Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Nuna Wasu Manyan Fina-Finai 22
Published: 19th, May 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da nuna wasu manyan fina-finai masu dogon zango 22 sakamakon zarginsu da saɓa ƙa’idar hukumar.
Cikin wata sanarwa da jami’in hul da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar ya ce shugaban hukumar Abba Al-Mustapha ne bayar da umarcin saboda a cewarsa masu shirya fina-finan sun saɓa ƙa’idojin hukumar waɗanda suka tanadi cewa dole ne hukumar ta tace su kafin fitar da su.
Wasu daga cikin fina-finan da dakatarwa ta shafa sun haɗa da
Dadin Kowa
Labarina
Gidan Sarauta
Manyan Mata
Dakin Amarya
Kishiyata
Garwashi
Jamilun Jiddan
Mashahuri
Wasiyya
Tawakkaltu
Mijina
Wani Zamani
Mallaka
Kudin Ruwa
Boka Ko Malam
Wayasan Gobe
Rana Dubu
Fatake
Shahadar Nabila
Tabarmar
Rigar Aro
An umurci masu shirya fina-finan da abin ya shafa da su dakatar da duk wani nau’i na watsa shirye-shirye ko yawo nan da nan tare da gabatar da abubuwan da ke cikin su don amincewar tantancewa a cikin mako guda daga Litinin, Mayu 19 zuwa Litinin, Mayu 26, 2025.
Hukumar ta kuma yi kira ga gidajen Talabijin da Hukumar Yada Labarai ta Najeriya (NBC) da su taimaka wajen tabbatar da wadannan ka’idoji, tare da yin daidai da kokarin inganta kwarewa da bunkasar masana’antar Kannywood.
KHADIJAH ALIYU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar KNARDA Ta Ƙudiri Aniyar Yashe Madatsun Ruwa A Kano
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp