da ke cikin birnin Zariya, a Jihar Kaduna. Masarautar ta aike da ta’aziyyarta ga iyalan mamacin da ɗaukacin al’ummar Jihar Kaduna bisa wannan rashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    An gurfanar da wani mutum a gaban kotun Musulunci kan zargin yi wa matar maƙwabcinsa dukan kawo wuƙa a Jihar Kano. Mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotun da ke zama a unguwar Kurna Asabe cewa wanda ake zargin ya kuma ji wa matar auren munanan raunuka. Ya yi wa matar wannan aika-aika ne bayan wata taƙaddama, inda ya ji mata munanan raunuka a fuska da wasu sassan jikinta. Alƙalin kotun, Khadi Alhaji Jibrin Ɗanzaki, ya ba da umarnin tsare mutumin a gidan yari sannan ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga watan nan na Mayu. Ya kashe abokinsa saboda hula a Kano Matashi ya kashe saurayin ƙanwarsa a Kano NAJERIYA A YAU: Matsalar lantarki: ’Yan Najeriya sun...
    Babban hafsan hafsoshin sojojin JMI ya bayyana cewa sojojin kasar musamman sojojin ruwa a shirye suke su shigaba yaki dank are kasar a ko yauce, ya kuma kara da cewa idan makiya sun yi wani kuskure zasu yi nadamar hakan. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Manjo Janar Mohammad Hussain Bakiri yana fadar haka a jiya litinin a lokacinda shi da wasu manya manayan jami’an sojojin kasar suka kai ziyarar ganewa kansu irin shirin da sojojin kasar suke ciki a tashoshin jiragen ruwa da suke gabar tekun Farisa da kuma arewacin mashigar ruwa ta Hurmus Tare da manjo janar Bakiri dai akwai kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC  Manjo Janar Abdolrahim Mousavi, sai kuma Manjo Janar Hossein...
    Gwamnatin kasar Iran ta yi kakkausar suka ga gwamnatin HKI kan hare-haren da ta kaiwa wani sansanin yan gudun hijira a gaza inda ta kashe ko takai mutanen da dama ga shahada, daga ciki har da mata da yara jarirai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei yana fadar haka a jiya Litinin, a jawabinda ta saba gabatarwa a ko wace litinin. Esmaeil Baghaei ya kara da cewa nauyin MDD ce ta dakatar da kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza, kuma kasa yin haka wani abin kunya ne ga majalisar. Ya kuma kara da cewa ya zama wajini kutunan kasa da kasa wadanda suka hada da ICJ ta...
    Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kasin ya bayyana cewa kungiyarsa ba zata mika kai don takurawa da kuma matsin lambar da takewa gwamnatin kasar Lebanon don kawo karshen kungiyar ba. Tashar talabijin ta Almanar ta nakalto Sheikh Qasim yana fadar haka a jiya litinin, a wanijawabinda ya yi ta tashar talabijin ta AL-Amnar na kungiyar don tunawa da babban kwamandar kungiyar Sayyed Mustafa Badreddin wanda yayi shahada shekaru 9 da suka gabata. Sheikh Kasim ya kara da cewa kungiyar tana kan al-kawalinda na tsagaita budewa juna wuta duk tare da cewa HKI ta keta wannan yarjeniyar har sau 3000. HKI dai ta amince da tsagaita budewa juna wuta bayan fafatawa da kungiyar Hizbullah na tsawon watanni 14,...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudia a wani tafiya ta musamman don samar da kuded da kuma harkokin kasuwa ga Amurka a yankin Gabas ta tsakiya. Trump  zai ziyarci wasu kasashen larabawa a yankin, wadanda suka hada da Qatar da HDL da kuma Turkiya inda ake saran zai tattauna dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine tare da shugaban  kasar Turkiyya Rajab Tayyid Urdugan. Shugaban yana zuwa yankin ne a dai-dali lokacinda HKI ta ci gaba da kissan kiayashi ga Falasdinawa a Gaza da kuma hana abinci shiga Gaza. Shugaban ya sami labarin saken wani ba’amerike mai suna Edan Alezander wanda yake tsare a hannun kungiyar Hamas tun shekara ta 2023. Kungiyar Hamas...
