Rikici Tsakanin Faransa Da Aljeriya Ya Shiga Wani Sabon Salo Na Koran ‘Yan Kasashen Juna Daga Kasashensu
Published: 17th, May 2025 GMT
An samu bullar rikicin da ba a taba ganin irinsa ba a dangantaka tsakanin Aljeriya da Faransa
Rikicin ma’aikatan harkokin diflomasiyya tsakanin Aljeriya da Faransa ya dawo kan gaba a fagen dakaddamar da ke tsakaninsu.
Rikici dai na kara kamari ne tsakanin Aljeriya da Faransa, tun daga rikicin korar ‘yan kasar Aljeriya daga Faransa zuwa rikicin korar ma’aikatan diflomasiyyar Faransa daga Aljeriya.
Wannan kiran ya biyo bayan maimaita cin zarafi mai tsanani da bangaren Faransa ya yi ne, yana wakiltar keta doka da aka kafa da kuma keta tsarin al’ada don nada ma’aikata a ofisoshin diflomasiyya da na ofishin jakadancin Faransa da aka amince da su a Aljeriya.
Akalla ma’aikatan Faransa 15 ne aka nada don gudanar da ayyukan diflomasiyya ko na ofishin jakadancin a kasar Aljeriya, ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba, gami da sanarwa a hukumance ko kuma ba da izini, kamar yadda ka’idoji da yarjejeniyoyin kasa da kasa suka bukata.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Aljeriya da
এছাড়াও পড়ুন:
Salon Zamanantarwa Na Sin Kyakkyawan Misali Ne Ga Kasashen Afirka
Tabbas fannonin zamanintar da kai na Sin na iya zama babbar taswira da kasashen Afirka ka iya bi, wajen kaiwa ga bunkasa yankuna, da kyautata zamantakewar al’ummunsu, da samar da isassun damammaki na gudanar da kyakkyawar rayuwa mai cike da walwala ga al’ummun nahiyar.(Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp