An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato
Published: 20th, May 2025 GMT
Wasu makiyaya biyu sun rasu bayan da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka buɗe musu wuta a kusa da ƙauyen Tahore, da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da mamatan ke dawowa daga kasuwar Maikatako a kan babur.
Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja Harin ’yan bindiga ya sa Zamfarawa sun koma kwana a jejiShugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana sunan mamatan a matsayin Umar Sa’idu da Rashida Yakubu.
Ya ce lamarin ya faru ne da yamma, kuma ya sanar da manyan jami’an tsaro ciki har da sojoji da ’yan sanda.
Babayo ya yi Allah-wadai da kisan, ya kuma roƙi hukumomin tsaro da su ɗauki mataki don hana sake faruwar irin haka a gaba.
Ya kuma buƙaci ’yan uwansa Fulani da su kwantar da hankalinsu tare da kaucewa ɗaukar doka a hannu.
“Abin da ke faruwa da al’ummarmu yana da matuƙar tayar da hankali. Mun riga mun rasa shanu sama da ɗari tare da wasu makiyaya. Yanzu kuma an kashe mana wasu biyu,” in ji shi.
Sai dai wani jigo a ƙungiyar raya al’adu ta Bokkos (BCDC), John Apollos Maton, ya ce bai da labarin faruwar harin.
Ya kuma musanta cewa mutanensu na da hannu a lamarin, inda ya bayyana cewa su dai kawai suna kare kansun ne daga ’yan ta’adda.
Mai magana da yawun Rundunar Operation Safe Haven, Manjo Samson Zhakom, bai amsa tambayar da wakilinmu ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Tun da farko, Aminiya ta ruwaito cewa an kai hare-hare da dama ƙauyukan Bokkos tsakanin watan Maris da Afrilu, inda mutane da dama suka mutu.
Hukumomin tsaro sun tura jami’ansu domin wanzar da da zaman lafiya a yankin.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Tsaro Na Kasar Iran ya bada Labarin Gwajin Wani Sabom Makami Mai Limzami Mai Daukar abubuwan Fashewa Har Ton Biyu
Ministan tsaro na kasar Iran ya bayyana cewa sojojin kasar sun yi gwajin wani makami mai linzami wanda yake iya daukar abubuwan fashewa hart un biyu.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Burgediya Janar Amir Nasirzade yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa . wannan gwajin sako ne ga gwamnatin Amurka da kawayenta. Idan wani ya dora mana yaki sai sun fi mu shan wahali. Don tare da wadannan shirye shiryen da kuke na kare kammu sai mun kori amurka daga yankin nan.
Yace iran tana cikin fushi kan abinda yake faruwa a Gaza don haka duk wata dama da ta samu zata maida martanin da ya dace. Ministan ya bayyana haka ne a jiya Laraba bayan taron Majalisar ministoci tare da shugaban kasa.