    Gwamnatin kasar Burtaniya ta gabatarwa majalisar dokokin kasar sabbin tsare-tsare na shigar kasar ta hanyoyi daban-daban. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Firai ministan kasar ta Burtania Keir Starmer yana fadar cewa abinda yake gabatarwa Majalisar don neman amincewarta, wani tsari ne wanda zai kawo tsabta a harkokin bada Visar shiga kasar Burtaniya daga kasashen duniya daban-daban. Starmer ya kara da cewa kafin haka tsarin shige da fice a kasar ta zama a tarwatse yake. A halin yanzu bayan samar da wadannan tsare-tsare masu zuwa kasar Burtania ko wadanda suke son zama a kasar dole ne su zama masu amfanar kasar,. Da farko dole su iya turancin ingishi da wasu abubuwan da zasu taimawa ci gaban kasar. Kafin haka...
    Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke hukuncin ratayewa ga wani mutum da ta samu da laifin kashe abokinsa saboda hula. Kotun da ke zamanta a kan titin Miller ta yanke wa mutumin mai suna Adamu Isma’ila Arzai hukuncin ne bayan an gurfanar da shi kan zargin soka wa abokinsa mai suna Auwal Shehu Kabara wuƙa a lokacin da suke faɗa. A shekarar 2016 ne faɗa ya kaure tsakanin abokan biyu a kan wata hular sanyi a lokacin da suka yi wata tafiyar fatauci a Jihar Bauchi. A yayin zaman kotun, mai gabatar da ƙara, Wahida Isma’il, ta gabatar da shaidu biyar, shi kuma wanda ake tuhuma ya kare kansa. Matashi ya kashe saurayin ƙanwarsa a Kano NAJERIYA A YAU: Matsalar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wasu ’yan Najeriya sun yi Allah-wadai da umarnin da Hukumar Kula da Harkar Wutar Lantarki a Najeriya (NERC) ta bai wa kamfanonin rarraba wutar da su biya diyya ga abokan huldarsu da ke rukunin Band A. NERC ta bai wa kamfanonin wannan umarni ne sakamakon rashin samar wa ’yan Band A ɗin wutar lantarki na aƙalla sa’a 20 a kullum a watan Afrilu. A cewar waɗanda suke kan rukunin Band B zuwa ƙasa, matsalar wutar ba ta keɓanci ’yan Band A kaɗai ba, galibi ma su suka fi ɗanɗana kuɗarsu saboda rashi wutar. Ko me ya sa rukunin Band A ne kawai za su amfana da wannan diyya? NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin...
    Kasar Sin ta harba wani rukunin taurarin dan adam daga cibiyar harba tauraron na Taiyuan dake lardin Shanxi na arewacin kasar. An harba taurarin ne jiya Lahadi da misalin karfe 9:27pm agogon Beijing, bisa amfani da samfurin rokar Long March-6 da aka yi wa ‘yan gyare-gyare. A cewar cibiyar ta Taiyuan, rukunin taurarin mai suna Yaogan-40 02, ya shiga da’irarsa cikin nasara. Za a yi amfani da taurarin ne wajen gwaje-gwajen fasahohi da gano yankuna masu tasirin haduwar maganadisu da lantarki. Aikin na jiya shi ne karo na 574 da aka yi amfani da samfurin rokar Long March. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Dangin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukar matakin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, da kuma ƙara tura jami’an tsaro zuwa yankin. Harin ya zo ne a lokacin da ake samun ƙaruwar ayyukan ‘yan ta’adda a wasu sassan ƙasar, musamman a yankin Arewa-Maso-Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta amince da kashe naira biliyan 2 da miliyan 300 domin sayo  na’urar binciken cututtukan zuciya (cardiac catheterization machine) a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.   Ministan Lafiya da Jin Daɗin Al’umma, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai bayan zaman majalisar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja.   A cewar ministan, wadannan kayan aiki na zamani za su taimaka matuka wajen aikin gano cutar da kuma warkar da cututtukamasu alaƙa da zuciya.   Ya bayyana cewa hakan  wani mataki ne na  gwamnatin tarayya don ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya na musamman a yankin Arewa maso Yamma da kuma rage bukatar zuwa ƙasashen waje...
