Taron Tehran ya bukaci tattaunawa cikin gaggawa kan kalubalen yankin
Published: 19th, May 2025 GMT
Manyan jami’ai daga kasashe da dama da ke halartar taron tattaunawa na Tehran sun yi kira da a tattauna domin tunkarar manyan al’amura a yankin.
Manyan jami’ai daga kasashe 53 da suka hada da ministoci da masana da ne ke halartar taron na kwanaki biyu.
Ministan harkokin wajen Oman Badr bin Hamad Al Busaidi ya ce a halin yanzu yankin yammacin Asiya na fuskantar kalubale da dama da ke bukatar tattaunawa cikin gaggawa.
A yayin jawabin nasa, Ministan harkokin wajen Oman ya bayyana matukar damuwarsa kan tashe-tashen hankula da kisan kiyashin da al’ummar Falasdinu ke fuskanta, yana mai bayyana wannan lamari a matsayin wani abin takaici a duniya.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Tajikistan ya jaddada bukatar yin tattaunawa mai ma’ana don tinkarar manyan matsalolin da duniya ke fuskanta.
Armeniya ta bakin sakatarenta na komitin sulhu Armen Grigoryan ta tabbatar da aniyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Shi kuwa tsohon firaministan kasar Iraki Adel Abdul-Mahdi ya bayyana matukar damuwarsa game da matsalar jin kai da kuma ci gaba da kisan kiyashi a zirin Gaza.
Ya yi Allah wadai da gazawar kasashen Larabawa da kungiyoyin kasa da kasa, wadanda a cewarsa, sun kasa dakile irin ta’asar da Isra’ila ke yi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yan Majalisar Kudu Sun Nemi Gafarar Tinubu Ga Nnamdi Kanu
’Yan Majalisar Tarayya daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci.
Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
Tuni aka tura Nnamdi Kanu zuwa gidan yari a Jihar Sakkwato inda yake zaman waƙafi.
A cikin sanarwa bayan taron gaggawa da suka gudanar a Abuja, ’yan majalisar sun ce duk da cewa suna girmama kotu da tsarin shari’a, lamarin ya rikiɗe zuwa matsalar ƙasa mai tasiri ga rayuwar jama’a, tattalin arziki da tsaro.
Da yake karanta sanarwar, Hon. Iduma Igariwey ya ce yin afuwa zai taimaka wajen rage tashin hankali da dawo da zaman lafiya a yankin.
Sun lissafa dalilai guda huɗu da suka sa suka yi wannan kira.
Dalilan da suke bayyana su ne ƙaruwa da rashin tsaro da tashin hankali da ke da alaƙa da tsare Kanu; Wahalar rayuwa da tattalin arziki da jama’a ke fuskanta da kuma buƙatar shugabanci mai tausayawa wajen shawo kan matsalolin ƙasa.