An Cafke Mai Garkuwa Da Mutane A Sansanin Alhazan Abuja
Published: 18th, May 2025 GMT
Wani babban jami’in hukumar jin daɗin alhazai ta babban birnin tarayya Abuja wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya tabbatar da cafke Yahaya Zango inda ya ce ya daɗe yana wasan ɓuya tsakaninsa da jami’an tsaro kafin dubunsa ta cika a yau.
“Ya so ya shige cikin sauran alhazai amma tuni jami’an tsaro sun gama shirya kama shi” a cewar jami’in.
Har kawo yanzu dai jami’an tsaro na farin kaya ba su ce komai ba game da kamen da suka yi.
Nigeria dai tana fama da matsalar rashin tsaro na masu garkuwa da mutane da ƴan bindiga musamman a yankin Arewa ta tsakiya da Arewa maso yamma. Duk da yunƙurin da jami’an tsaro suke yi amma har yanzu matsalar tsaron tana ciwa gwamnati tuwo a ƙwarya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: jami an tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane 8 A Jihar Filato
Wani ganau mai suna Kespan Iliya wanda shi ma mazaunin unguwar ne ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan unguwar na cikin barci lokacin da ‘yan bindigar suka iso cikin shigar kwamandoji, inda suka rika harbe-harbe kan mazauna unguwar.
LEADERSHIP ta fahimci cewa, sama da gidaje 96 ne kuma aka kone a Gyenbwas, al’ummar gundumar Langai ta karamar hukumar Mangu a yayin harin.
Kokarin jin ta bakin jami’im yada labarai na rundunar ‘Operation Save Haven (OPSH)’, Manjo Samson Zhakom ya ci tura domin wayarsa a kashe take a lokacin rubuta wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp