Jami’an tsaro sun daƙile harin Boko Haram sun kashe mayaƙa 5 a Borno
Published: 17th, May 2025 GMT
Sojoji da mafarauta don halaka mayaƙan Boko Haram biyar tare da daƙile wani hari da ’yan ta’addan suka kai a ƙauyen Warambe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.
Warambe na daga cikin yankunan da mazanaunansu suka dawo da zama a baya-bayan nan, kuma mayaƙan Boko Haram sun sha yin yunƙurin kurɗawa cikinsa.
Shugaban mafarautan wanda ɗan asalin garin ne ya ce a safiyar Juma’a ne maharan suka nemi shiga ƙauyen, “amma muka gana su, muka kashe mutum biyar daga cikinsu. An miƙa makaman da muka ƙwato daga hannunsu ga sojoji.”
Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Kudancin Borno, ya jinjina wa ƙoƙarin jami’an tsaron, musamman wajen ɗaukar mataki cikin gaggawa yana mai ba su ƙwarin gwiwar su ƙara jajircewa.
Mutum 3 sun mutu, 21 sun jikkata a turmutsitsin karɓar kuɗin tallafi a Borno Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a TarabaSanata Ndume yace ce, “ina farin cikin sanar da ku cewa an kashe ’yan ta’adda biyar a ƙauyen Warambe. Ina kunjinjina wa mafarauta da kuma yadda aka yi saurin ɗaukar matakin tura sojojin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ zuwa wurin, wanda ya ƙara wa al’ummar yankin ƙwarin gwiwa.”
Makaman da aka ƙwato sun hada da bindiga ƙirar AK47 guda biyu da harsasai, kuma an damƙa su a hannun sojoji.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram mafarauta
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe ubangidan Turji, Kacalla Ɗanbokolo a Zamfara
Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa jami’an sa-kai sun kashe wani riƙaƙƙen ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan jihar mai suna Kacalla Ɗanbokolo.
Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Ahmad Manga wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana kisan Ɗanbokolo a matsayin gagarumin nasara a yaƙi da matsalar tsaro.
“Ɗanbokolo mutum ne da ya fi Bello Turji fitina, ya fi Turji aikata miyagun laifuka, illa kawai shi Turji sunansa da ya karaɗe kafofin yaɗa labarai,” in ji Ahmad Manga.
“Mutanensa da aka kashe sun haura 100, saboda haka wannan gagarumar nasara ce a gare mu,” in ji Manga.
Ya bayyana cewa Kacalla Ɗanbokolo ya rasa ransa a wata arangama a ƙauyen Kurya, tsakanin jami’an sa-kai na Gwamnatin Jihar Zamfara da mayaƙan ɗan bindigar.
Bayanai sun ce Ɗanbokolo ya shafe shekaru masu yawa yana kai hare-hare yankunan Jihar Zamfara tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Riƙaƙƙen ɗan bindigar ya gamu da ajalinsa ne tare da wasu ɗimbin mayaƙansa a lokacin da jami’an tsaron sa-kai -— da Gwamnatin Zamfara ta samar.
Mazauna yankin na kallonsa a matsayin mutum marar imani da tausayi da ya addabi yankunansu, ta hanyar kai hare-hare da kisan mutane.
“Shi mutum ne da bai yarda da sulhu ko ta wane hali ba, hatta ɗan uwansa Bello Turji ya taɓa nuna alamun amincewa da sulhu, amma shi wannan bai taɓa nuna hakan ba”, kamar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana wa BBC.
Wannan ne karo na biyu da jami’an tsaro ke kashe riƙaƙƙun ’yan bindiga da ake gani a matsayin iyayen gida da Bello Turji.
Ana iya tuna cewa, a watan Satumban 2024 ne jami’an sojojin Nijeriya suka kashe Halilu Sububu, wanda shi ma ubangida ne ga Bello Turji a wani kwantan ɓauna da suka yi masa tare da mayaƙansa.