    Mataimakin firaminsitan kasar Sin He Lifeng, ya gana da babbar jami’ar hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, a daren jiya Lahadi a Geneva. Yayin ganawar tasu, He ya ce, kamata ya yi mabambantan bangarori su daidaita bambancin ra’ayi da takaddama bisa shawarwari, kuma cikin adalci karkashin ka’idar WTO. Haka kuma, a hada hannu wajen kiyaye manufar daidaita harkoki tsakanin mabambantan bangarori da yin ciniki cikin ’yanci, don gudanar tsarin sana’o’i da na samar da kayayyaki a duniya yadda ya kamata. Ya ce Sin za ta ci gaba da taka rawa cikin kwaskwarimar da za a yiwa WTO a dukkan fannoni, kuma tana goyon bayan WTO ta bayar da gudunmawa a matsayin mai ba da tabbaci ga raya...
    Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Liman Dahiru, ya kaddamar da wani shiri na kiwon lafiya domin inganta kula da lafiya ga mazauna gundumar Makera.   Shugaban majalisar zai sanya mutane 700 da suka fito daga gundumar cikin Tsarin Kiwon Lafiya na Hadin Gwiwa na Jihar Kaduna (KADCHMA), matakin da ake sa ran zai kara yawan mutanen da ke da inshorar lafiya a yankin.   An yi hakan ne da nufin bai wa jama’a damar samun kula da lafiya mai inganci cikin sauki, domin inganta jin dadinsu baki daya.   A shirye-shiryen kaddamar da shirin, Shugaban Ma’aikata na Shugaban Majalisar, Honarabul Bashir Adamu Nababa, ya gana da Darakta-Janar na KADCHMA, Mallam Abubakar Hassan, inda suka tattauna kan...
    Ɓarkewar cutar kwalara ta yi ajalin mutum huɗu yayin da wasu gommai suka kwanta jinya a yankunan Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato. Aminiya ta ruwaito cewa yankunan da abin ya shafa sun haɗa da Hurti, Bokkos ta Yamma, Bokkos ta Tsakiya da kuma Mangol. ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 5 a Filato Jami’ar Maryam Abacha ta rufe ɗakunan kwanan ɗalibai a Kano Galibin waɗanda ake zargi sun harbu da cutar an killace su a cibiyoyin lafiya a matakin farko daban-daban da kuma Asibitin Cottage inda suke samun kulawar gaggawa. Shugaban Ƙaramar Hukumar Bokkos, Mista Amalau Samuel Amalau wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce suna aiki tare da mahukuntan asibitin domin daƙile ƙalubalen A cewarsa,...
    A yau Litinin, mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, Sin da Amurka sun cimma matsaya tare da fitar da sanarwar hadin gwiwa bayan taron kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, inda ya kara da cewa, hakan wani muhimmin mataki ne da bangarorin biyu suka dauka na warware sabaninsu ta hanyar yin shawarwari da tuntuba bisa daidaito, tare da aza tubali da samar da yanayi na kara dinke baraka da zurfafa hadin gwiwa. Daga bangarenta kuwa, Darakta-Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, a jiya Lahadi ta bayyana cewa, ta yi farin cikin ganin an samu sakamako mai kyau yayin taron kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. A cikin...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba yin watsi da haƙƙinta na makamashin nukuliya na zaman lafiya ba a kowane yanayi Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran da gaske take yi wajen gudanar da tattaunawa domin neman cimma matsaya da zata gamsar da kowane bangare, amma neman yin watsi da cibiyoyin nukiliyarta ba abu ne da za a amince da shi ba. A yammacin jiya Lahadi ne jami’an gwamnatin kasar Iran suka gudanar da wani taro karkashin jagorancin shugaban kasar Masoud Pezeshkian, inda ya jaddada aniyar gwamnatin kasar na kare nasarorin da Iran ta a fagen ayyukanta na zaman lafiya, yana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba neman mallakar makamin...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar Iran da Amurka ba zata shafi matakin jan layi da Iran ta gindaya ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa da gaske kasarsa tana tattaunawa da Amurka, kuma tana neman cimma matsaya, amma batun neman yin watsi da cibiyoyin nukiliyarta wani zabi ne da ba za a taba amincewa da shi ba. A cikin rashin tabbas da ke tattare da ci gaba da aiwatar da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka, biyo bayan cin karo da maganganun da jami’an fadar mulkin Amurka ta White House suka yi, da kuma karuwar bukatar Amurka kan Iran; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kawo karshen matsin lambar da ake yi mata; Yayin da shugaban Iran Masoud...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun aiwatar da mummunan kisan kiyashi a garin Jabaliya, tare da janyo shahada da jikkatan wasu a Khan Yunis A rana ta 56 da sake komawa yaki ta hanyar kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da yin luguden wuta kan wasu wuraren zama, da matsugunan ‘yan gudun hijira da suke Gaza, a matsayin matakin farko na hare-harensu a yau Litinin. Bayan nan Sojojin mamayar sun farma garin Jabaliya da ke arewacin zirin Gaza, inda suka kai wasu munanan hare-hare kan garin da jiragen saman yaki da suka aiwatar da mummunan kisan kiyashi a makarantar Fatima Bint Asad, da ya zama mafaka ga ‘yan gudun hijira. Hare-haren bama-bamai biyu da...
