Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5
Published: 19th, May 2025 GMT
Akalla manoma 90 ne mayakan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP suka kashe a Jihar Borno cikin watani biyar da suka gabata.
Mayakan kungiyar sun kuma yi garkuwa da wasu da dama baya ga wadanda suka tsallake rijiya da baya a hare-haren kungoyiyoyin da raunin harbi.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa kungiyoyin ‘yan ta’addan sun kai hare-haren ne a tsakanin watan Janairu zuwa Mayun nan da muke cikin na shekarar 2025.
Hari na baya-bayan nan shi ne wanda mayakan kungiyar ISWAP suka yi ritsa manoman da ke aiki a gonakin wake suka yi wa mutum 50 kisan gilla a yankin Karanti da ke Karamar Hukumar Kukawa a ranar Alhamis, 15 ga watan Mayu.
Gwamnatin Kano ta dakatar da haska shirin Labarina da Dadin Kowa da wasu 20 NAJERIYA A YAU: Mece ce Makomar Dimokuraɗiyya Idan Aka Wajabta Kada Kuri’a?A gefe guda kuma, mayakan kungiyar Boko Haram da ba sa ga-maciji da ISWAP sun kai wani hari garin Baga, mai tazarar kilimita 9, inda suka yi wa masunta da manoma kisan gilla.
Wata majiya a garin na Baga ta bayyana cewa kafin harin na Boko Haram manoma da masunta da ke garin sun jima suna samun kariya daga wani shugaban ISWAP a yankin.
Majiyar ta ce, manoman, “suna da takarda daga kwamandan da ke kula da yankin Malam Karanti zuwa Dawashi, mai suna Amir Akilu, kuma sun shafe watanni a karkashin kulawarsa, inda suke biyan haraji, kafin wannan harin.”
Ta bayyana cewa mayakan Boko Haram sun yi amfani da damar tafiyar da kwamandan na ISWAP da mayakansa, wajen kaddamar da mummunan harin, saboda zargin manoman da yi wa abokan gaba leken asiri a kansu.
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya ya bayayana cewa mayakan na Boko Haram sun yi musu kawanya tare da barazanar harbe duk wanda ya yi yunkurin tserewa.
Ya ce, “wasunmu sun ma riga sun fara girbin wakensu kafin aka kawo harin. Suka tara mu a wuri guda suna baraznar kashe duk wanda ya yi yunkurin guduwa, amma duk da haka muka zabi mu tsere maimakon mutuwar wulakanci a hannunsu.
“Ina tabbatar maka sun kashe mutane 50, yawancinsu ta hanyar yankan rago, sa’annan sun yi garkuwa da wadansu. Yanzu haka sun shiga Dawashi suna yin irin wannan kisan gillar,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu bayan ya tsira.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram ISWAP Kukawa
এছাড়াও পড়ুন:
Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba – Gwamna Muftwang
Ya ce kamar yadda mutane suka karanta a jarida, shi ma ya karanta, amma babu gaskiya cikin batun.
Ya ce a yanzu, kowa ya san yana cikin PDP kuma yana da matsayi a jam’iyyar, bai bar ta ba kuma da yardar Allah zai ci gaba da zama a cikinta.
Ya ce dalilin da ya sa wasu ke son ya koma APC shi ne domin jam’iyyar APC a Filato ba ta da shugabanni nagari, shi ya sa suke kallon shugabannin PDP da fatan su shiga jam’iyyar domin kawo gyara.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin mambobin APC na ƙasa suna sha’awar abubuwan da PDP ta yi a Filato, kuma suna ganin irin waɗannan ayyuka na buƙatar shugabanni masu nagarta.
Amma ya ce su dai suna sa Allah a gaba a siyasa da kuma a cikin jama’a, kuma duk inda Allah Ya nufa da inda jama’a suke so su tafi, to a can ne za su tafi.
Game da rikicin cikin gida da PDP ke fama da shi, gwamnan ya ce yanzu an sasanta matsalolin.
Ya ce an yi zama na musamman da na haɗin kai domin kawar da bambance-bambancen da suka jawo rabuwar kawuna.
Ya ce kusan shekara guda suna fama da wannan rikicin, amma yanzu da yardar Allah an wuce wannan mataki.
Ya ce shugabanni da magoya bayan jam’iyyar sun yi farin ciki da zaman da aka yi, kuma suna fatan rikicin ya zama tarihi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp