Kwankwaso ya fice daga NNPP tun a 2023 — Shugaban jam’iyya
Published: 16th, May 2025 GMT
Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dokta Agbo Gilbert Major, ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ba ya tare da jam’iyyar tun watan Yunin 2023.
Ya ce Kwankwaso ya fice daga NNPP tare da mabiyansa na Kwankwasiyya.
Tinubu zai halarci rantsar da sabon Fafaroma Leo Cikin makonni kaɗan Obasanjo ya murƙushe Boko Haram — AtikuA yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin ‘Daily Politics’ na Trust TV, Dokta Major ya ce:
“Kwankwaso ya zama tarihi a jam’iyyar NNPP.
“Bisa tsarinmu da kuma hukuncin kotu daga Abiya da Abuja, ba ya cikin jam’iyyar tun 2023.”
Shugaban jam’iyyar ya kuma yi bayani game da sauya sheƙa da wasu ‘yan siyasa ke yi daga jam’iyyar, inda ya bayyana cewa yawancin waɗanda suka fice ba su da matsala da NNPP, sai dai da tsagin Kwankwasiyya.
Ya ce waɗanda suka fice har yanzu suna da alaƙa da jam’iyyar.
“Suna ci gaba da faɗa mana cewa ba su da matsala da NNPP, matsalarsu dai ita ce tsarin tafiyar Kwankwasiyya. Wasu na cewa ta koma tafiyar mutum ɗaya, kuma sun gaji da haka,” in ji Major.
Ya ƙara da cewa waɗanda suka fice sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar NNPP, musamman a Jihar Kano, kuma ficewarsu babbar asara ce.
Amma ya ce jam’iyyar na nan da ƙarfinta – duk da ba ta tare da Kwankwasiyya.
Dokta Major ya kuma ƙi bayyana yadda dangantakar Kwankwaso ta ke da fadar shugaban ƙasa.
“Yana da ’yancin zuwa inda ya ga dama. Mu fa mun wuce wannan batun, mu yanzu muna duba gaba ne.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jam iyya Kwankwaso Siyasa a jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Sanar Da Dakatar Da Tattaunawa Da Amurka A Wannan Lokaci Da Take Fuskantar Yaki Daga Isra’ila
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Babu wata tattaunawa da zata yi da Amurka a halin da take ciki na kare kanta
A yayin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasar Iran, a hukumance Iran ta bayyana rashin yiwuwar ci gaba da zaman tattaunawa da Amurka kan batun shirinta na makamshin nukuliya, tare da dora wa Amurka alhakin abin da ke faruwa kai tsaye.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Akwai hadin kai tsakanin haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka wajen kai hare-hare kan kasar Iran domin rusa zaman tattaunawar nukiliya da haka ke bayyana kawar da duk wata magana ta hakikanin aniyar Amurka na samar da hanyar warware takaddamar Shirin Iran ta hanyar lumana.
A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa ci gaba da tattaunawa da Amurka a yayin da ake ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri yana gwada tsarin tattaunawar ba shi da ma’ana. Ya yi kakkausar suka ga matakin da hukumar ta IAEA ta dauka, inda ya yi la’akari da hakan a matsayin wani dalili na halasta cin zarafi a kan cibiyoyin nukiliyar Iran.