    Kasar Siriya ta rikide daga Jihadi da zaluncin gwamnatin mamayar Isra’ila zuwa ga kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin ‘yan mamaya Gaskiya ta fara bayyana daya bayan daya, sannan makirci da makarkashiyar kungiyoyin masu dauke da makamai bisa da’awar gudanar da jihadi a Siriya suka fara bayyana ga al’umma, masu da’awar jihadi sun kama hanyar fitar da Siriya daga cikin sahun masu fada da makirce-makircen yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya ta hanyar kulla kyakkyawar alaka da su, da janyewa daga duk hakkokin kasar Siriya da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta mamaye na Siriya a baya-bayan nan. Manufar samar da sabuwar gwamnatin masu da’awar jihadi, kamar yadda aka sani, ita ce tabbatar da tsaron babban sansanin Amurka mafi girma a yanking abas ta tsakiya,...
    Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutane biyar yayin da suka kai hari ana tsaka da cin kasuwa a ƙauyen Dogon Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato. A cewar mazauna, maharan sun wawushe kayayyaki a shaguna inda suka yi awon gaba da kayan abinci da magunguna masu tarin yawa. Jami’ar Maryam Abacha ta rufe ɗakunan kwanan ɗalibai a Kano Awakin da ke rayuwa sama da shekaru 200 a inda babu ruwa Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun kai hari kan kasuwar ce mai tara ɗaruruwan mutane da ke zuwa daga gari-gari makwabtaka domin baza hajoji iri-iri musamman kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, fulawa, wake, lemuka da sauransu. Shafi’i Sambo, wani shugaban matasa...
    Wani hari kan gidan yarin Al-Obeid yayi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane da dama a kasar Sudan Ministan al’adu da yada labarai, kuma kakakin gwamnatin Sudan, Khaled Al-Aiser, ya tabbatar da cewa: Mutane 20 ne suka mutu, yayin da wasu 50 na daban suka jikkata a wani harin da ‘yan ta’addar Daglo na  kungiyar Rapid Support Forces masu aikata laifuka suka kai hari kan gidan yarin Al-Obeid. Al-Aiser ya bayyana cewa: Harin da aka kai ya hada da asibitin birnin, inda ya yi sanadin mutuwar mutane musamman majinyata masu yawa tare da raunata wasu kimanin 50, wadanda dukkansu fararen hula ne, yana mai cewa wannan yana daga cikin manyan laifukan yaki. Ministan ya kara da cewa: “Abin da ya faru...
    Jami’ar Maryam Abacha MAAUN ta rufe wasu gidaje biyu da ke zaman ɗakunan kwanan ɗalibanta mata a Jihar Kano. Hukumar gudanarwar jami’ar ta rufe ɗakunan kwanan ɗaliban da ke unguwar Hotoro da titin UDB a Kano saboda zargin rashin ɗa’a. Awakin da ke rayuwa sama da shekaru 200 a inda babu ruwa Za mu ci gaba da aikin haƙo ɗanyen mai a Arewa —NNPCL Wannan jami’i da ke kula da ɗakunan kwanan, Hamza Garba, ya ce an ɗauki matakin ne a ƙoƙarin da jami’ar take yi na tabbatar da aminci da tsaro da kuma daƙile duk wata kafa ta aikata masha’a a tsakanin ɗalibai. Jami’ar ta ce cikin dalilan da ta ɗauki wannan mataki akwai ayyuka na rashin ɗa’a, ƙarancin...
