Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Kafa Dokar Karba-karba A Shugabancin Nijeriya
Published: 17th, May 2025 GMT
Sai dai dan majalisar wakilai Ali Isah na (PDP, Gombe), bai amince da matsayin Madaki ba. Ya ce sanya shugaban kasa na a tsarin karba-karba a cikin kundin tsarin mulkin kasar zai samar da adalci da sanin ya kamata ga dukkan shiyyoyin siyasar kasar nan.
Dan majalisa Sada Soli na (APC, Katsina), yayin da yake adawa da kudurin, ya ce dokar da aka gabatar “Na da illa sosai ga hadin kan kasa.
Ya ce sanya ka’idar shugabancin karba-karba a cikin kundin tsarin mulkin kasar zai kai ga samar da abubuwa bisa cancanta.
“Hakan zai iya sanya muradun yanki da na kabilanci a gaba su zamo mafi cancanta. Zai karfafin zabin mutanen da za su iya tsayawa takara kuma zai kara kwarin gwiwa wajen fafatawa a yankin da ake samun karancin hadin kai,” in ji Soli.
Sai dai Kalu yayin da yake mayar da martani ga matsayin Soli, ya yi watsi da muhawarar da ake tafkawa a kan neman karagar mulkin, inda ya kara da cewa duk yankin siyasar kasar nan na da kwararrun mutane da za su iya samu nasarar shiga fadar shugaban kasa da mataimakinsa.
Ya ce, jigon kudirin dokar shi ne a tabbatar da cewa kowane bangare na kasar nan ya samu damar bayar da gudunmawa wajen gudanar da mulki da ci gaban kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ganduje ya halarci Majalisar Wakilai don sheda ’Yan Majalisa 2 zuwa APC
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci zauren Majalisar Wakilai a ranar Alhamis domin ganewa idanunsa ficewar wasu mambobi biyu na Jam’iyyar adawa ta NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
’Yan majalisar biyu, sun haɗa da: Dan Majalisar Wakilai, Abdullahi Sani Rogo mai wakiltar mazaɓar Rogo/Karaye da kuma Ɗan Majalisar Wakilai Kabiru Alhassan Rurum mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Rano/Bunkure/Kibiya, sun sauya sheƙa a ranar Alhamis.
Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato Dalilin da ya sa gwamna Bala ya yi ƙoƙarin mari na – In ji MinistaHakazalika mamba mai wakiltar mazaɓar Ijesha Oriade/Obokun na Jihar Osun, Wole Oke, ya kuma bayyana ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC.
Shugaban Majalisar Wakilai Tajudden Abbas wanda ya sanar da sauya sheƙar, ya bayyana cewa mambobin sun bayyana dalilansu na ficewa daga jam’iyyarsu zuwa APC.
Sai dai Babban mai tsawatarwa na Marasa Rinjaye, Isa Ali JC, ya nuna rashin amincewarsa da cewa sauya sheƙar ya sabawa kundin tsarin mulkin ƙasar.
Ganduje wanda ya samu rakiyar wasu jami’an jam’iyyar, ya fice bayan sanarwar.