    Yayin da ake cika shekaru 10 da kaddamar da dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Latin Amurka watau China-CELAC Forum, kafar yada labarai ta CGTN da hadin gwiwar jami’ar San Martin de Porres da cibiyar nazarin siyasa da tattalin arzikin kasar Sin ta Latin Amurka da jami’ar Santiago de Chile, sun fitar da wani sakamakon nazari da aka yi kan mutane 2,500 a fadin kasashe 10 na Latin Amurka. Sakamakon nazarin ya nuna cewa, masu bayar da amsa sun amince da manufa da nasarorin da aka cimma na zamanantar da kasar Sin, tare da gamsuwa da dangantakar Sin da kasashen Latin Amurka. Al’ummar Sin da Latin Amurka mai makoma ta bai daya na kara samun goyon baya daga mutanen yankin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kasar Sin za ta sauya matsaya kan adadin harajin fito da ta ayyana kan hajojin dake shiga kasar daga Amurka karkashin sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 4 ta 2025, ta hanyar dage karin kaso 24 bisa dari a wa’adin farko na kwanaki 90, tare da wanzar da karin kaso 10 bisa dari kan kayayyakin, da jingine sauyin harajin fiton karkashin tanajin sashen haraji na hukumar kwastam mai lambar 5 na 2025, da sanarwar sashen haraji na hukumar kwastam mai lamba 6 na 2025. Kazalika Sin za ta aiwatar da dukkanin matakai na hukuma wajen dage sauran matakan ramuwar gayya da ba na karin haraji ba da ta ayyana kan Amurka tun daga ranar 2 ga watan Afirilun...
    Ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar mazabar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya bar jam’iyyar NNPP ya koma APC. A cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban majalisar, Hon. Ismail Falgore, Masu ya bayyana cewa rikice-rikice da shari’o’in cikin NNPP a matsayin dalilin ficewarsa. Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar 2027: PDP Ta Mutu, APC Na Shirin Sake Yin Nasara – Martanin Ganduje Ga Lamido  Shugaban majalisar ya karanta wasiƙar a zaman majalisa na ranar Litinin, inda ya bayyana cewa Masu ya fice daga NNPP tun daga ranar 12 ga Mayu, 2025, kuma ya samu amincewa ga shugabannin APC a dukkan matakan da suka dace su karɓe shi. Ɗan majalisar ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabbin Kwamishinonin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kafin fara taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya a fadar gwamnati da ke Abuja.   Sabbin Kwamishinonin INEC din da aka rantsar su ne Mallam Tukur Yusuf, mai wakiltar yankin Arewa maso Yamma, da Farfesa Sunday Aja, mai wakiltar Jihar Ebonyi.   Haka kuma, an rantsar da mambobi biyu na Hukumar Da’a ta Kasa (CCB).   Mambobin su ne Ikpeme Ndem, daga Jihar Cross River, da Mai Shari’a Buba Nyaure mai ritaya, daga Jihar Taraba.   Daga Bello Wakili.        
    Sojojin sun kuma kwato mujallun AK-47 guda biyar da sauran makaman yaki daga a yayin artabun.   Majiyoyin sojin sun bayyana cewa, farmakin wani sabon shiri ne na sake tarwatsa shirin ‘yan ta’addan da kuma dakile hanyoyin da suke amfani da su wajen kai muggan hare-hare a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masana kimiyya suna ƙoƙarin fahimtar yadda garken awaki ke rayuwa a wani tsibiri da ke Arewa maso gabashin Brazil fiye da ƙarni biyu (shekara 200) ba tare da samun tsaftaccen ruwan sha ba. Ba a fayyace yadda ainihin awakin suka hau saman tsaunin Santa Barbara tun a farko ba, wanda ɗaya ne daga cikin tsibirai biyar masu aman wuta da suka haɗa da tsibiran Abrolhos, kimanin kilomita 70 daga gaɓar tekun Bahia, amma masana kimiyya sun yi imanin cewa, ’yan mulkin mallaka ne suka kawo su, suka bar su a wurin. Za mu ci gaba da aikin haƙo ɗanyen mai a Arewa —NNPCL Yaran Bello Turji sun ƙwace garin su tsohon Gwamnan Sakkwato, Bafarawa Dabbobi kamar irin su awaki da...
    Rukunin farko na maniyyata dari biyar da sittin (560) daga jihar Kwara tare da jami’an hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON su biyu, sun tashi daga Filin Jirgin Sama na na Babatunde Idiagbon da ke Ilori zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025. Yayin da yake jawabi ga maniyyatan kafin tafiyarsu, Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukace su da su kasance masu kamun kai da kuma wakiltar jihar da kasa Najeriya. Gwamna AbdulRazaq, wanda mai ba shi shawara ta musamman, Alhaji Saadu Salaudeen, ya wakilta, ya yi kira ga dukkan maniyyata 2,174 daga jihar da su yi addu’a domin zaman lafiya da hadin kai a jihar da kuma kasa baki daya. Gwamnan ya kuma gargadi maniyyatan da...
    Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin Naira 830 zuwa N835 kan kowacce lita.   Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin mako guda a cikin watan Afrilu, inda ta rage farashin man ta daga N880 zuwa N835 kan kowace lita.   Ana kyautata zaton cewa, ragin na da nasaba da sabunta tsarin sayen danyen mai da takardar Naira, biyo bayan dakatarwar da aka yi na wucin gadi.   Kokarin samun wata sanarwa a hukumance daga Kakakin Rukunin Dangote, Anthony Chiejina, kan batun rangwamen ya ci tura...
    ‘Hudu daga cikin ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran sun isa birnin Jakarta na kasar Indonesia domin halartar taron majalisun kungiyar kasashen musulmi. A yau Litinin ne dai aka bude taron majalisun kasashen kungiyar kasashen musulmi a birnin Jakarta na kasar Indonesia wanda shi ne karo na 19. Taken da aka bai wa taron karo na 19 shi ne: “Kafa Gwamnatoci masu hikima a kuma cibiyoyi masu karfi a matsayin ginshikin jajurcewa.”  Tawagar ta Iran dai wacce Ruhullah Mutafakkir Azad yake jagoranta, ta kuma kunshi Sara Fallahi, Sayyid Yahya Sulaimani, da Muhammad Mahdi Shahriyari. Taron zai ci gaba har zuwa ranar 15 ga watan nan na Mayu da ake ciki, kuma tawagar ta Iran za ta gabatar da jawabi a...
    Yayin da a wannan Litinin ake bikin ranar jami’an jinya ta Duniya ta shekarar 2025, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai kashi 42 cikin 100 na ma’aikatan jinya a Afirka, dake cike da burin ficewa daga nahiyar saboda rashin cikakkiyar kulawa da kuma albashi mara tsoka. A jawabin da ya gabatar akan ranar ma’aikatan jiniya ta duniya, Daraktan riƙo na Hukumar ta WHO a Afirka, Chikwe Ihekweazu, ya ce ficewar tasu za ta nakasa harkokin kiwon lafiyar da ake riritawa a nahiyar. Ihekweazu ya cigaba da cewa wannan ɓangare na masu aikin jinyar na da matuƙar muhimmanci ga ɗaukacin al’umma, don haka bashi kulawa, abu ne da ya dace, domin zai ba da gudunmawa ga cigaban ɓangaren lafiya,...
     Kungiyar Kurdawan Turkiya PKK ta sanar da cewa za ta ajiye makamanta ta kuma rusa kanta. Kamfanin dillancin labarum “Furat” mai kusanci da kungiyar ta PKK, ya nakalto cewa; Kungiyar ta yanke zartar da wannan matakin ne a yayin taron da ta yi kaso na 12 da ta yi kwanaki kadan da su ka gabata. Sanarwar ta PKK ta kuma kunshi cewa;Jam’iyyun siyasa na kurdawa za su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa domin bunkasa tsarin demokradiyya da sake gina al’ummar Kurdawa.” Haka nan kuma PKK ta ce, da akwai alakar a sake Shata salon alakar Kurdawa da Turkiya. A martanin da jam’iyyar dake Mulki a Turkiya ta fitar, ta bayyana cewa;  Zartar da  matakin da kungiyar...
    Saraki, shi ne zai jagoranci kwamitin sai kuma ƴan kwamitin da suka haɗa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare; gwamnan jihar Filato, Caleb Muftiwang da kuma gwmanan jihar Enugu, Peter Mba.   Sauran ƴan kwamitin sun haɗa da Sanata Seriake Dickson da Sanata Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Abia, Chif Okezie Ikpeazu.   Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da gwamnonin Enugu da Zamfara da Adamawa da Taraba da Osun da Oyo.   Ministan babban birnin tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike shima ya je taron sai kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Maƙarfi.   Suma ƴan jam’iyyar irin su Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Sule Lamido da Samuel Ortom da Gabriel Suswan da Seriake...
    Dubun wani ɗan daba da ƙwacen waya da satar babura a cikin shigar mata mata wajen aikata ayyukan laifinsa a unguwar Ɗorayi da ke Jihar Kano ta cika. An kama matashin mai suna Abdullahi, wanda aka fi sani da “Audu Manye,” ne bayan tsawon shekaru ana zargin sa da tunzura faɗan ’yan daba, fashi da makami da ƙwace wayoyi da satar babura a yankin. Audu Manye ya shafe shekaru ya tsere wa jami’an tsaro ta hanyar yin shigar mata da hijabi da siket da da niƙabi, inda yake shiga cikin mata ba tare da an gane shi ba a yayin da yake aikata laifukansa. Amma a ranar Laraba, dubunsa ta cika, inda haɗin gwiwar ƙungiyar “Gamayyar Matasan Kano,” tare da...
    Shugaba da mataimakinsa an tsige su ne kan zargin almundahana, rashin ɗa’a, rashin mayar da hankali kan aiki da kuma cin zarafin ofisoshinsu.   Kafin masa wannan naɗin riƙon kwarya, Wali ya kasance Kansila da ke wakiltar gundumar Tumfafi kuma shi ne ya kasance shugaban Kansiloli na ƙaramar hukumar.   Gwamnatin jihar Bauchi ce ta sanar da rasuwar nasa a ranar Lahadi ta cikin sanarwar manema labarai da kakakin gwamnan jihar, Mukhtar Gidado, ya fitar.   Da ya ke miƙa ta’aziyyasa ga iyalan mamacin, gwamna Bala Muhammad ya misalta marigayin a matsayin jajirtaccen mutumin da ya hidimta wa jama’a tare da bayar da gudunmawarsa wajen kawo cigaba a ƙaramar hukumar Shira da ma jihar Bauchi.   Gwamnan ya yi addu’ar...
    Ɗan Majalisar Wakilai, Honorabul Yusuf Gadgi, ya yi iƙirarin cewa mayaƙan Boko Haram sun ƙwace makaman sojoji da kuɗaɗensu ya kai tiriliyoyin naira a hare-haren da kungiyar ta kai kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas. Gadgi ya bayyana haka ne a yayin da yake tsokaci kan ƙudirin da Honorabul Ahmed Satomi daga Jihar Borno ya gabatar a zauren Majalisar, kan gobarar da ta tashi a ma’ajiyar makamai ta rundunar soji da ke Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri da kuma ƙaruwar hare-haren Boko Haram a jihohin Borno da Yobe a baya-bayan nan. Ɗan malisar ya ce yawan yadda ’yan ta’adda ke lalata kayan yaƙin sojoji a yanzu, ba a taɓa ganin irinsa ba a baya. Ya ƙara...
    Lamido a ranar Lahadi ya ce, “Ina da yakinin cewa duk wadanda suka bar PDP za su dawo ciki har da Ganduje, domin nan ba da dadewa ba APC za ta balle ta rabu gida biyu, saboda tana rungumar mutane masu tunani daban-daban.   “Na fadi haka, kuma ina sake maimaitawa: nan da watanni shida, duk wadanda suka koma APC za su dawo, kuma PDP za ta farfado da karfi don kwace mulki a 2027.”   A wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin ta hannun sakataren yada labaransa, Edwin Olofu, shugaban jam’iyyar APC na kasa ya yi watsi da ikirarin da cewa, hakan ba zai yi wu ba.   Ganduje ya ce maimakon ya koma PDP, Lamido...
    ’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa. ’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna Danbakolo ne ya jagoranta, ya kuma shafi ƙauyukan Gebe, Kamarawa, Garin Fadama da Haruwai. Ana zargin harin da aka kai da kusan ƙarfe 11 na safe ran Asabar, martani ne ga ayyukan sojoji na baya-bayan nan da suka yi niyyar fatattakar ’yan bindiga a yankin. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO NDLEA ta kama matar da ta ɓoye hodar iblis...
    ’Yan bindiga sanye kayan ’yan sanda sun kai hari a wata makarantar sakandaren gwmanati inda suka harbe wani malami har lahira sannan suka sace mata uku a Jihar Zamfara. Cikin matan da aka sace har da matar malamin a wannan mummunan lamari ya faru a Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Raka, a ranar Asabar. Wani jami’in gudanarwa na makarantar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa maharan sun shiga harabar makarantar ne ta wata ƙofa da ke bayan katangar makarantar. “Sun mamaye harabar makarantar sanye da cikakkun kayan ’yan sanda, da hula da takalman roba. Sun yi amfani da kofar da ke bayan katangar wajen shiga da kuma guduwa bayan harin,” in ji shi. Rahotanni sun nuna...
    ’Yan bindiga da ake zargin yaran fitaccen jagoran ’yan bindiga Bello Turji ne, sun ƙwace yankin Bafarawa, garin su tsohon gwamna Attahiru Dalhatu Bafarawa. ’Yan bindigar sun kai harin tare da ƙwace wasu ƙauyuka huɗu ne a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato. Harin, wanda ake zargin wani kwamandan Turji mai suna Danbakolo ne ya jagoranta, ya kuma shafi ƙauyukan Gebe, Kamarawa, Garin Fadama da Haruwai. Ana zargin harin da aka kai da kusan ƙarfe 11 na safe ran Asabar, martani ne ga ayyukan sojoji na baya-bayan nan da suka yi niyyar fatattakar ’yan bindiga a yankin. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO NDLEA ta kama matar da ta ɓoye hodar iblis...
    Kwamitin ya kuma haɗa da Honarabul Sulaiman Adamu Gummi, Kwamishinan Al’amuran Addinai, wanda ke riƙe da muƙamin mataimakin shugaba, sai kuma Alhaji Habibu Balarabe, Babban Sakataren Hukumar Zakka, a matsayin sakatare.   Yayin ƙaddamar da kwamatin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ana sa ran tawagar za ta tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da walwala, aminci da jin daɗin alhazan Jihar Zamfara.   “Gwamnatin Jihar Zamfara, a madadin al’ummarmu, ta ba ku kwarin gwiwa sosai wajen ganin an aiwatar da kowane fanni na aikin Hajjin 2025 cikin inganci, mutunci, da gaskiya.   “Ina kira gare ku da ku ci gaba da ƙulla kyakkyawar alaƙa da Hukumar Alhazai ta Jihar Zamfara, da hukumomin Tarayyar da abin ya shafa, da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin JMI da Amurka zagaye na hudu, yana tafiya kamar yadda ya dace. Kuma kasashen buyu sun kara fahintar ra’yin juna. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran da nakalto Aragchi yana fadar haka a wani hira da da ya gabatar bayan kammala zagaye na 4 na tattaunawar a jiya. Ministan y ace bangarorin biyu sun tattauna babututuwan da suke da zurfi a cikin matsalolin da kasashen biyu suke son su warware, na farko gamsar da Amurka kan cewa shirin makamashin Nukliya na kasar Iran ban a tsaro bane. Da kuma maganar daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. Yace tattaunawar jiya   yafi...
    Sojojin HKI sun ci gaba da kai hare hare kan birane da garuruwan yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, hare-haren jiya sum sun fi maida hankali ne a garin Tulkaram da kuma sansanin yan gudun hijirar yankin A wannan karomma sojojin HKI sun bada umurni ga ma zauna garin Tullaram mata da maza da yara da tsoffi duk su fice daga gidajensu. Kwanaki 105 da suka gabata ne gwamnatin HKI ta fara wannan shirin na korar falasdinwa da kuma rusa gidajensu da nufin korarsu kwatakwata daga yankin. MDD ta bayyana a baya ya zuwa yanzu sun kori falasdinawa kimani 40,000 daga gidajensu, inda suka rusa su suka kuma . A wani...
    Kungiyar Magajunan Gari Na Kasashen Asiya Ta Zabi Birnin Esfahan na tsakiyar kasar Iran a matsayin cibiyar yawan bude ido na wannan shekara ta 2025. Manufar zaben birnin Esfahan a wannan karon shi ne gabatar da shi ga kasashen Asiya saboda sa mutanen Nahiyar Asiya su su ziyarci kasar da kuma birnin don sanin dumbin wuraren tarihin da suke cikin birnin da kuma kewayensa. Labarin ya bayyana cewa birnin Esfahan ayana daga cikin birane mafi tsufa a kasar , sannan yana dauke da wuraren kallo da kuma bude ido a cikin birnin Har’ila yau labarin ya kammala da cewa ana da kayakin tarihi kimani 200,000 a cikin birnin, sannan wasu 1940 na kayakin tarihin kasar, hukumar UNESCO ta zama wurare...